Gwamnan Jihar Sokoto. Mallakar hoto: FB/Sokoto Government House
|
Getting your Trinity Audio player ready...
|
Da’wa: Wani mai amfani da Facebook ya yi ikirarin cewa wani babban jami’in ‘yan sanda yana aiki a matsayin jami’in ADC ga shugaban Hisbah.
Hukunci: Yaudara ce. Hoton da aka yi amfani da shi bai nuna shugaban Hisbah tare da ADC na ‘yan sanda ba. Yana nuna Gwamnan Jihar Sokoto ne tare da ADC dinsa a wani taro da ya shafi Hisbah.
Cikakken Bayani
Wani bayani da ya yadu a Facebook a ranar 2 ga Mayu, 2026, ya janyo ce-ce-ku-ce bayan ikirarin cewa Nijeriya “ta zama kasar Musulunci gaba daya,” tare da zargin cewa malaman addini na karɓe iko da hukumomin gwamnati.
Sakon ya kara da cewa Rundunar ‘Yan Sandan Nijeriya na karbar “umarnin kai tsaye” daga Hisbah, wanda aka bayyana da “kungiyar addini da ba ta cikin tsarin doka,” sannan ya tambayi dalilin da ya sa wani jami’in Sufurtanda na ƴan sanda zai zama ADC ga wani jami’in Hisbah.

Hoton sakon da aka yada
An yaɗa ikirarin da wani hoto da ke nuna jami’in ‘yan sanda sanye da kaya yana tsaye a bayan wani mutum da ke sanye da tufafin jami’an tsaro, inda mai wallafar ya ce shugaban Hisbah ne da ADC na ‘yan sanda ke yi masa hidima.
Cikin sa’o’i biyu kacal da wallafa sakon, ya samu martani 322, sharhi 464, an kuma yaɗa shi sau 40, wanda ke nuna yadda ya yadu cikin sauri.
Sakon ya jawo ra’ayoyi mabambanta a kafafen sada zumunta, inda wani mai suna Rawlings O. Michael ya ce wannan “cin zarafin hukma ne karara.”
Adegboye Kaysuccess Adekunle ya yi shaguɓe cewa “za ka gaji da kuka… Duk da haka, Hisbah tana da matsayi a doka, dokokin jiha ne suka samar da ita.”
“Ina ganin ya kamata ka fahimci lamarin sosai kafin magana. Ba daidai ba ne ka mai da hankali kan bangare guda kawai. Don Allah a yi magana cikin girmamawa.” Martanin Rabiu Tuji Goma ga wanda ya wallafa labarin.
Saboda yadda lamarin ya shafi addini a Nijeriya, DUBAWA ta binciki gaskiyar ikirarin.
Tantancewa
Hisbah wata hukuma ce ta yaƙi da munanan halaye da ake samu a wasu jihohin arewacin Nijeriya, wadda aka kafa domin tallafawa aiwatar da wasu dokokin Shari’a a wadannan jihohi.
Duk da cewa tana aiki karkashin dokokin jihohi, Hisbah ba ta cikin tsarin tsaron tarayya kuma ba ta da iko a kan Rundunar ‘Yan Sandan Nijeriya.
Rundunar ‘Yan Sandan Nijeriya tana karkashin gwamnatin tarayya kuma tana aiki bisa kundin tsarin mulkin Nijeriya.
A gefe guda kuma, ADC jami’in tsaro ne da ake nada domin kare manyan jami’an gwamnati kamar gwamnoni tare da kula da harkokin tsaronsu.
DUBAWA ta yi amfani da mahajar binciken hotuna ta Google domin gano asalin hoton.
Sakamakon binciken ya nuna cewa mutumin da ke cikin hoton shi ne Ahmad Aliyu, Gwamnan Jihar Sokoto, ba shugaban Hisbah ba.
An dauki hoton ne a wani taron kaddamar da ayyukan Hisbah a Jihar Sokoto, inda gwamnan ya halarta a matsayinsa na shugaba.
A cewar Darakta Janar na Harkokin Yada Labarai na Gwamnatin jihar Sokoto, an gudanar da taron ne a ranar 21 ga Nuwamba, 2024.
Hakama Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Sokoto ta hannun kakakinta, Ahmad Rufa’i, ta bayyana ikirarin a matsayin karya da yaudara, tana mai jaddada cewa babu wani jami’in ‘yan sanda da aka tura domin yi wa wani shugaban Hisbah hidima.
“Jami’in ‘yan sandan da ke kusa da shi ADC dinsa ne na hukuma, wanda aka saba bai wa manyan jami’an gwamnati domin tsaro”, in ji shi.
Babu wata hujja da ke nuna cewa jami’in ‘yan sandan yana aiki ga wani shugaban Hisbah ko yana karbar umarni daga wata hukuma ta addini.
A Ƙarshe
Ikirarin cewa wani shugaban Hisbah yana da ADC na ‘yan sanda yaudara ce.
