Wadanda aka yaudara da tsarin CBEX. Asalin hoton: Punch.
|
Getting your Trinity Audio player ready...
|
MAYAUDARA a harkokin samun kudade sun rungumi amfani da fasahar AI ta yadda za su samu saukin yaudarar mutane su daukai abin da ake tallata masu gaskiya ne, a yarda da shi a kuma runguma, ba tare da an gano karya ce ba aka lullubeta.
Kasancewar ana iya amfani da fasahar ta AI a samar da fuska kamar ta mutane, a yi murya irin ta mutum a hada bidiyo irin na kwararru cikin mintuna, mazambatar yanzu basa bukatar mai zuba jari na gaske ko harkokin zuba jari na gaske idan suna son jan hankalin mutane da ake son a yaudara, maimakon bata lokaci sai su sanya mutane su yarda da su saboda abubuwan da suka gani kamar na gaskiya sai kawai a yada su a shafukan sada zumunta.
Najeriya ta sha ganin irin wannan kasuwancin yaudara da kan fada kan daidaikun mutane da iyalansu. Rushewar kasuwancin yaudara na CBEX ya kasance a gaba cikin manyan misalai na irin wannan kasuwanci, inda yayi awon gaba da miliyoyi dubbai na mutane miliyoyi wadanda suka yi amanna sun zuba jarinsu a inda za su samu riba. Da dama wadanda suka fada komar wadannan mazambata sun rasa kudadensu na kasuwanci da kudaden makarantarsu da kudaden haya inda za a sanya gidaje cikin rudani na matsalolin tattalin arziki.
Kafin ma mazambatan na CBEX, akwai wasu masu kama da su wadanda kawai sauya masu suna kawai ake manufarsu daya kamar MMM da Loom da Ultimate Cycler da Racksterli da sauran wasu da ke yaudarar a shafukan intanet da “kulob na masu zuba jari” da dama a intanet, wadada kan yi wa masu zuba jari alkawura na samun arziki cikin hanzari wadanda kuma suna dogara ne da wadanda ke zuba jari sabbi don ci gaba da wanzuwa. Da zarar wani cikin masu zuba jarin ya dan ja baya shikenan sai tsarin ya fadi wadanda suka zuba jari a karshe shikenan an yi gaba da kudinsu ba za su sami komai ba.
Abin da ya sanya wannan nau’in zamba ke zama mai hadari shine yadda masu aikatawa suka rungumi kirkirarriyar fasaha ta AI, ta hanyar amfani da AI mazambatan kan hada fuska irin ta mutane su hada murya kamar tasu sai su hada labari na bidiyo da zai bayani kan harkokin na samun kudade wannan ya sanya ake ganin suna zuwa da wani abu na musamman da ba a saba gani ba a baya.
Duba da yadda matsin tattalin arziki ke karuwa mutane na kara duba hanyoyi na samun kudade, wannan nau’in zamba ta hanyar amfani da AI na kara bunkasa. Gano hanyoyi na fahimtar irin wadannan mazambata abu ne muhimmi wajen ba da kariya ga harkoki na tattalin arzikin mutane.
- Sheda a irin bidiyo da ake hadawa da fasahar AI mai kama da na gaske
Da dama irin wadannan tallace-tallace da ake ana nuna mutane da karfin gwiwa suna nuna cewa sun samu riba mai gwabi cikin kwanaki ko makonni. Irin wadannan bidiyo ana hada su ne da fasahar ta AI, ma’ana mutanen da ake nunawa babu su a zahirin gaskiya duk da cewa idan aka kalla kamar na gaske akwai wasu abubuwa da za a iya gano su kamar yadda fuskar ke juyawa da murya kamar ta mutum-mutumi wadannan ke nuna cewa hadawa aka yi.
Labarin nasarar ana tsara shi ne kamar gasje don ya maye gurbi wanda ya amfana da kasuwancin na gaskiya, wanda shi asalin mazambacin ba shi da shi.
Hoto na kirkirarriyar fasahar QuantumAI wanda aka yi talla a shafin YouTube.
