African LanguagesHausa

Wai da daske ne akwai ‘yan Najeriya miliyan 3.7 da ke rayuwa a Amurka ba tare da nagartattun takardun izinin zama ba kamar yadda ake zargi?

Getting your Trinity Audio player ready...

Da’awa: Wani mai amfani da shafin X na da’awar cewa akwai ‘yan Najeriya kusan miliyan 3.7 wadanda ke rayuwa a Amurka ba tare da izinin zaman da ya dace ba.

Wai da daske ne akwai ‘yan Najeriya miliyan 3.7 da ke rayuwa a Amurka ba tare da nagartattun takardun izinin zama ba kamar yadda ake zargi?

Hukunci: Karya ce! Alkaluman da mahukuntan Amurkar suka fitar ba su goyi bayan wannan da’awar ba. Najeriya ba ta ma cikin kasashe 10 na farko da ke da mafi yawan masu rayuwa a kasar ba tare da nagartattun takardu ba.

Cikakken bayani

Ranar  20 ga watan Janairun 2025, shugaba Donald Trump na Amurka ya yi rantsuwar kama aiki a matsayin shugaban kasa na 47 a tarihin Amurka. Da dai aka kammala wannan rantsuwar Trump ya shiga ofishin sa ya zartar da umurnai da dama a ciki har da ayyana cewa lamarin masu zama a kasar ba tare da izini ba lamari ne da ya kai matakin gaggawa dan haka ya tura dakarun sojoji zuwa iyakokin kasar.

Daya daga cikin umurnan da ya zartar ma ya yi kokarin hanawa yaran da aka haifa a kasar kasancewa ‘yan kasa idan har iyayensu baki ne marasa izinin sama ko kuma suna dauke ne da bisa ta wucin gadi. Wannan matakin ya dauki hankalin masu rajin kare ‘yancin shige da ficce.  

Kamar yadda aka zata, masu amfani da soshiyal mediya suna ta yayata bayanan da ba daidai ba suna fadar abubuwan da shugaba Trump din bai fada ba.

DUBAWA ta lura cewa wani mai amfani da shafin X, @Zaddy_Bruh, ya wallafa jaddawalin wasu jerin kasashe tare da adadin marasa izinin zaman da suka fito daga kasashen, tare da zargin cewa mai yiwuwa za’a tasa keyarsuu daga kasar.

Ya wakilci kowace kasa da tutarta, kuma ya sa Najeriya a kan gaba da da’awar cewa na ta mutanen sun kai miliyan 3.7. Haka nan kuma ta na biye da Zimbabwe mai mutane 765,000, sai Ghana miliyan 1.2 sa’annan Mozambique 123,000 kafin Mexico wadda ke da gagarumin yawa da miliyan 17.

Wannan da’awar ta kuma bayyana a Facebook, kamar yadda za ku iya gani a  nan, nan da nan.

Ganin yadda wannan batun ke tattare da sarkakiya ne ya sa DUBAWA tantance sahihanci ko kuma gaskiyar batun.

Tantancewa

DUBAWA ta kura cewa mai da’awar bai bayyana majiyarsa ba kuma ma bayan da aka tambaye shi a kan majiyar ko ma inda ya sami nasa labarin bai mayar damartani ba. 

Kiyasin yawan al’umma daga Hukumar Tsaro da Kididdiga ya nuna cewa baki daya bakin da ke rayuwa ba takardun izini na zaman miliyan 11 a watan Janairun 2022. A watan Afrilun 2024 ta hukumar ta sanar da hakan.

Takardar wannan kididdigar ta kwatanta baki a matsayin duka wadanda ke baki ne kawai ba lallai sai wadanda ba su da izinin zama ba. Bacin haka ta sake jaddada cewa yawancin wadannan mutanen ko sun shiga kasar ne ta barauniyar hanya ko kuma sun kawo ziyara na wani takaitaccen lokaci amma suka cigaba da zama ba tare da neman ainihin takardun da za su ba su izinin cigaba da zamansu a hukumance ba.

Sauran wadanda ke cikin wannan rukunin kuma su ne wadanda aka basu izinin zama na wucin gadi (TPS) da kuma wadanda aka haife su a kasar duk da cewa iyayensu ba su da takardun da suka dace (DACA) da ma wadanda ke zama a kasar na wani takaitaccen lokaci kafin a kammala sauraron shari’arsu a kotu.

“Baki marasa izinin zama wadanda ke neman samun izinin zama na LPR a karkashin dokar shige da ficce ko kuma INA, na daga cikin wadanda ke zama a haramce har sai sadda aka ba su cikakken izini bisa tanadin dokokin kasar. Wadanda aka kawo su kasar daga kurkuku su ma za su cigaba da kasancewa baki marasa izini har zuwa lokacin da za su sami izini a hukumance,” takardar ta bayyana.

Cikakken bayanin da takardar ta yi kan yawan al’ummar bisa kasar da aka haife su ya nuan cewa kasar Maexico ce ke da mafi yawan mutanen da ke zama a haramce a Amurkar, inda ta ke biye da kasashen Guatemala, El Salvador, da Honduras. Rahoton ya kuma kara da cewa al’ummar Mexico da ke zaman miliyan 4.81 shi ne kashi 44 cikin 100 na jimilar al’ummar bakin a shekarar 2022. Kamar yadda za ku gani a kasa.

Are there 3.7 million illegal Nigerian immigrants in the US, as alleged?

Teburin da ke nuna yawan marasa izinin zaman. Asali: Hukumar Tsaro da Kididdiga ta Amurka.

Bisa wannan teburin, ana kiyasin mutanen da ke zama a Amurka ba tare da izini ba a shekarar 2022 sun kai miliyan 11.

Abun lura kuma shi ne kusan miliyan 2.6 na wannan kason sun fito daga “sauran kasashe” amma wannan bai bayyana ko ‘yan Najeriya na cikin wannan adadin ba ko kuma ma dai ainihin kasashen da adadin mutanen da suka fito daga wuraren.

A Karshe

Da’awar mai amfani da shafin X na cewa mutane miliyan 3.7 na bakin da ke zama ba izini a Amurka ‘yan Najeriya ne karya ne kawai.

Show More

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
Translate »