African LanguagesHausa

Mahimman bambance-bambance guda bakwai tsakanin Twitter da manhajar hamayya ta Threads

  

Ranar Alhamis, kamfanin Meta ya kaddamar da sabuwar manhajar da ake kira Threads. Wanda aka hada da Instagram, kuma an kaddamar da shi a kasashe 100 ciki har da Najeriya.

Jim kadan bayan kaddamar da ita, mahajar ta sami mutane miliyan goma bisa bayanan rahotanni, yanzu shafin mai takaitattun bayanai ya wuce miliyan 35 kuma yana cigaba da fadada.

Ana yawan kwatanta shi da Twitter sai dai akwai wuraren da suka bambanta.

  1. Dandalin Tattaunawa na Spaces: Twitter na da wani wuri da ake kira spaces inda mutun zai iya kunnawa ya tattauna da jama’a kuma kowa na iya shiga ya saurara amma Threads ba ta da shi.
  1. Wurin bincike: Yayin da wurin binciken twitter ke barin mutun ya bincika ya gano masu amfani da shafin ya kuma ga mahimman batutuwan da ke daukar hankali a kasashen duniya ko kuma ma a unguwar da mutun ke zama, ya ma gano bidiyoyi masu kayatarwa. Threads na barin mutun ya nemi mutane ne kawai wadanda zaka rika bi a shafin.
  1. Alamun sada zumunta ko hulda, da mayar da martani: A shafin Twitter, da zarar wani ya yi tsokaci, akwai zabi da yawa na irin martanin da mutun zai maida. Misali kana iya nuna alamar amincewa da latsa alamar ‘like’ , kana iya tsokaci, kana iya rabawa da wadanda ke iya ganin shafinka ko kuma ma dai tura adireshin ga duk wanda ake so ya ga labarin.
  1. Maballin da ke da hoton “Hamburger”: Wannan maballin a shafin Twitter can taimaka wajen bin mai bin shafin wanda ke amfani da shi dan ganin abubuwan da ya ke rubutawa. Ana kuma iya amfani da shi wajen gayyatar mutane da kuma toshe su dan hana su ganin shafin ka. Ana iya sa su cikin da’irar abokai, ko kuma toshe su da kai kararsu idan har suka rubuta abun da ba shi ne ba. A shafin Threads, wannan maballin sai dai ya bayar da damar cire mutun daga shafin ka, do toshewa sai kuma rufe sakon da ya rubuta da kuma kau karar labarin.
  1. Sako na kai-taye: Yayin da Twitter ke da yadda mutun zai iya zantawa da abokai ta kai tsaye ba tare da kowa ya gani ba. Threads ba zai iya yin hakan ba.
  1. Yawan haruffa: Yayin da Meta ya tabbatar cewa ana iya amfani da haruufa 500 a kowane sako, a shafin Twitter, wanda ba ya biya kuma kamfanin bai riga ya tantance shi ba haruffa 280 kadai zai iya amfami da su.

7. Threads na barin kowa (har da wadanda ba’a tantance ba) su wallafa bidiyo mai tsawon munti biyar yayin da a a Twitter wadanda ba’a  tantance ba sai dai su wallaga bidiyon da ke da tsawon minti biyu da sakan 20.

Bugu da kari, babban shafin Twitter na la’akari da abun da mai shafin ke so ya samar da mahimman kannun labaran a matsayin shawarwarin da ka iya daukar hankali, yayin da a yanzu haka babban shafin Threads sai dai mutun ya duba abun da aka riga aka yi tanadi a shafin.

Show More

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button