Bincikenmu a baya ya nuna yadda aka fallasa wani talla a shafin YouTube wanda aka tsara da nufin yaudarar ‘yanNajeriya bayan da aka kaddamar da shi a watan Yuni,2025. Bidiyon ya nuna wani mutum a karamar riga yana magana irin ta “yanAfurka wandfa ke kiran mutane su rungumi Quantum AI, wani AI da mazambatan ke amfani da shi, duba da yadda mutumin ke magana yayi kama da dan’Adam, mutane da dama ba za su gane cewa AI ba ne.
- Amfani da wasu fitattun mutane suna ba da shedar tsarin cewa mai kyau ne
Wata dabarar da masu wannan zamba ke amfani da ita ita ce su dauko bidiyon wasu fitattun mutane su sanya bakinsu na magana da za ta gaskata tsarin da suka zo da shi. Ta hanyar amfani da fasahar ta AI suna sauya fuskar da muryar malaman coci da manyan ‘yankasuwa da manyan ‘yanjarida da masu tarin mabiya su yi dabarun da za a dauka daidaikun mutanenne suke ba da kwarin gwiwa cewa tsari ne mai kyau, wannan na sanyawa mutane su amince da abin da ake fadi cikin gaggawa duk kuwa da cewa duk abin hadawa aka yi karya ce ba su suke maganar ba.
Binciken fari na cibiyar ICIR ya nunar da cewa akwai tarin bidiyo na manyan mutane da aka hadasu da manhajar ta AI, misali a 2023 dantakarar shugaban kasar Najeriya karkashin inuwar jam’iyyar Labour Peter Obi da danmajalisa Saliu Mustapha, anyi amfani da su wajen tallata wani tsarin kasuwanci na mazambata.
A bidiyon na AI an nuna Mustapha fitaccen mai tallafa wa al’umma a Najeriya inda aka yi dabaru aka nuna yana cewa wannan tsari na da karfin amfani da fasahar AI da zai iya sharhi yayi hasashe na abin da ka je ya kawo, sannan wadanda suka yi rijista da tsarin idan suka zuba jari na N395,000 za su iya samun N1,580,000 a duk mako.
Saliu Mustapha a tallan da aka hada da fasahar AI
Shi kuwa Obi, a nasa bangare an hada nasa bidiyon ne wai yana cewa idan mutane suka zuba jari a wata harkar zuba jari ta mazambata za su iya samun kudi Naira miliyan 7 a duk wata.
Tsohon dantakarar shugaban kasar a rahoton an nunar da cewa yana fadin cewa wannan dama da hannunsa a wajen samar da ita da kuma samun goyon bayan gwamnatin tarayya,
Sai dai dukkanin abubuwan da ICIR ta gano ya nunar da cewa babu wani daga cikin wadannan bidiyo da ke zama sahihi.
- Alkawarin samun gwaggwabar riba
Tallace-tallace da ake hadawa da fasahar ta AI suna yawaita bayyana samun riba da hankali bai kamata ya dauka ba, wani lokaci su nunawa masu zuba jari cewa za su iya samun ninki na kudadensu. su kuma samu cikin sauri ba tare da wata fargaba ba, wadannan alkawura sun saba tunani na halastaccen kasuwanci wanda za ka ga babu tabbaci kan irin ribar da ake samu wani lokaci ma ayi asara. Ana ba wa mutane tabbaci na samun ribar ne don cire masu shakku da kuma jan hankali na mutane da idanunsu suke a rufe wajen neman ganin sun yi kudi ko ta halin kaka.
Ga misali a tsarin kasuwanci na CBEX, wanda yayi awon gaba da kudade ‘yan Najeriya da dama, yayi wa al’umma alkawari na samun riba da kaso 100 na abin da suke zuba jari a cikin kwanaki 30.
- Akwai fankama da rudani na abubuwan da ake fadawa mutane za su samu
Mai makon yi wa mutane bayani kan yadda wannan kasuwanci yake sai su rika amfani da wasu manyan kalmomi da ba kowa ya sansu ba, ko ba a fahimta ta yadda wanda zai zuba jarin ba lallai ya fahimci ta inda kudaden suke shigowa ba, Wannan rashin gaskiya shi ke sawa ba zaa fadawa mai zuba jari cewa zai samu kudinsa ne daga sabon mai zuba jari ba.
