Getting your Trinity Audio player ready...
|
Da’awa : Wani shafin Facebook ya yada wani labari na bidiyo (video) cewa shan wani maganin gargajiya zai sa mace ta haifi ‘yan biyu musamman mace da ke da ciki.
Hukunci: Karya ce! Nazari da bayanan kwararru sun tabbatar da cewa yin amfani da magungunan gargajiya da ake hade-haden saiwa da tafarnuwa da citta da danginta ba sa taimaka wa mace ta samu ciki.
Cikakken Sakon
Samun ciki na samuwa ne yayin da maniyin namiji ya hadu da kwan haihuwa na mace a cikin halittar da Allah ya samar a jikin mace daga nan sai su samar da abin da ake cewa (zygote) wanda daga nan sai ya girma ya zama dantayi (embryo). Ciki na samuwa bayan bin wasu matakai ne kadan sai abin ya faru.
Da fari dai mace ana haifar ta ne da kwayaye a wani kwanso da ke a mahaifarsu, yayin da take girma da kara shekaru wadannan kwayaye ingancinsu na raguwa kamar yadda binciken Royal College of Obstetricians and GynaecologistsTrusted Source suka nunar.
Mace dole sai ta fitar da lafiyayyen kwai sannan ne zai hadu da maniyyin namiji su hade bayan bin wasu matakai da wasu hanyoyi a jikin na mace.
Mai amfani da shafin facebook (Facebook user,) Everyday with Irene, na yada wani bidiyo (video) da ke d’aawar cewa amfani da saiwowin da suka hadar da tafarnuwa da citta da abin da ake kira beetroot a Turance da karas da kofi biyu na ruwa ake jika su a cikin roba kwana daya, zai taimakawa mace da ke son haihuwa. Ta kira su da sunan TTC Mai daawar ta nunar da cewa za a iya sanya maganin gargajiyar a naurar sanyaya kaya fridge, za a sha tsawon kwanaki uku kafin mace ta fara jinin al’ada.
Wannan bidiyo (video) da aka wallafa a ranar biyu ga watan Fabrairu, 2024 ya samu wadanda suka nuna sha’awa (Likes) 2100 da masu sharhi(comments) 132 da wadanda suka gani(views) 36000.
Wata mai bin wannan shafi (user follower, Osaruluka Jima) ta yi sharhi da cewa “akwai ilimantarwa a wannan bidiyo (video)”
Wata babbar mai bin shafin Adefunke Pinioluwa, ta yi nata tsokacin da cewa “abu mai matukar ilimantarwa ina ‘yanmatan TTC ku zo ku kalli wannan. Allah Ya sa a yi guda daga karshe.”
Duba da yadda wannan bidoyo ke bazuwa da hadarin da ke tattare da shi ta fuskar lafiyar al’umma, DUBAWA ya ga dacewar a tantance shi.
Tantancewa
Idan maniniyin namiji ba mai kazar-kazar ba ne sosai (motile) ba za su iya tafiya da nisa ba, don haka samun ciki ba zai yiwuwu ba, haka nan a bangaren halittar ta macen ma sai an samu yanayi na karbar maniyin ta yadda zai ci gaba da rayuwa. A wasu lokutan maniyin kan mutu a kan hanyarsa yana linkaya zuwa inda kwan na mace yake.
Ci gaban fasaha ya samar da yanayi yadda ake taimaka wa matan yadda maniyin namiji lafiyayye zai kai ga kwan haihuwarsu lafiyayye, a samu ciki ta hanyar abin da ake kira (intrauterine insemination ko in vitro fertilisation)
Ta ina ne samun cikin ke faruwa
A cewar Healthline, maniyi na iya hadewa da kwan mace a wurin da ake kira fallopian tube, wanda ke zama hanya ce daga kwanson da ke dauke da kwan haihuwar mace zuwa mahaifar mace. A cewar University of California San Francisco maniyin namiji kan dauki sa’oi 30 yayi tafiya daga kwanson da ke dauke da kwayayen na mace zuwa follopian tube.
A lokacin da kwan ke tafiya zuwa fallofiantube yana tsayawa ya yada zango a wata matattara da ake kira ampullary-isthmic junction. Anan ne maniyin ke hadewa da kwai. Idan kwan ya hade da maniyi shikenan sai ya gaggauta tafiya zuwa mahaifa ya samu wajen zama.
Abubuwan dubawa game da batun na samun ciki
Wasu matan na da matsaloli da ke sawa ba sa iya fitar da kwan na haihuwa wasu duk da fitar da kwan da ma hadewa da maniyin na namiji samun cikin sai ya gagara.
A wasu lokutan kwan ko maniyin watakila ba lafiyayye bane, dantayin ma watakila ba lafiyayye bane.
Bayanan Masana
Dr Nafisa Yusuf, da ke zama magatakarda a sashen kula da lafiyar mata a babban asibitin Abuja ta bayyana cewa, “Game-game irin na citta da tafarnuwa da Beetroot da Cinnamon da kanumfari ba zai taimaka wa mace ta samu ciki ba, babu wani bincike da ya tabbatar da haka.”
Ms Yusuf ta kara da cewa kwayoyin halitta na chromosome su ke nuna jinsi na jariri. Iyaye maza na da kwayoyin halittar na chromosomes XY yayin da mata ke da XX, namiji na ba da X ko Y yayin da ita mace ke ba da X chromosome.
Ms Yusuf ta kammala da cewa babu wani nau’in abinci da za a ce na taimakawa wajen samun ciki, amma idan mace na zuwa awo a asibiti ana fada masu su rika amfani da folic acid wanda kan taimakawa mace ta samu lafiyayen jariri.
Haka shima Dr. Johnson Udodi, babban magatakarda a baban asibitin na Abuja shima bakinsu ya zo daya da Ms Yusuf inda shima yace wannan hada maganin gargajiya da wadannan ‘yanitatuwa da suka hadar da tafarnuwa da citta bushasshiya da citta danya da beetroot da tafarnuwa a jika su a ruwa a sha don samun haihuwa, wannan karya ce. Ya jaddada cewa babu wata sheda da ta tabbatar da cewa wannan gane-game zai taimaka wa mace ta samu ciki.
Mr Udodi yace babu wani bincike da aka yi da ya mara baya ga wannan da’awa, cikin bayanan wacce ke wannan da’awa har tana cewa wai cikin abubuwan da ake hada maganin na gargajiya har da wacce ke sa mahaifa ta yi kauri. “Kaurin mahaifa na taka rawa wajen samun ciki” wannan bayanin ma bashi da amfani sauraronsa. Kamar yadda da’awar ta gabata karya ce.
Kammalawa
Nazari da bayanan masana su nunar da cewa amfani da maganin gargajiya da ake hadawa ta hanyar tsima beetroot da citta busasshiya da danyar citta da tafarnuwa da kayan kanshi na cinnamon da kanumfari don wai a samu ciki. Tsabar karya ce
Mai binciken yayi wannan aiki ne karkashin shirin gano gaskiya na DUBAWA 2024, karkashin shirin samun kwarrewa na Kwame KariKari da hadin gwiwar gidan jaridar Premium Times da Jami’ar jihar Legas UNILAG a kokari na fito da “gaskiya” a aikin jarida da inganta ilimin aikin jarida a fadin kasar.