Dasa Kiyayya:Wani shafin X da aka tsara yana yada farfaganda ta goyon bayan Rasha da yaki da dimukuradiyya a Najeriya

Wata rana an wayi gari da hayaniya da safiya da kararrakin babura, sai dai wannan yanayi ya sauya da tsakiyar rana. Sojoji sun cika titina, sun karbe tashar yada labarai sun kuma bayyana cewa an rushe gwamnati, dare na yi kuwa shiru kake ji juyin mulki da ake rade-radi ya tabbata.

Irin wannan yanayi shigensa ne aka rika samu kasashen Mali da Burkina Faso da Niger, tsakanin shekarun 2022 da 2023, abin da ya girgiza kasashen na yankin Sahel da sauya harkoki na zamantakewa da siyasa na kasashen.

“Wadannan juyin mulkin sun hambarar da jaririyar dimukuradiyya sun haifar da rashin kwanciyar hankali da kara fargaba tsakanin kasashen yankin.” a cewar Silas Jonathan kwararren masani kan harkokin samar da bayanai a intanet ( OSINT ) kuma manaja a sashin da ke bincike a shafukan intanet a Cibiyar aikin Jarida Kirkira da Cigaba (CJID).

Ya kara da cewa a shekarun bayan nan yankin na Sahel ya dauki wani yanayi. Tasiri na kasashen ketare na zahiri da badini ana gani a shafukan intanet da wadanda ba a intanet ba, ana amfani da su wajen neman mayar da wadannan kasashe kan tsari na mulkin soja, tsarin da a baya kasashen suka yi watsi da shi. Bisa amannarsu cewa “Milki mai karfi ” shine mafita a gare su.

“Wannan shi ke fadada zuwa kasashe makota kamar Najeriya ta hangar shigar da farfaganda a shafukan intanet, mutane na nuna sha’awarsu ga mulkin soja.” Wannan shine gargadin da Jonathan yayi.

Misali da aka gani karara shine zanga-zangar tsadar rayuwa ta #EndBadGovernance

 Wacce aka yi a watan Agusta, 2024 inda mutane a jihohi da dama suka rika daga tutar kasar Rasha da kira na sojoji su kawo masu dauki da ma nuna goyon bayansu ga salon mulkin soja, da dama ciki kuwa har da kananan yara (minors,) an rika ribatarsu da basu wasu ‘yankudade kalilan ana yaudararsu da wayar masu da kai a shafukan intanet don neman su goyi bayan wannan fafutuka.

Wannan abun yayi kama da abin da ya faru a yankin na Sahel inda rawar da kasashen ketare suka taka ya haifar da halin da ake ciki kawo yanzu, irin wannan yanayi na matsowa Najeriya ta hanyar yada labarai na karya a shafukan sada zumunta, inda suke son ganin al’umma sun amince cewa wannan ita ce mafita a gare su.

Salon janye hankali da labaran karya

Daya daga cikin misalai na irin wannan ya fara ne da wani shafin X da aka fi sani da Twitter wanda yake a kasar Mali kamar yadda bayanan shafin suka nunar @Sissoko Sora Demba, wanda ake amfani da shi wajen yada labarai ko bayanai kan Najeriya wanda da dama daga cikinsu labaran karya ne ko na yaudara.

Duk da cewa an bude shafin a kasar da ake magana da harshen Faransa yana mayar da hankali kan al’amura da suka shafi Najeriya, wannan ne ma ya sanya aza ayar tambaya a kan shafin saboda wasu dabi’u nasa da suka saba yadda aka saba gani. An bude shafin ne a watan Janairu 2023, shafin na da mabiya 26,100 yana kuma bin shafuka 7,849 yana kuma wallafa abubuwa masu tarin yawa, sama da wallafa 100,000 kawo  yanzu.

Wannan shafi ba shi da wasu bayanai da ake tantance mutum da shi. Kwararre kan yin fassara Faransanci zuwa Ingilishi ya bayyana cewa abubuwan da ake wallafawa akasari sharhi kan harkoki na siyasa ne, wadanda suke ba da karfi kan dangantakar kasashen yankin Sahel da Najeriya da alakarta da kasashen Yammacin Turai da Gabashinta.

Sowing discord: Coordinated X accounts driving pro-Russian propaganda and anti-democratic narratives in NigeriaHoto da aka dauka na shafin X na Sissoko Sora Demba

Wannan shafi ba lallai ne ya dauki hankali ba, ba don yana tattauna abubuwa da suka shafi Najeriyar ba tare da ba da bayanai na karya da ma yaudarar da ke cikinsu. Daya daga cikin misalin shafukan shine wanda aka yada ( shared)a ranar 3 ga watan Yuni, 2024 wanda ya nuna wasu dauke da makamai sanye da kayan sojoji ga kuma motar sojoji a bayansu.

