Cikakken Sakon
Wata na tuni da mata a da ake bikinsa a kasashe da dama na duniya a tarihance shine watan Maris, a irin wannan lokaci ne ake duba irin ci gaba ko nasararori da mata ke samu a fannoni da dama na rayuwa, ba tare da nuna banbanci ta fuskar kasar da suka fito ba da kabilarsu da harshensu da al’ada da tattalin arziki ko siyasa ba.
A dangane da bikin wannan wata ne DUBAWA yayi duba na tsanaki kan lamuran na lafiya da suka shafi matan, don duba irin kalubalen da suke fuskanta a fafutuka ta neman su samu lafiya. Muna da burin ganin an duba lamuran daban-daban tare da bukatar jan hankali don a dauki matakai kan batutuwan.
Jima’i da Kulawa da Lafiyar da ta shafi jima’i
Kulawa da lafiyar da ta shafi jima’i (Sexual health) na nufin samun gamsasshiyar nutsuwa ta zahiri da badini, wannan ya hadar da samun damar kaucewa samun ciki ko juna biyu ba tare da an yi niya ba, ko zubar da ciki ta hanya mai hadari da samun cutittika ta hanyar jima’i, wannan kuwa ya hadar da samun cuta mai karya garkuwar jiki ta HIV da cutika da ake samu ta jima’i (STIs) da cutika da ake samu a tsarin jikin dan Adam masu alaka da haihuwa (RTIs) da cutar daji da rashin haihuwa da samun ciki ba tare da an yi nufi ba / zubar da ciki da rashin sha’awa/karfin mazakuta da sauran nau’ikan matsaloli da suka shafi jima’i. Abubuwan da suka shafi kulawa da lafiyar da ta shafi jima’i suna da fadi, sannan sun hadar da wayar da kan al’umma kan abin da ya shafi jima’i da tantance jinsi da bayyana abin da ya shafi jima’i da dangantaka da sha’awa.
Kulawa da lafiyar da ta shafi jima’i na nufin tsarin da ya shafi yadda mace ka iya haihuwa a matakai daban-daban na rayuwarta. Kula da lafiyar a kan lokaci da samar da tsarin kula da haihuwa na tseratar da rayuka.
Tsarin kula da goyon ciki da haihuwar jarirai da amfani da magungunan tazarar haihuwa da tsarin iyali da tsarin ba da shawarwari ga wadanda suka fuskanci cin zarafi saboda jinsinsu da kula da masu cutar HIV da ba da kulawa ga wasu rukunan al’umma daban-daban na karfafa zukatan al’umma su ji suna da ‘yanci da samar da yanayi da mutanen da aka raba da muhallansu za su ji cewa za su iya haihuwa koda yaushe? Da tayaya za su rika jima’i sau nawa ko ma za su samu ciki.
Duk da irin samun ci gaba da ake yi samun kulawa da lafiyar da ta shafi jima’i abu ne da ba ko’ina ake samu ba ko kuma a samu nakasu. Wasu batutuwan da suka shafi lafiyar da ta shafi jima’in sun hadar da cutar da kan shafi wajen mahaifa (Endometriosis,) da cutar kansa da kan shafi tsarin haihuwar mace (Gynecologic Cancer) da cutar da kan shafi mafitsara ta Interstitial cystitis (IC), da cutar kumburi a tsarin samun ciki na mace (Polycystic Ovary Syndrome (PCOS) da cin zarafi ta hanyar jima’i (SV) da karin mahaifa (Fibroids).
- Endometriosis: Matsala ce da kan shafi mahaifar mace. Endometriosis shine lokacin da ake samu wani dan yadi ko halitta mai makon a same shi a cikin mahaifar sai a ganshi a wani wajen na daban yana iya tsira a kwanson da ke fitar da kwan halitta na mace ko a bayan mahaifar ko tsakanin hanji zuwa mafitsara ko a kan mafitsara.
