Asalin hoton: Africa Press
|
Getting your Trinity Audio player ready...
|
Da’awa: Wani mai amfani da shafin X, @itz_masha, ya wallafa wani gajeren bidiyon da ke da’awar wai wasu a Zamfata sun fara shiga daji dan kama ‘yan bindiga ba tare da tallafin gwamnati ba.

Hukunci: Yaudara ce! Yayin da bidiyon ke nuna dan bindigan da ake zargi fararen hula sun kama, lamarin ya faru ne a jihar Kwara ba zamfara ba, kuma bidiyon tun shekarar 2025 ya ke shafukan sada zumunta.
Cikakken bayani
Mai amfani da shafin X wanda aka tantance, Big Masha @itz_masha, ya wallafa (ana iya ganin makalar a nan) wani bidiyo ranar 7 ga watan Yunin, 2026, wanda ke nuna wani mutun rike da bindiga. A bidiyon dai ya yi kaman ya na zaune ne a tsakiyar wani rukunin mutanen da ke masa tambayoyi.
A bayanin da aka wallafa da hoton, mai shafin na X ya yi da’awar cewa mutumin dan bindiga ne wanda mazauna Zamfara suka kama da kansu ba tare da wani tallafi daga jami’an tsaro ba. “Mutanen Zamfara sun fara kama Fulani ‘yan bindigan da suka addabe su a cikin daji ba tare da taimakon mahukunta ba,” shafin ya bayyana.
Fassarar abin da wanda ake zargin dan bindigan ne ya fada, @itz_masha ya yi bayani kamar haka, “Suna na Saleh Yusuf. Ni dan Kawula ne. Da ina gudanar da ayyukan ta’addanci kuma sunan mai gidanmu Haro. Bai san cewa na zo nan ba. Na taba zuwa kurkuku kuma da na fido ya gargade ni cewa kada in sake sata. Tun lokacin ban sake sata ba sai kwanan nan sadda na shihga harkar garkuwa da mutane …..”
Daga 8 ga watan Yunin 2026 mutane sama da 533,500 sun kalla bidiyon, wasu 643 sun yi tsokaci, 3,000 sun sake rabawa wasu 11,000 sun sanya alamar amincewa da labarin yayin da wasu 1,200 kuma suka adana.
DUBAWA ta kula cewa yawancin masu amfani da shafin da suka yi tsokaci a kan labarin sun yarda da shi, yayin da wasu suka nuna shakkunsu dangane da sahihancin labarin.
Wani mai amfani da shafin, Afolabi Olaide (@afor007) ya yi tsokaci kamar haka,
“Su sami duk wani bayani mai mahimmanci daga wurin shi, wata kila za su iya kama wasu . Bayan nan, sai su hada su da ma’aikinsu. Ta haka adadinsu zai ragu.”
“Ba wanda zai zo ya cece ku, ku kare kanku a matsayin ku na ‘yan Najeriya, ku kasance a raye dan ku kare iyalanku, kasancewar ku kiristoci ba ya nufin cewa Ubangiji zai sauko da kansa ya taya ku fuskantar yakinku… ku yi amfani da hikima,” a cewar wani shi ma mai amfani da X Tipzi (@tipzii_t) ya rubuta.
Haka nan kuma, Firdausyy(@Firdaussrr) sun yi tsokaci kamar haka, “Wannan bidiyon ya tsufa, ya fi shekaru uku. Ko daina yaudarar mutane.”
Wannan labarin ya shuhura kamar yadda za ku iya gani a wadannan shafukan nan, nan, nan, nan, nan, nan, nan, da nan a Facebook.
Ganin yadda irin wannan batun ke da sarkakiya ne ya sa DUBAWA tantance gaskiya.
Tantancewa
DUBAWA ta fara da cire mahimman hotuna daga cikin bangarorin bidiyon ta tantance su ta yin amfani da manhajar reverse image search dawasu manhajojin tantance sahihancin bayanai. Binciken ya nuna mana cewa tun 2025 bidiyon ke yanar gizo-gizo, haka nan kuma labarai daga kafofin yada labarai masu nagarta sun tabbatar mana cewa tun ranar uku ga watan Maris na shekarar 2025 aka wallafa bidiyon.
Wata kafar yada labarai, Sahara Reporters, ta wallafa labarin a watan Maris na 2025 kan yadda wata kungiyar ‘yan banga a garin Oke-ode, da ke karamar hukumar Ifelodun jihar Kwara, ta kama wani wanda ake zargi mai garkuwa da mutane ne, mai suna Saleh Yusuf. Sa’annan ta fanso wanda ya sata. Bidiyon ya kasance cikin bayanin da suka yi a labarin.
Wani shafin Facebook, OMO IBILE OKE ODE, ya yi amfani da labarin na Sahara Reporters wajen wallafa wannan bidiyon na 2025 tare da taken cewa ‘yan banga sun kama mutumin a jihar Kwara.
Bugu da kari binciken da muka yi ya nuna cewa kundin labarai na Linda Ikeji’s blog ma ya dauki labarin na shekarar 2025 tare da wallafa hotunan bangarorin bidiyon. Haka nan kuma, D English Alhaji, Dan Najeriyan da ke yawan sharhi a shafukan sada zumunta musamman kan rashin tsaro, ‘yan bindiga, garkuwar da ake yi da jama’a, batutuwan da suka shafi shugabanci da siyasa, musamman a yankunan arewacin Najeriya ya wallafa wannan bidiyon shi ma da bayanin cewa a garin Oke-ode na jihar Kwara ya faru.
Taken da ya yiwa bidiyon ya ce:, “Wadanda ake zargi masu garkuwa da mutane ne a Oke-Ode, Ifelodun, jihar Kwara. ‘Yan banganmu sun gano makamai da dama har da bindigogi kirar AK-47, da miyagun kwayoyi duk sun kasance daga cikin abubuwan da aka gano a wurinsa.”
A Karshe
Bidiyon da ake da’awar ya nuna mazauna Zamfara sun kama wani dan bindiga a dawa yaudara ce. Tantancewar mu ya nina cewa an kama mutumin ne a Oke-Ode, da ke karamar hukumar Ifelodun a jihar Kwara a shekarar 2025,ba a jihar Zamfara ba.
“Cibiyar Habbakawa da Koyon Sabbin Dabarun Aikin Jarida (CJID) ke aiwatar da wannan horaswar ta musamman tare da tallafin Kungiyar Tarayyar Turai.”
