Kiristoci da Musulmi suna addu'a tare. Asalin hoton: Reuters.
|
Getting your Trinity Audio player ready...
|
Da’awa: Wani mai amfani da shafin X ya yada wani bidiyo inda yayi da’awar cewa Musulmai sun kashe mabiya addinin Kirista su 500,000 a Najeriya cikin shekarar 2025.

Hukunci: Babu isassun shedu!Babu wasu bayanai da zaa kafa hujja da su cewa Musulmai ko wata kungiya ta kashe Kirista 500,000 kamar yadda mai da’awar ya nunar.
Cikakken Bayanin
Tun bayan da Shugaba Donald Trump na Amurka ya bayyana Najeriya a matsayin kasar da ya kamata a sa idanu a kanta, batun cewa Musulmai na aikata kisan gilla kan Kirista wani batu ne da ake ci gaba da bijiro da shi daga lokaci zuwa lokaci a tsakanin al’ummar kasar.
Kan dai wannan batu alal misali a baya-bayan nan wani mai amfani da shafin X ya yada wani bidiyo kamar yadda aka killace shi nan mai da’awar da baa fayace ba yana cewa “Musulmi sun kashe mabiya addinin Kirista 500,000” a Najeriya a cikin shekarar 2025.
Mutumin da yake magana a wani taro mai kama da taron kasa da kasa yace munafunci ne mutumin da ke fafutukar ganin an ‘yantar da Falasdinawa a kasarsa ake ci gaba da samun mutanen da ake kashewa.
“…Ina nufin zan iya fada maka cewa a shekarar da ta gabata sama da mabiya addinin Kirista 500,000 ne aka kashe a Najeriya cikin shekara guda kawai, babu kuma mutum guda da ya fito yayi adawa da hakan, ‘yanfafutuka babu abin da suke cewa. A wajena wannan munafunci ne “A arewacin Najeeriya ana kashe mabiya addinin Kirista a duk rana, saboda masu tsatstsauran kishin addinin basa son ganin mabiya addinin Kirista suna raye a arewacin na Najeriya,” a cewarsa.
Wannan wallafa ta sake dawo da muhawarar aikata “kisan kiyashi na Kirista” a kasar, inda da dama a masu amfani da shafin na X suke ganin abin da ake fada gaskiya ne, ya zuwa yanzu wannan wallafa ta samu wadanda suka kalla 300,000 da wadannan suka nuna sha’awarsu 49,000 da wadanda suka sake yadawa su 16,000.
Watanni da suka shude DUBAWA ta yi fatali da tarin da’awowi da ake bayyanawa cewa ana aikata kisan kiyashi kan mabiyan na addinin Kirista wadanda aka gano cewa karya ce kawai. Wannan batu na kisan kiyashi abune da ke bukatar taka tsan-tsan wannan ya sanya dole gudanar da binciken gano gaskiya kan batun.
Tantancewa
Da farkon fari mun gudanar da bincike ta hanyar gano asalin bidiyo, sakamakon ya nunar da cewa wannan bidiyo da fari an taba wallafa shi a shafin X a watan Satumba,2025 a wani shafin Blog mai suna Israel News Pulse. Ganin wannan bidiyo an wallafa a 2025 ya haska cewa mutumin da ke maganar cewa a “shekarar bara” yana nufin a 2024. Wannan shi ya haifar da tarin tambayoyi kan wane lokaci ne ake da’awa a kai.
Haka kuma a bidiyon babu inda Mutumin yace “Musulmai na kashe Kirista” sai dai abin da ya fadi aka ci a karshe shine masu “tsaurin kishin addini da sunan na Islama.”
DUBAWA ta lura cewa mai shafin na Blog ya juya kanun labaran ne don kawai ya haifar da muhawara. Mun kuma samu irin wannan wallafar da wani mai amfani da shafin Facebook wanda shima ya juya ma’anar taken labarin don kawai ya cimma manufarsa a shekarar bara.
Domin kaucewa duk wani rudani “Musulmai” da mai amfani da shafin na X ko Facebook suka bayyana suna nufin masu fafutuka da sunan Jihadi kamar Boko Haram da ISWAP da sauran kungiyoyi na ‘yanta’adda. Duk da cewa wadannan kungiyoyi sun kashe mabiya addinin Kirista da dama rahotanni sun nunar da cewa wadannan kungiyoyi sun kashe Musulmi da dama a Najeriya.
Domin tantance da’awar cewa an kashe mabiya addinin Kirista 500,000 a 2025 ko 2024, kamar yadda abubuwan da aka gano suka nunar, DUBAWA ta bincika don samo sahihin rahoto da ya tabbatar da abin da ake fadi, amma babu ko daya.
Kuma babu wani bayani ko da guda daya daga gwamnatin Najeriya wanda ya ba da bayani a fayyace kan adadi na Kiristoci da aka halaka a wadannan shekaru.
Abun da kawai aka gani shine bayanai daga ‘yansiyasa da masu fafutuka bayanan da ke zama masu karo da juna, akasari sun gaza ba da bayanai na hanyoyin da suka bi wajen tattara bayanansu ko tushen bayanan.
Ko da ma ace hanyoyin da suka bi na hakika ne, dukkanin rukunan da suka ba da bayanan a 2025 sun ba da rahoto ne na mutane 11,968.
Tsakanin watan Oktoba, 2024 da Satumba,2025, Open Doors International ta ba da rahoto cewa an kashe mabiya addinin Kirista 4,849 a fadin duniya. Daga cikin wannan adadi kungiyar ta bayyana cewa 3,490 an kashe su ne a Najeriya. Wannan adadi yayi kasa matuka idan aka kwatanta da mutum 500,000 da mai da’awar ke fadi. Idan ma aka zurfafa adadi mafi yawa shine 189,009, Kungiyar kasa da kasa ta (The International Society for Civil Liberties and Rule of Law (Intersociety), wata kungiya mai zaman kanta ta kafa hujja da wannan adadi a matsayin adadin Kirista da aka kashe a Najeriya sanadin aika-aikar masu Jihadi tun daga shekarar 2009.
Wani kaulin kuma shine daga Sanata a kasar Amurka Ted Cruz, wanda ake kafa hujja da fadinsa a tattaunawa da BBC yake cewa Kiristoci 50.000 ne aka kashe tun daga 2009 a Najeriya.
Saboda haka ganin cewa babu wani bayani daga mahukunta, ba daidai ba ne wani yayi da’awar cewa an kashe ‘yan Najeriya 500,000 ko a shekarar 2024 ko ta 2025.
A Karshe
Babu wata hujja mai kwari da ta bayyana cewa masu fafutukar Jihadi sun hallaka mabiya addinin Kirista 500,000 a Najeriya, ko da dai akwai mabanbantan bayanai na adadin wadanda aka halaka sai dai akwai tazara mai yawan gaske da abin da mai da’awar ke fadi.