A wannan wallafa an yi zargin cewa dakarun soja ne su 20 da fararen hula 71 aka kashe da wasu kuma 190 da aka yi garkuwa da su a hannun mayakan Boko Haram a yayin wani hari da suka kai wani shingen bincike a Aba a jihar Abia. A wannan lokaci wannan wallafa ta samu tarin martani  da ya hadar da wadanda suka kalla su (Views) 13,900  da masu tsokaci (Comments) 23 da masu sake yadawa su 35 sai masu nuna sha’awarsu (Likes) 218 da masu daukar adureshin wallafar don amfanin gaba  (bookmarks) su hudu

Sowing discord: Coordinated X accounts driving pro-Russian propaganda and anti-democratic narratives in NigeriaHoto da aka dauko daga shafin na X da ke nuna da’awar

Binciken DUBAWA kan wannan da’awa ya nuna cewa karya ce. Abin da ya faru ba a jihar Abia ba ne kuma hoton da aka lika na yaudara ne, hoton tsoho ne an yi shi tun a 2013 wanda ya hadar da shugaban Boko Haram Abubakar Shekau lokacin da yayi bidiyo yana nuna goyon bayansu ga kungiyar ISIS.

Duba da tattaunawa da wadanda suke jin harshen na Faransanci da ke amfani da shafin ya nunar da cewa da dama sun aminta da abin da ake fadi a shafin.Wasu bayanansu na nuni da cewa matsalar tsaro na bukatar sa hannun kasashen waje da ya hadar da bukatar shigowar sojoji don jagorantar kasa a matsayin mafita.

Wani bidiyon da ya zama ya watsu sosai shine na fitaccen mai arzikin nan dan Najeriya Aliko Dangote da aka nunar yana magana da harshen Faransanci (speaking French). Da aka nazarci wannan bidiyo da manhajar gano asalin bidiyo ta Deepware.ai ya tabbatar da cewa wannan bidiyo na karya ne kuma ma yadda labbansa ke sama da kasa ya nuna cewa ya saba dana ka’ida. Ya zuwa ranar 26 ga watan Nuwamba, 2024 wannan bidiyo ya samu martani sosai akwai wadanda suka kalla (80,000 views,) an sake yadawa sau (224 shares) da nuna sha’awa 595 (Likes) da wadanda suka kwafi link na shafin don duba a gaba 137 (bookmarks), wannan ya taimaka wajen yada labarai na karya.

Wannan shafi sau tari yana sukar salon mulkin Shugaba Bola Ahmed Tinubu inda yake nuna cewa shugaban ba zai iya mulki ba ineffective yana kuma alakanta shi da masu dillancin miyagun kwayoyi sau da yawa kuma yana kiran da a samu jagorancin sojoji a Najeriya dama nuna muhimmancin salon mulki na kasar Rasha.

Kasar Rasha (Russia) sau tari ana nuna ta a matsayin wacce ba a yi mata katsalandan wacce ke da tsaro (security,) da banbancinta karara da kasashen yammacin duniya kamar Amurka da Birtaniya da Faransa wadanda sau tari shafin ke nuna su a matsayin masu kutse masu mulkin mallaka.

Sowing discord: Coordinated X accounts driving pro-Russian propaganda and anti-democratic narratives in NigeriaJadawali daga Rejoice Taddy.

Shafin na X na kafa hujja da wasu abubuwa a kokari na tabbatar da cewa kasashen yamma na tsoma baki kan harkokin cikin gidan Najeriya, misali mika sammaci na kama Andrew Wynne, wanda dan asalin Birtaniya ne wanda ake zarginsa da kokari na tada hartgitsi a Najeriya bayan da ya boye kansa a matsayin mai siyar da litattafai. Ya dauki wannan a matsayin sheda ta kafa hujjar tsoma bakin kasashen waje a harkokin cikin gidan Najeriya. Hakazalika wannan shafi yana alakanta ziyartar Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu zuwa ga Firaministan Faransa (French Prime Minister) a matsayin dalili na sanya bakin Faransa a harkokin cikin gidan Najeriya, abin da ya bayyana da sake komawa turbar mulkin mallaka. 

 A bayyane take wannan shafi na kokari na kambama Rasha a matsayin gwamnati da ya kamata kasashen Afurka su yi koyi da ita muddin suna son tsayawa da kafarsu da tsari na kin kasashen yamma.