- Gynecologic Cancer: Wannan cutar daji ko kansa ce da ake samu a tsarin halittar jikin mace da take haihuwa. Gynecologic cancers na faruwa ne a cikin kowane bangare a tsakankanin kwibina ko kugun na mace wato daga kasan ciki kenan tsakanin kasusuwan mazaunai.
- Interstitial Cystitis (IC): Wannan ciwo ne mai tsanani da kan shafi mafitsara ya hana mutum sukuni ga zafi a tsakanin kwibi biyu na cinyar mutum. Mutanen da ke da cutar ta IC kan iya samun kumburi da jin zafi ko tsagewa da rashin iya rike fitsari a mafitsararsu.
- Polycystic Ovary Syndrome (PCOS): Polycystic ovary syndrome wannan na faruwa ne idan kwanso na kwan haihuwar mace ya zama yana fitar da sinadarai na maza fiye da tsaka-tsaki. Daya daga sakamakon da ake samu ta dalilin wannan shine a samu cysts(kwanso cike da ruwa-ruwa) wanda ake samu a cikin kwan halitta na bangaren mata. Mata da suke da jiki ko teba sun fi samun PCOS. Kuma matar da ta samu PCOS ba wahala ta samu cutar sukari (diabetes) da cutar zuciya. Daga cikin alamu na kamuwa da wannan cuta sun hadar da jinin al’ada da ke zuwa ba akan ka’ida ba, rashin haihuwa da ciwo tsakanin kwibi biyu tsakanin kasusuwan cinya da yawaitar tsirowar gashi a fuska da kirji da ciki da sharaba da yawan kiba fata ta rika kyalli da dabbare-dabbare.
- Sexual violence (SV): Wannan na nufin yin jima’i da mutum ba tare da yardarsa ba, Kowa zai iya fusknatar wannan cin zarafi na SV amma amfi samu a mata, Sau tari maza ke yi ga wanda suka sani ko na kusa da su ta yiwu ya zama aboki ko makoci ko wani daga cikin dangi da sauransu.
- Pregnancy-related complications:Wasu matan kan fuskanci wasu matsaloli da suka shafi lafiya a lokacin da suke da ciki, wannan na iya yiwuwa cutar ta shafi uwar ne ko dan nata (jariri) ko duka biyun, ko da matan da ke lafiyayyu kafin su samu ciki suna iya samun wasu matsalolin, wadannan matsaloli kuwa sun hadar da ciwon suga na masu ciki (gestational diabetes,) da hawan jini na masu ciki (preeclampsia,) da haihuwa kafin cikar lokaci (preterm labour,) da ciwon damuwa (depression and anxiety,) da barin ciki (miscarriage,) da sauransu.
Lafiyar Nono ko mama
Lafiyar Nona kan fara ne da samun ilimi kan abin da ya shafi yadda nonon yake. Mace ta zama tana da masaniya kan yadda take ji a nononta da lura da sauyi da zarar ya samu. Bayan lokaci mace na iya fahimtar yadda nononta ke sauyawa da yanayin yadda yake saurin ji idan an taba shi da sauyinsa lokacin al’ada da shekaru da sauransu.
Babban lamari anan da shine cutar kansar nono (Breast cancer.) Wannan na faruwa ne sa’ilin da ‘ya’yan halittar nonon ke sauyawa cutar daji ta shige su, su yi ta hayayyafa nonon ya girma da kumburi. Wannan ya fi samuwa ga matan da shekarunsu suka kai 50 ko sama da haka. Ana samu ma a matan da basu kai hakan ba.
Yayin da a wasu lokutan cutar kan bayyana ba tare da nuna alamu ba, mafi akasari alamun cutar sun hadar da samun sauyi a girman nono da halittarsa da layi-layin da ke jikinsa da nauyi da kaurinsa, wannan kan faru a jikin nonon ko kusa da shi karkashin hammata, abun da ke ci gaba da faruwa a lokutan batan wata ko jinin al’ada a samu digo-digo na jini ko jinin ya rika fita a kan nonon.
