African LanguagesFact CheckHausaHealth

Da’awowi biyar masu daure kai dangane da cutar daji da muka bincika a 2024

Getting your Trinity Audio player ready...

Duk da kasancewarsa wani dandali da ake samun bayanai na karya, kafafan sadarwar zamani sun kasance wata kafa da mutane da dama ke ziyarta don neman bayanai da ke da alaka da lafiya, yayin da a hannu guda masu aikin gano gaskiyar bayanai suke aiki shekara bayan shekara a kokari na tsaftace dandalin sadarwar ta zamani.

Cutar daji ko kansa ta kasance a kan gaba wajen sanadi na rayukan al’umma a duniya, abin takaici masu yada labaran karya na amfani da wannan dama wajen ba da bayanai na yaudara ga al’umma ba tare da la’akari da illar hakan ba. A matsayinta na zama dandali da ke ba wa al’umma bayanai masu inganci jaridar DUBAWA  ta duba wasu da’awowi da dama kan batun da ya shafi cutar ta daji ko kansa, ga wasu daga cikinsu: 

  1. Wasu nau’ikan abinci na maganin cutar kansa

A watan Fabrairu, 2024 wani mai amfani da shafin Facebook yayi da’awar cewa cin wake da miyar da aka yi da wake da lemon tumatir suna warkar da cutar daji ko kansar mafitsara ko ta nono ko wacce kan shafi yankin kwanciyar da a cikin mace ko ma girman tsiro a jikin dan Adam.

Sai dai binciken masana ya nunar da cewa duk da cewa wannan nau’ikan kayan abinci na da alfanu ga jikin dan Adam akwai bukatar binciken kimiya kafin tabbatar da hakan, musamman a wannan fanni. 

Kwarraru sun bayyana wannan wallafa a matsayin mai hadari wajen ba da bayanan karya, inda suka yi gargadin cewa masu cutar kansa da suka yarda da wannan da’awa za su iya ci gaba da zama a yanayi na yunwa, suna ma iya ajiye rigakafin da suke yi a game da cutar. Za a iya karatu idan aka duba wannan link Read more.

  1. Jijiyar fulawar ko furen nan Dandelion na maganin cutar daji cikin sa’oi 48 

A shekarar ta 2024 ce wani mai amfani da shafin sadarwar yayi da’awa cewa jijiyar wannana fulawar ko fure ta Dandelion na maganin cutar daji da kaso 98 cikin dari cikin kwanaki biyu.

Amma bincike ya  nunar da cewa akwai yiwuwar cewa jijiyar ta fulawar ko furen Dandelion na dakile bazuwar kwayoyin halittar kansar nono a jikin bera, wannan bincike bai kai ga yi a jikin dan Adam ba.

Har ila yau wasu ayyukan bincike sun nunar da cewa dandelion na iya taimakawa yaki da cutittika, masana sun yi gargadi cewa  akwai bukatar neman shawarar kwararru kafin shan shayi na furannin dandelion, wanda hakan na iya jawo cutika a jikin dan Adam  idan ba a lura ba. Akwai karin bayani a nan ( here). 

  1. Amfani da karamar lasifika ta kunne tsawon lokaci na iya jawo cutar kansar kwakwalwa

Wata da’awar da ke da alaka da cutar kansa da DUBAWA ta yi nazari a kanta a 2024 ita ce yadda wani bidiyo da aka yada a shafin Instagram wanda aka fi sani da Instablog wannan bidiyo da aka yada ya nuna yadda wata mata ta yi da’awar cewa wani mutum ya ja hankalinta da cewa idan mutum ya dauki lokaci mai tsawo yana amfani da wannan karamar lasifikar ta kunne yana iya fuskantar hadarin kamuwa da cutar kansar kwakwalwa. 

Har kawo yanzu babu wata sheda a kimiyance da ta goyi bayan wannan da’awa, sai dai kwararru na ba da shawara da a rika rage karfin lasifikar idan an zo likawa ko amfani da ita a kunne, saboda suna cewa idan sautin yayi karfi yana iya illa ga jin mutum, ba wai ya haifar da cutar kansa ba. Za a iya kara nazari idan an bi wannan link More details.

  1. Man shafawa na Vaseline na jawo cutar kansa 

A wani labarin kuma wani mai amfani da shafin X yayi da’awar cewa amfani da man Vasiline na da hadari, inda yayi kira ga jama’a da su rika amfani da Mankadanya na asali ko Sheabutter a Turance maimakon Vaseline. 

Wannan mai amfani da shafin na X yayi da’awar cewa Vaseline na dauke da wasu sinadarai wadanda za su iya jawo cutar dajin mama ko nono da jawo tsufan fata da wuri da rikita kwayoyin halitta.

Sai dai bincike ya nunar da cewa ana iya fuskantar hadari ne idan ana amfani da Vaseline wanda ba a tace ba. Wata makala da kamfanin Unilever yayi bayani a cikinta yayi bayani cewa ana tace abin da ake yin Vaseline akalla sau uku a tabbatar da an cire duk wasu abubuwa masu hadari. 

Wasu nazarce-nazarcen da aka yi kuma sun nunar da cewa babu alaka tsakanin Vaseline da cutar ta kansa. Zaa iya zurfafa bincike idan aka duba wannan link (Read more here).

  1. Turiri daga na’urar dumama abinci na jawo cutar kansa

Wannan  da’awa ta karshe an samo ta ne daga wani mai amfani da shafin Facebook wanda ya sake yada labarin da mutane suka dade suna ji wanda ke nuna cewa amfani da na’urar dumama abinci na jawo cutar daji ko kansa a jikin dan Adam. Ko da dai wannan na’ura na fitar da wani tururi kadan saboda lantarki da karafan da ke jikinta kamar yadda ake samun irinsu a samaniya da suke fesawa duniya, kamar ita ma na’urar da ke ba da intanet Wi-Fi da sautin rediyo, da dama sun aminta da samun cutar daga wadannan sabubba musamman na’urar ta dumama abinci ana alakantata da jawo cutar ta daji ko kansa.

Sai dai bincike da aka yi sun nunar da cewa amfani da na’urar dumama abinci baya lalata abinci sanadin tururin da ke fita.Ko da yake mai da’awar yace tsayawa kusa da na’urar dumama abincin na iya jawo cutar daji, wani bincike ya nunar da cewa cibiyoyi na gwamnati sun ba da shawarwari cewa a guji tsayawa kai tsaye kusa da na’urar a lokacin da take aiki, ba kawai saboda cutar kansa ba don gudun iya samun wasu raunika da ka iya shafar fatar jikin mutum ko ma idanuwansa. Za a iya samun karin bayani idan aka bi wannan link (information here).

Show More

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button
Translate »