“Kowa yana da ‘yanci na yada ra’ayinsa a shafin intanet, ko don wata manufa ko karfafa gwiwa, sai dai idan an yi amfani da labaran karya wannan kuma an keta hakkin jama’a na bukatarsu ta samun labarai masu inganci,” A cewar Mista Jonathan. 

Manyan batutuwa da aka yada kan Najeriya a shafin na X

Sowing discord: Coordinated X accounts driving pro-Russian propaganda and anti-democratic narratives in NigeriaJadawali daga Rejoice Taddy

Lokacin da aka fara zanga-zangar yaki da tsadar rayuwa ta #EndBadGovernance wannan shafi ya kara yawaitar ayyukansa na yada hotuna (images) da bidiyo (videos) tare da nuna azama, Ya rika nuna yadda ‘yan Najeriya basa jin dadin gwamnati mai ci da ma kiran shigowar kasar Rasha (Russian intervention,) da kara nuna cewa kasar Rasha ita ce kasar da ta fi dacewa kasashen Afurka su runguma.

Duk da cewa shafin bai nuna bangaren da ya dauka ba kan zanga-zangar yayi ta kokari 

Nuna wasu hotuna ko bidiyo da suka nuna yadda ake daga tutar kasar Rasha, don sake nuna yadda ‘yan Najeriya basa maraba da salon mulkin shugabansu. Wasu lokutanma yana nuna wasu hotuna da bidiyo wadanda yake dangantawa da zanga-zangar.

Sowing discord: Coordinated X accounts driving pro-Russian propaganda and anti-democratic narratives in NigeriaJadawali na sama na nuna yadda aka rika yada irin wadannan bayanai kafin zanga-zanga da lokacinta da bayanta a zanga-zangar ta #EndBadGovernance a 2024

Wani abin sha’awar kuma shine adadi na bayanai da aka tattara da suka shafi kasar Rasha da wannan shafi na X kan wallafa, shi ke da kaso 83% na baki dayan abin da aka wallafa, wani lokacin abu guda ko a bishi da tattaunawa kan abubuwan da suka shafi kasashen kamar a Najeriya.

Adadin kaso na abubuwan goyon bayan Rasha da shafin na X ya wallafa

Sowing discord: Coordinated X accounts driving pro-Russian propaganda and anti-democratic narratives in NigeriaJadawali daga: Rejoice Taddy

Shafuka da ke da alaka

Yayin da shafin na X ke yada labarai na karya, wasu shafukan a yankin na Sahel na tattaunawa da wannan shafi na @Sissoko Sora Demba inda suke yada abin da ya wallafa da ke zama na karya. Wadannan shafukan har ila yau suna yada goyon baya ga Rasha, a cikinsu akwai shafuka biyu da ke da alaka ta kusa da Najeriya wadanda suke taimakawa wajen yada irin wadannan labarai da ma goyon bayan ganin an girka gwamnatocin soja a Afurka.

Sowing discord: Coordinated X accounts driving pro-Russian propaganda and anti-democratic narratives in Nigeria Jadawali na sama yana nuna shafukan da ke sake yada wallafar da ke nuna goyon baya ga Rasha da labaran karya a kan Najeriya duka suna haduwa wajen sake yada abin da suka gani daga babban shafin.

Biyu daga cikin jerin wadannan shafuka suna yada bayanansu a harshen Ingilishi : @Africanman da @ColonelAfzal. Dukkaninsu sun bayyana kansu a matsayin masu goyon bayan kasar Rasha da kasashe na Afurka masu goyon bayan Rasha.

@ColnelAzfal dan Najeriya ne wanda ke bayyana kansa a matsayin mai adawa  da masu cusa kansu kan harkokin kasashe da kishin Afurka wanda ke nuna goyon bayan kasashen Afurka da ke tare da Rasha, wanda kuma yayi amanna cewa babu abin da Rasha ke yi face mai kyau, ba ya kuma jin kunyar yada abin da ke ransa da tunaninsa da goyon bayansa ga Rasha. Kasar da ya amince kamata yayi Najeriya ta yi koyi da ita.

Sowing discord: Coordinated X accounts driving pro-Russian propaganda and anti-democratic narratives in Nigeria

Wallafar da aka yi a watan zanga-zangar #EndBadGovernance

Samfur na irin wallafarsaTataunawa a shafin X. 

@Africanman, wanda ya bayyana kansa a matsayin dan kasar Yuganda wanda ke yada batutuwa kan Najeriya da a kan yi cece-ku-ce a kansu yana kuma nuna goyon bayansa ga Rasha da kasashen da ke tare da ita da adawa da kasashen yamma.