- Jan hankali sosai kan a isar da sakon kasuwancin ga wasu
Wadanda suka zuba jari a wannan kasuwanci ana karfafa masu gwiwa su gayyato wasu don su kara samun kudade,
Mai makon mayar da hankali kan abin da kamfanin ke samarwa sai a fi mayar da hankali kan neman mutane su zo su shiga wannan kasuwanci.Wannan tsari kuwa shi ke nuna cewa samun kudaden irin wannan kasuwanci ya dogara ne da sabbin wadanda suka zuba hannun jarinsu, wanda idan tafiyar ta ci gaba da tafiya a haka za a kai gabar da idan babu masu zuba jari sabbi sai kasuwancin ya fadi kasa baki daya.
Ga misalin, MMM da CBEX suna ba da ribar kaso 10 cikin 100 idan mutum ya kawo wani sabo ya sa hannun jarinsa, domin samun riba da yawa masu hannun jarin sai su bude asusu da dama ta hanyar nuna Link na cewa sun hada kamfanin da wasu wato (referral links).
- Dabarun matsin Lamba
Da dama irin wadannan tallace-tallace ana tsara su ta yadda mutum zai ji ya zaku yayi abin da aka umarce shi cikin gaggawa, wani lokaci sai su nuna cewa wannan damar na daf da karewa ko a ce damar kadan ta rage. Sai wadanda suka gani su gaggauta zuba jarinsu ba tare da sun gudanar da wani bincike ba. Sanya mutane su ji cewa sun zaku su aikata wani abu dabara ce da irin wadannan mazambata ke amfani da ita da ke hana mutane su zauna su yi tunani kafin yin wani abu.
- Shafuka ko adireshin intanet da ke zama abin zargi
Irin wadannan tallace-tallace ana wallafa su ne a sabbin shafuka da aka kirkira wadanda basu da wani tarihi mai tsawo, Shafukan ko adireshin na intanet sau tari suna maimaita yabo da aka yi masu wanda a lokuta da dama abin yana faruwa ne saboda an tsara yayi tayi kamar abin da za a kira otimatik wanda za a iya cewa ba na gaskiya ba ne.
Harkokin zuba jari na gaskiya ana ganinsu a shafukan intanet da bayanan tuntuba da ma bayanai na wasu da suka ziyarci shafukan, su kuwa irin wadannan shafukan na mazambata na bacewa da zarar kasuwancin ya durkushe.
- Bukatar biyan kudi ta hanyar da za a iya cewa ba a hukumance ba ko hanyar da zai zama da wahala a bibiye ta
Maimaikon amfani da wata cibiyar kudade sananniya ko wacce aka yi wa rijista mazambatan sau tari suna neman a biya kudade a wani asusu na wani mutum ko hanyoyi na kananan asusun ajiya na wallet ko wasu hanyoyi da hukuma bata san da su ba, hakan na sawa yayi wahala a dawo da kudade da suka sulale ta irin wannan hanya muddin aka ce tsarin kasuwancin zambar ya rushe, mazambatan sai su bace ba tare da an gano su ba.
- Ba su da amincewar hukuma ko yin rijista bisa doka
Yawancin masu irin wannan kasuwanci na zamba basa samun sahalewa ta hukumomi masu sa idanu kan hada-hadar kudade kamar hukumar da ke sa idanu kan hada-hadar kudade da basu tsaro a Najeriya wato SEC. Idan an tambayi masu gabatar da irin wannan kasuwanci halascin abin da suke sai su yi kokarin kaucewa tambayoyin da ake masu ko su rika ba da wasu takardu wadanda ke da alamun tambaya a kansu.
Halastaccen kasuwanci a ko da yaushe ana masa rijista kuma babu wata rufa-rufa kan abin da ya kunsa.
Wannan labari ya samu tallafin cibiyar Pulitzer Center. Za a iya karanta wani binciken da aka yi a baya kan tsarin da ke samun tallafin AI kamar a nan.
