Getting your Trinity Audio player ready...
|
Cikakken Sakon
A wani hukuncin Kotun Koli da ya kafa tarihi a ranar Alhamis 11 ga watan Yuli, 2024 a Najeriya, kotun ta ba da cin gashin kai ga kananan hukumomi 774 da ke fadin kasar. Wannan na zuwa ne bayan da gwamnatin tarayya ta kai karar gwamnonin jihohin kasar 36 saboda yadda suke wasarairai da yadda suka ga dama da harkokin da suka shafi kananan hukumomin.
Gwamnati da ta samun jagorancin babban mai gabatar da kara na tarayya Lateef Fagbemi, ta nemi kotun ta ba da umarni da zai hana gwamnoni yadda suka ga dama da rushe zababbun shugabanni na kananan hukumomi da aka zaba ta hanyar dimukuradiyya.
Hukuncin Kotun Kolin ya karfafa batun cin gashin kai na kananan hukumomi a Najeriya. Tsawon sama da shekaru 20 gwamnatocin kananan hukumomi su fuskanci tasgaro a fadin Najeriya inda gwamnoni ke karbe kudaden da ake tura masu daga gwamnatin tarayya a tura masu kudaden ba wadatattu ba.
Wannan dama da gwamnatoci suka dauka ya taimaka masu wajen kara mallake kananan hukumomin ciki kuwa har da batun damar da suka samu na iya tube shugabannin kananan hukumi da al’umma suka zaba duk kuwa da cewa a kwai matsayar kotu da dama da ta nuna cewa aikata hakan haramun ne.
Dogaron da gwamnatocin kananan hukumomin ke yi bai rasa nasaba da yadda gwamnatocin ke yadda suka ga dama da wasu hukumomi, kamar hukumar zabe mai zamankanta mallakin jiha.
Haka kuma hukuncin kotun ya hadar da wasu muhimman abubuwan da suka kara sauya matsayin kananan hukumomin a Najeriya. Umarnin kotun ya tanadi cewa yanzu kai tsaye ne gwamnatocin za su rika karbar kudadensu daga ofishin akanta janar na kasa inda za su rika ratse gwamnatin jiha. Akanta Janar yanzu zai rika ba da kudi kai tsaye ga kananan hukumomi ba tare da jira ko katsalandan na gwamnatocin jiha ba.
Don haka duk wani rike kudaden gwamnatocin kananan hukumomi haramun ne, don hukuncin kotun ya haramta yin hakan, a rike masu kudade ana basu abin da bai taka kara ya karya ba.
Haka nan hukuncin kotun ya kara fito da damar da kundin tsarin mulkin kasa ya ba wa kananan hukumomin na zabin shugabanni karkashin dimukuradiya, ta kuma yi kakkausan suka kan yadda gwamnonin ke rushe shugabancin kananan hukumomin.
Har ila yau ta kara da cewa zaben na shugabannin kananan hukumomi wani bangare ne na tsarin zabin shuganni wakilai, ma’ana kananan hukumomi har yanzu za su dogara gwamnatin jiha wajen fidda shugabanni sahihai da za su yi jagoranci.
Nakasu da ke tattare da hukuncin
Francis Oronsaye, babban jami’i a Heritage Attorneys ya yabawa hukuncin babbar kotun saboda yadda ta ba wa kananan cin gashin kai a harkokin kudadensu, dama hana gwamnoni yi masu kutse kan kudadensu, yace wannan hukunci ya karfafi kananan hukumomi ta yadda al’umma a can kasa za su fi amfana a fadin kasar.
Wannan kuma zai kara kafafa umarnin ko oda mai lamba (No. 10) da Muhammadu Buhari ya tsohon shugaban Najeriya ya bayar a lokacin mulkinsa a 2010, wacce ta kara karfi ga kananan hukumomin.
“Ko da yake ba wannan ne karon farko ba da aka bawa kananan hukumomin cin gashin kai kamar yadda yake a shari’ar (GOVERNOR OF EKITI STATE V OLUOMO (2017) 3 NWLR (PT 1551),) wacce ta ba da umarnin cewa a rika biyan kudade kai tsaye ga kanan hukumomin,” a cewarsa.
”Har yanzu tsugune ba ta kare ba a dangane da batun bawa kananan hukumomin kudaden su kai tsaye, kasancewar gwamnonin na da iko kan wasu batutuwa da suka shafi kananan hukumomin. Sakamakon da ake son samu ba lalle ba,” a cewarsa.
Ya kara da cewa “Kowace jiha na da dokoki da suka shafi kananan hukumomi kamar yadda yake a sashi na bakwai daya cikin baka na kundin tsarin mulki. Sun banbanta daga jiha zuwa jiha, wasu na da tsare-tsare da ke zama sila ta cigaba ko bunkasar kananan hukumomi, hakan kuma na nufin suna iya ragewa kananan hukumomin karfi. ”
Sai ya ba da misali da yadda gwamnoni ke iya wasa ko suyi rikon sakainar kashi da wa’adin mulkin shugaban karamar hukuma, ta hanyar sanya kwamishinan kula da kananan hukumomi ya takaita kudade da zai amince ayi amfani da su a karamar hukuma ko ma su zama kanwa uwargamni a tsige wani shugaban karamar hukuma kasancewar wannan karfin iko an bawa gwamnonin jiha.
“Tambayar itace muddin aka ce gwamnatocin jiha na da iko kamar yadda kundin tsarin mulki yayi tanadi su iya fitar da dokoki na kananan hukumomi, sannan su gudanar da zabukan kananan hukumomi, matsalar ba za ta kauce ba nan kusa. Akwai dai kiraye-kiraye cewa Hukumar Zabe mai Zamanta Kanta ta Kasa ta rika gudanar da zabukan kananan hukumomi.”
Haka kuma akwai bukatar a yi gyara a sashe na 162(6) na kundin tsarin mulkin kasa wanda ya tanadi samar da asusun hadaka,” a cewar Mista Francis.
Karshe
Yayin aka samar da ‘yancin cin gashin kai ga kananan hukumomi wanda ake ganin ci gaba ne irin na dimukuradiyya, akwai dai wasu tarnakai ga aiwatar da shi. Sai an yi gyara ne ga kundin tsarin mulki ta yadda gwamnatin tarayya za ta iya tasiri kai tsaye a kananan hukumomi ta haka ne za a ga tasirin hukuncin ga al’umma da ke a can kasa.