Shekarun dena Haihuwa da Sauyin sinadaran Jiki
Menapause: Wani mataki ne a rayuwa da mata ke shiga wanda ke nuna cewa sun kai gabar dena haihuwa. Da yawa mata idan suka kai wannan gaba su kan dena jinin al’ada saboda kwanson da ke fitar da kwan haihuwa nasu ya dena aikinsa a lokacin. Wanda hakan ke nufin kwanson na (Ovary) ya dena sakin kwai da zai hadu da maniyyin namiji a samu da. Irin sauyin sinadarai a jikin matan da ake samu a wannan gaba kan shafi matan a zahiri da tunaninsu da hankalinsu da jin dadin rayuwarsu.
Yadda abun kan shafi matan da suka kai Manepause ya banbanta daga mace zuwa mace wasu na ganin alamunsa da yawa tare da su, wasu kuma kadan, wasu abun kan shafe su sosai yadda zai shafi yadda suke rayuwarsu da ingancinta a yau da kullum. Wasu kuma ana ganinsu da alamun shekaru masu yawa.
Wasu daga cikin alamu na cewa macen ta kai manepause sun hadar da jin zafi da yin gumi cikin dare da sauyi a tsarin jinin al’ada da bushewar farjin mace da jin zafi lokacin saduwa ko jima’in da shan wahala idan ana son yin bacci da jin kunci da damuwa.
Lafiyar Kwakwalwa
Kimanin mace daya daga cikin biyar na da irin matsalar da kan shafi kwakwalwa guda daya kamar damuwa da bacin rai, yayin da dalilai da dama kan iya zama musabbabi na wannan matsala, wasu da ake ganin na gaba sun hadar da sauyin lamuran rayuwa da sauyin sinadaran da ke jikin matan a wannan gaba na iya shafar lafiyar kwakwalwarsu, damuwa lokacin daukar ciki da bayan haihuwa da shekarun dena haihuwa da cin zarafi da kan shafi akasari mata idan aka kwatanta da maza.
Wasu daga cikin alamu (symptoms) na samun damuwar kwakwalwar a mata sun hadar yawaitar samun bacin rai da rashin samun kwarin gwiwa da sauyin dabi’a da kuzari da sauyin dandanon baki da samun wahalar yin bacci ko yawan yin baccin da sauyin nauyin jiki da yawan gajiya da saurin fushi ko sanyin rai sosai da ciwon kai da ciwon jiki da rashin narkewar abinci a ciki ba tare da wani dalili ba, da saurin fushi da rashin hakuri da janye jiki daga cikin mutane.
Citittika da kan Shafi Mafitsara (UTIs)
Cutittikan da kan shafi mafitsara (urinary tract infection) cutika ne da za su iya shafar duk wani bangare da ke tattare da mafitsara da suka hadar da koda da hanyar fitar fitsari da matattarar fitsari da jijiyar da fitsari ke bi ya fita daga jiki.
Mata su suka fi hadarin kamuwa da cutar da kan shafi mafitsara UTI idan aka kwatanta da maza. Ba kasafai wannan cuta ke nuna alamu ba kafin ta bayyana, amma a wasu lokutan ta kan nuna alamun kamar: Jin bukatar yin fitsari ya ki kuma fita da jin zafi lokacin yin fitsari da yawan yin fitsari da yin fitsari dan kadan da sauyi a kalar fitsarin, fitsari ya zama ja ko finki ko kalar leman cola da alamun jini a fitsarin da jin ciwo a matse-matsi tsakanin cinya da cinya.
