African LanguagesExplainersHausaMedia Literacy

Manhajoji bakwai wadanda “masu yada bayanan bogi” ke amfani da su wajen kirkiro labaran karya

A bara, wani bidiyon bogi ya rika yawo a shafukar soshiyal mediya yana nuna Vlodomyr Zelensky, shugaban kasar Ukraine, yana sanarwar cewa ya mika wuya bayan da Rasha ta mamaye kasarsa.

A wani bidiyon irin na karyar shi ma, wani mai karanta labarai ne wanda ya taje gashinsa mai launin baki da kyau, ya zauna ya na bayyana jerin abubuwan da a ganinsa su ne ke ta’azzara abun kunyar da Amurka ke yi tunda ba ta dauki mataki kan hare-haren bindiga a kasarta ba.

Babu ko daya daga cikin bidiyoyin nan da ke dauke da kanshin gaskiya. Masu karanto labaran ma ba mutanen gaskiya ba ne. Sautin muryoyin ba ya fita da kyau kuma ma bai tafiya dai-dai da yadda bakinsu ke motsi. Nazarin  da jaridar New York times ta yi ya bayyana cewa fuskokinsu sun yi kama da na irin hotunan da ake amfani da su a wasannin bidiyo kuma gashin da ke kansu ma sun yi kaman an manna ne.

Duk wadannan hotuna ne wadanda komfuta ta kirkiro ta yin amfani da manhaja mai kwakwalwar da ke kwaikwayon dabi’un dan adam wato AI. Abun da aka fi sani da “Deepfake” technology ko kuma fasahar karya mai zurfi, ya cigaba da habaka yanzu na kusan shekaru 10 ke nan har ma ya kirkiro ‘yan tsana masu magana ta yin amfani da fasahar zamanin.

A kan yi amfani da manhajar ta AI wajen lalatawa ko gurbata hotunan sanannun mutane. Amma kuma manhajar ma tana iya kirkiro na ta mutanen da kanta, abun da ya dara salon gyaran hotuna na gargajiya inda ake amfani da wadansu fasahohi na musamman a inganta hotuna, irin wadanda ake amfani da su a masana’antar fina-finai ta Hollywood, kuma wannan ya sa layin da ke tsakanin abun da ke karya da gaskiya dushewa a wani yanayin da ba za’a iya kamantawa ba.

Ganin cewa babu dokoki masu yawa da ke takaita yaduwar ire-iren wannan fasaha, tun ba yau ba, kwararrun da ke nazarin yadda labarai marasa gaskiya ke yaduwa, suke  gargadin cewa irin wadannan bidiyoyin wadanda ke hana banbanta gaskiya daga karya idan suka kasance a hannun mayaudara, ana iya amfani da su wajen tayar da rigima ko kuma ma kirkiro rikicin siyasa. Ga shi kuma yau hasashensu ya zama gaskiya.

Ga hanyoyi bakwai da ake amfani da su wajen kirkiro labaran bogi

1. Shafin “Break your own news” wato wallafa na ka labaran

Wannan dandalin ya kan kirkiro labarai da dumi-duminsu a shahararriyar kafar yada labarai. Ya na bai wa masu amfani da shafin damar asanya hotuna, rubuta labari da wallafawa.

Wadanda suka kirkiro manhajar sun fayyace cewa “burin manhajan shi ne ba’a, a ba jama’a dariya – ku yi hattara wajen labaran da kuke kirkirowa da yadda kuke rabawa. Kada ku yi abubuwan da suka sabawa doka, kada ku yi amfani da kalaman batacin ko kuma wani abun da zai tayar da hankali. Ku sha dariya amma ku kyautata wa jama’a!”

To sai dai ba kowa ne ya dauki wannan shawara ba domin ana amfani da shi wajen kirkiro labaran karya.

