Wata kirkira da ta kafa tarihi a kungiyar kafafan yada labaran Afurka a kokari na yaki da labaran karya da labaran karya da gangan shine samar da manhajar gano gaskiyar labari ta DUBAWA Chatbot. Wannan muhimmiyar manhajar, kwararru ne daga cibiyar raya aikin jarida da kirkire-kirkire (Centre for Journalism Innovation and Development (CJID)/DUBAWA) suka samar da ita, aka kuma kaddamar da ita a hukumance a 2024 (officially launched in 2024).
Wannan manhaja an nazarce ta a kasashen Afurka da dama da wajen nahiyar, ciki kuwa har da Najeriya da Gambiya da Senegal da Ghana da wasu kasashe da DUBAWA ke gudanar da ayyukanta tsawon shekaru inda take gudanar da ayyukan gano asalin labarai da ilimantar da mutane kan aikin jarida da gabatar da wasu makaloli da za su amfanar da al’umma.
Manhajar DUBAWA ChatBot
Tun bayan da aka kaddamar da wannan manhaja, a kasar Saliyo masu aikin gano gaskiyar labari sai suka samu sauki, da zarar mutum ya ce (Hi) da mika tambaya, manhajar za ta ba da bayanai kan abubuwa da dama da ake bukata. Za ta ba da bayanai kan sahihan shafukan intanet da kungiyoyi masu ba da bayanai na gaskiya wadanda dama tuni sun gudanar da binciken gaskiya kan bayanan. Sai dai wannan manhaja an tsara ta ta yadda kowane mutum a Saliyo da Najeriya da Ghana da Laberiya da sauransu za su iya amfani da su don kaucewa labaran karya da labarai da ake tsarawa na karya da gangan.
Ta yaya DUBAWA Chatbot ke aiki?
Manhajar ta DUBAWA Chatbot App wata manhaja ce ta laturoni da ke tallafa wa mutane su gudanar da bincike ko su gano hakikanin bayani kan wata da’awa ta hanyar amfani da manhajar WhatsApp wacce ita ke zama kan gaba wajen yada labaran da ke zama na karya.
Wannan manhaja na da saukin yin amfani da ita, ba sai mutum ya zama kwararren masanin fasaha ba zai iya amfani da manhajar, abin da kawai kake bukata shine wayar tarho da na’urar kwamfuta tafi da gidanka, sai kawai ka nemi tattaunawa da manhajar. Manhajar a yayin tattaunawa tana fahimtar wasu da bangare na jumla da muhimman kalmomi da wasu kalmomi na musamman, bayan ‘rubuta bukatar’sai a jira manhajar ta ba da amsa.
Wannan ita ce hanyar da za ka yi amfani da DUBAWA ChatBot:
- Latsa wannan link (Click on the link) don zuwa ga manhajar
- Kana iya sauke manhajar a wayarka ko na’urar kwamfuta ko Chromebook
- Bayan sauke manhajar sai a yi mata magana ko tambaya da cewa “Hello/Hi,”, daga nan za a ga amsa daga manhajar.
Tattaunawar manhajar tana aiki kan daya daga cikin ayyuka hudu da aka bata
- Tantance da’awa
- Samar da sabbin bincike da aka yi
- Neman sani game da DUBAWA
- Ba da rahoton wata da’awa
Ko da ace baka latsa wannan link da aka bayar ba a sama, kana iya daukar wayarka ka kara mata hoton QR Code da ke a kasa. Wannan zai iya kaika kai tsaye wurin da za ka iya zuwa ka yi bincike kan da’awar da kake so ka fayyace.
DUBAWA ChatBot App QR Code — ka dauki hoton QR code don tantance da’awarka! Asalin hoto: CJID / DUBAWA
Hoton shafin da za ka je lokacin da ka bude karamar wayarka don kara ta kusa da QR Code— Asalin hoto: DUBAWA / Fayia J. Moseray
Wannan shafi shine za ka samu kanka, idan ka kara wayarka don daukar hoton QR Code , abu na gaba shine ka rubuta bukatar da kake da ita sai ka ba da sifes “type space” sannan ka tura “send, nan da nan za a tantance da’awar da kake da bukata a kanta.
A LURA: A kula kada a kwafo ko a kara tura wani bayani na da’awa daga wani da ya turo maka ko wani rubutu a wurin da aka tanada don yin rubutu, maimakon haka ka rubuta da kanka tambayarka za ka ga an baka amsa kan da’awar da kake nema!
Da wannan kirkira ta DUBAWA ChatBot an mayar da aikin gano gaskiyar labarai sun zama masu sauki ga al’umma, aiki kadan ba tare da amfani da wani ilimin fasaha mai zurfi ba na yaki da yada labaran karya.
Karshe
Kamar sauran wasu manhajoji, ita ma manhajar ta DUBAWA ChatBot Mobile ba kawai za ta taimaka wa ‘yanjarida ba wajen saukaka aikinsu, za ta zama wani bigire na samar da sauyi ga masu aikin bincike da masu aikin gano gaskiyar labari ko bayani da dalibai da al’umma da ke neman samun bayanai sahihai ba tare da bata lokaci ba su samu bayanai masu inganci.