Sowing discord: Coordinated X accounts driving pro-Russian propaganda and anti-democratic narratives in Nigeria

Hoton shafin X na African man 

Mahangar masana kan abubuwan da ake yadawa a intanet da suka shafi Dimukradiyyar Najeriya

Mark Duerksen, manajan tsare-tsaren sadarwa kuma mai bincike a cibiyar nazarin  tsare-tsare ta Afurka, ya bayyana cewa akwai mutanen gari ko masu fada aji da ake daukarsu haya su yada wasu bayanai, ko wasu kungiyoyi da aka tsara wadanda wasu masu fada aji daga Rasha suna da alaka da su don juya lamuran siyasa:

”Duk wannan na da alaka da siyasa yana haifar da sanya kokonto wajen ba da rahotanni na gaskiya, yana kuma kokari nuna cewa masu mulkin soja wasu fitattu ne a yankin Sahel, sun yi nasara kuma suna yin abin da suka yi alkawarin za su yi, kuma suna kokari na nuna cewa kasar Rasha ita ce uwa a garesu.”

Mista Duerksen ya kara da cewa wannan fafutuka ba ta tsaya anan ba har da ci gaba da bibiyar kafafan yada labarai na cikin gida da sauran kafofin samun bayanai  don jin bayanai da suka shafi karfin fada aji na kasar ta Rasha.

Sowing discord: Coordinated X accounts driving pro-Russian propaganda and anti-democratic narratives in NigeriaJadawali na Cibiyar Nazarin Tsare-Tsare ta Afurka da ke nuna yadda tasirin Rasha ke karuwa da kamfe da ake mata a Afurka ta Yamma

“Kamata yayi mu waiwaya baya mu yi tunani me yasa Najeriya aka nufa da wannan kamfe, muna iya nazartar taswirar tsarin kasashen da siyasarsu sai mu yi tunani na gaskiya cewa duk da kasancewar Najeriya na da irin nata kalubale a fagen shugabanci za a iya lura cewa har yanzu ita ke magana da murya guda kan kasashen da ke yankin na ECOWAS don tabbatar da mulki na bin doka da oda.” 

Ya kara da cewa ita ake wa kallo na jagoranci a yankin da kokari na ganin an bi doka, amma da zuwan sojoji suna yin juyin mulki a yankin na Sahel, wannan na nuna cewa ana so a ga an ragewa kasar karfi a yankin, hanya daya da za abi kuwa ita ce a tabbatar da samar da hargitsi a cikin kasar ta yadda kasar za ta koma tana kokari na warware matsalolinta na cikin gida ba wai ta zama mai karfin fada a ji ba a yankin.

Mista Duerksen ya kara da bayyana cewa bayan fafutuka a shafukan na intanet akwai kuma fafutuka a wajen intanet a yada labaran karya da rudani inda ya ba da misali da zanga-zanga ta baya-bayan nan a Najeriya:

“ Wadannan abubuwa zagon kasa ne da cin iyaka ga Najeriyar da ke da ‘yanci, ina zaton wannan abu ne da zai ci gaba da faruwa, ina tunanin ya danganta, fadar Kremlin za ta ci gaba da karfafa ayyukanta da amfani da yada labaran na karya a mataki na gaba da tsarin cin hanci da janye ‘yansiyasa da masu fada aji duk da burin ganin an sanyaya gwiwar Najeriyar.”

Sai ya kammala da bayyana bukatar da ke akwai ta fadakarwa kan irin wadannan dabaru: “Akwai bukatar a fadada wayar da kan jama’a kan wadannan ajandodi da yadda suke aiki da kokarin da ake yi na yin zagon kasa ga kokarin da ake yi na karfafa dimukuradiyyar Najeriya.”

Shafin X ya fitar da matsayarsa kan abubuwan da suka shafi yada labaran karya (policy against coordinated disinformation): ‘Bamu amince ba a rika duk wasu abubuwa da za su zama na yaudara a kan shafinmu, ko a lalata mana ayyukanmu ta hanyar wani shafi wanda ba na gaskiya ba, ko wasu halaye ko wani abu da za a sa a shafin.” Laifukan da wannan shafi yake yi a bayyane suke kuma babu wani mataki da shafin na X ya dauka akai . 

A kalamansa na karshe Mista Jonathan ya bayyana cewa ba kawai magana ba ce ta yada labaran karya, amma magana ce ta ‘yanci na kasa da hadin kan al’ummarta da makomar kasar a tsakanin kasashen na Afurka ta fuskar siyasa da tattalin arziki. “Karfin da Najeriya ke da shi a yanzu ya dogara da kokarin da ta yi na wayar da kan jama’a da mayar da martani da sanya idanu wajen bibiyar duk wasu abubuwa da ake zuwar mata da su na lalata mata tsari.”

Exit mobile version