2. Manhajar Tweetgen

Tweetgen shafi ne da ke kirkiro sakonnin Twitter na karya. Yana da saukin amfani kuma masu amfani da shi na iya  kwaskware  shi duk yadda suke so suna iya canja kwanann wata, lokaci, adadin wadanda suka nuna suna son sakon da alamar like, yawan lokutan da aka raba labarin, sunan shafin, da wadanda ke amfani da shi wadanda su kuma sina hada da shafukan Twitter Web App, Iphone, Android da sauran ssu.

An alkinta manhajar da fasali irinta ta Twitter gaskiya. Misali ta na dauke da alamar tantancewar nan ta twitter mai ruwan buka da kuma yawan mutanen da suka sake raba labarin a shafukan su.

3. Prank me not – Ko kuma kada ku yi mun wasa/ba’a

Da shafin Prank me not, ana iya kirkiro shafin bayyana halin da ake ciki mai kama da na Facebook da ma tsokace-tsokace na karya. Shafin da ake iya amfani da shi dan sanya duk abubuwan da ake so na da saukin amfani. Ya na iya bari a sanya hotuna, a yi rubutu, a zabi alamar ‘like’ a kara tsokaci da sauran abubuwa da dama masu kayatarwa.

Da zarar aka sanya hotuna aka kuma yi rubutu sai shafin ta fara aiki. Daga nan sai a cigaba da karawa da rage abubuwan da ake so. Bayan an gama yana bayar da alamar rabawa da ‘yan uwa da abokan arziki.

4. Emkei mailer – Wasikun Emkei

Da Emkei mailer ana iya tura sakonnin imel na bogi. Ana kuma iya amfani da shi wajen kago adireshin imel, a tura imel din karya a kuma kirkiro hoton imel na karya.

 5. Fodey

Wannan shafin yanar gizo-gizo ne wanda ke iya kirkiro labaran bogi a shigen jarida. Idan mutun na so ya kirkiro labarin karya ya ce a wata jarida ya gani yana iya amfani da Fodey. Masu amfani da shi na iya cike guraben da aka tanadar da sunar jarida, kwanan wata, kanun labarai, daga nan sai a rubuta labari a raba. Duk da cewa ba za a iya ganin adireshin a latsa ba, masu amfani da shafin na iya sauke hoton jaridar da suka kirkiro su raba su kuma dora shi a duk shafukan da su ke so su dora.

6. Takardun biyan albashi, rasit da sauran takardun saye da sayarwa.

Wannan manhajar kyauta ce wadda ke taimakawa wajen kirkiro kowane irin takardun kudi da rasit. Manhajar na taimakwa masu amfani da ita zu zabi salon yin rasit da wani tarin da take da shi mai yawan gaske.

Ana iya kwaskware su yadda ake so a sanya tambarin kamfani a kuma zabi salon rubutun da ake su. Ana iya saukewa a buga bayan an gyara yadda ake so.

7. Deepfakes web- Shafin karya mai  zurfi

Ana amfani da shi wajen kirkiro bidiyoyin karya. Deepfakes manhaja ce a shafin yanar gizo wanda ake iya amfani da shi kamar wajen ajiya na Cloud. Abin da ake bukata kawai a dora bidiyoi sai a latsa wani wuri. Shi ke nan manhajar za ta yi sauran.

To sai dai duk bidiyon da ta kirkiro na dauke da wata alamar da ke nuna cewa kirkiro ta a ka yi. Ta na kuma barin alamun inda aka kwaskware bidiyon ta yadda nan da nan za’a gane cewa na bogi ne. “Mun yi imanin cewa duk wata fasaha ta karya mai zurfi dole a sanya mata alamar ganewa,” a cewar wadanda suka kirkiro ta.

Ko da shi ke fasahar ta cigaba sosai dan haka tana iya yaudarar dan adam.

Ana amfani da fsahar wajen nishadi, wasanni, barkwanci da shahararrun al’adu.

Show More

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button
Translate »