Abubuwan da kan jawo hadarin kamuwa da cutar ga mata sun hadar da tsarin halittar jikin mace (Jijiyar da fitsarin kan bi ta mata gajeriya ce idan aka kwatanta da maza don haka kwayoyin cuta irinsu bacteria nan da nan za su isa mafitsara ta mace idan aka kwatanta da ta maza).
Mua’amalar jima’i kan iya haifar da cutar ta UTIs, jima’i da sabon abokin jima’i na kara barazanar kamuwa da cutar), wasu daga cikin magungunan hana haihuwa ( Amfani da robar hana daukar ciki ta mata da amfani da maganin da ake shafawa a cikin farji duk za su iya haifar da barazanar kamuwa da cutar ta UTIs, shekaru na dena haihuwa ana samun raguwar sinadaran halittar estrogen wanda hakan kan shafi yadda hanyar da fitsari ke aiki, wannan na iya kara barazanar kamuwa da cutar ta UTIs).
Ra’ayin Kwararrun Masana
Mun tattauna da jami’ar lafiya Lynda Effiong-Agim, da ke aiki a asibitin kwararru na Chivar Specialist Hospital and Urology Centre, wacce ta yi bayanin cewa wani abu da ke zama na daban da ke damun mata shine cutar kansar nono ko dajin nono. Ta ba da shawarwari kan hanyoyi da za a bi a kaucewa cutar kamar shayar da yara nonon uwa da kaucewa shan taba da barasa da kaucewa yin kiba da yawan motsa jiki da kaucewa haske mai hadari na (radiation) da yin gwaji a asibiti da cin abinci mai gina jiki da yin gwajin nono kamar yadda jami’an lafiyar ke ba da shawara don gano wata alama ta kumburi, wadannan za su taimaka a kaucewa hadarin kamuwa da cutar ta kansar nono.
Jami’ar lafiyar ta kuma ja hankalin mata su ba da kulawa ga lafiyar kwakwalwarsu, abin da ta bayyana a matsayin ginshiki na lafiyar mata da walwalarsu. Ta bayyana lafiyar kwakwalwar a matsayin hakkin dan Adam.
“Duk da muhimmancin wannan fanni na rayuwarmu, a lokuta da dama ba a ba shi kulawar da ta dace, musamman a Najeriya, mutane ba kasafai suke fahimtar cewa mutum na fama da wata matsala ba da ta shafi kwakwalwa.” a cewarta.
Ta kammala da cewa rashin lafiya da ta shafi kwakwalwa abu ne da ake samun waraka sannan wayar da kan jama’a na bunkasa lafiyar ta kwakwalwa.
Mun kuma samu damar tattaunawa da masaniyar hada magunguna Precious Newman, wacce ta ba da shawarar cewa mata su rika ziyartar asibiti akai-akai, da zarar sun lura da wasu canje-canje a jikinsu, su je a duba lafiyarsu. Ta kuma kara da cewa su rika yawan amfani da kayan itatuwa da yawaita shan ruwa a abincin da suke ci.
Ta kuma bayyana motsa jiki a matsayin abin da ya kamata a rika yi a duk rana don jiki ya zauna lafiya a kone kitse da ke a jikin.
“Zuwa duba lafiyar nono da duba kwankwaso musamman ga mata idan suka kai shekaru 21 zuwa 40 sau biyu a shekara.” a cewarta.
Ms Newman ta kammala da cewa matan su rika samun hutu da yin bacci isasshe, su rika ba wa kansu lokaci su sami abinci mai gina jiki sannan su san tsarin lafiyar jikinsu.
Kammalawa
Batutuwa da suka shafi lafiyar mata abubuwa ne masu wuyar fahimta da ke da fannoni daban-daban wanda ke bukatar a yi nazari cikin tsanaki don samun mafita nagartacciya. Duk da haka za a iya samun ci gaba, idan aka mayar da hankali kan fadakarwa da wayar da kan jama’a da zuba jari kan gudanar da bincike kan lafiyar ta mata da abubuwan da suke bukata.