Zargi: Jaridar Daily Trust ta yi rahoton cewa gwamnatin tarayya, ta amince a karawa wasu manyan ma’aikatan gwamnatin da aka zaba a Najeriya, yawan albashinsu da kusan kasji 114 cikin 100
Sakamakon Bincike: Babu cikakkiyar gaskiya. DUk da cewa hukumar kula da yadda ake raba arzikin kasa ta amince a yi wa sabuwar gwamnatin Najeriyar karin albashi, sabuwar majalisar zartarwar ba ta kai ga amincewa da shawarar ba.
Cikakken bayani
Tun bayan da aka rantsar da sabon shugaban kasa Bola Tinubu a matsayin shugaban kasar Najeriya ranar 29 ga watan Mayun 2023, ya ke aiwatar da sabbin manufofin da kawo yanzu har sun fara tasiri kai tsaya a tattalin arzikin kasar. Kan gaba a cikin wadannan manufofin shi ne janye tallafin man fetir wanda ya jefa ‘yan Najeriya cikin wani yanayi na kunci tunda a halin da ake ciki, farashin kudin abinci da na abun hawa duk sun yi tashin gwauron zabi.
Wasu daga cikin shawarwarin da ‘yan kasa suka bai wa hukumar wadanda ya kamata ta yi la’akari da su sun hada da rage yawan albashin ‘yan siyasan da aka zaba zuwa mukaman gwamnati. To sai dai ribibin da ake yi na neman rage yawan kudin da ake batarwa kan ayyukan siyasa na cigaba da gamuwa da kalubale ko a gwamnatin da ta shude ta tsohon shugaba Muhammadu Buhari.
Dan haka ne ya kasance abun mamaki da jaridar Daily Trust ta ranar 21 ga watan Yunin 2023 ta bayyana cewa Gwamnatin Tarayya ta Hukumar Kula da yadda ake raba arzikin kasa da Albashi (RMAFC) ta amince a kara wa ‘yan siyasa albashi da kashi 114. Babban taken jaridar cewa ya yi “Gwamnatin Tarayya ta amince da karin albashin Tinubu, shettima, gwamnoni da wasu da kasji 114 cikin 100.” jaridar People’d Gazette ita ma ta dauki labarin, kuma ita ma jarida ce mai sahihanci.
Jaridun biyu duk sun yi amfani da kamfanin dillancin labaran Najeriya na NAN a matsayin majiyarsu wanda ke bayanin cewa shugaban hukumar, Muhammad Shehu, ne ya yi wannan batun yayin da ya ke gabatar da rahoton albashin gwamnan jihar Kebbi, Dr Nasir Idris wanda aka yi bita ranar 20 ga watan Yuni a birnin Kebbi. Shugaban hukumar wanda kwamishanar tarayya, Rakiya Tanko- Ayuba ta wakilta ya ce a tun da aka gyara albashin a shekarar ta 2007 ba’a sake ba.
Tun bayan da aka wallafa labarin, ya ke samun martanonin da ke kakkausar suka daga ‘yan Najerya, wadanda ke zargin cewa kudin da ake kashewa wajen gudanar da ayyukan kasar ya yi ywa sosai.
Haka nan kuma kungiyar da ke da rajin jare hakkokin yanayin zamantakewa da tattalin arziki dan tabbatar da inganci da cigaba dan gudanar da ayyika a bayyane, wato (SERAP) ta yi kira ga gwamnati da ta yi watsi da wannan “tayin mara kan gado” ko kuma ta fuskanci kotu.
Kadan daga cikin labarin da aka wallafa a twitter na cewa: “Labarai da dumi-duminsu: Ya kamata gwamnatin Tinubu ta yi watsi da wannan tayin na cewa a kara kudin albashin jami’an gwamnatin da aka zaba da kashi 114 cikin 100, da kuma kashe nera biliyan 24 kan wuraren zaman mambobin ‘yan Majalisa ta 10. Za mu hadu a kotu idan har ba’a janye wadannan kiraye-kirayen ba.
Labarin na twitter ya ce tayi ne aka gabatar ba wai an riga an amince da shi ba kamar yadda kafar yadda labaran ta bayyana. DUBAWA ta gudanar da bincike dan fayyace abun da ke kawo rudani.
Tantancewa
Sashi na 84 na kundin tsarin mulkin Najeriya (1999) ya baiwa hukumar ikon yanke hukunci kan yawan kudin albashin da ya kamata a biya ‘yan siyasa da wadanda ke rike mukaman gwamnati, yayin da karamin sashe na hudu ya bayyana wadanda suka cancanci samun karin albashin. Wadannan sun hada da masu aiki a fannin shari’a da mukaman gwamnati a matakin tarayya, yayin da sashi na 124 karamin sashe na hudu (4) ya bayar da iko a matakin jihohi.
Sashi na 70 ya ayyana cewa ‘yan majalisar da ke matakin tarayya za su iya samun karin albashi daga hukumar, wadda kuma ta sake yin la’akari da ‘yan majalisar a sashi na 111.
Sai dai akwai wadansu matakan da dole sai an dauka kafin a kai ga karin albashin. Misali sai shugaban kasa ya amince da karin bayan an gabatar da shi kamar yadda aka bayyana a sashi na 294 (2).
A cewar sashin, “Idan har za’a yi amfani da ikon da ke karkashin karamin sashe na daya (1), bai kamata a bayar da ikon ga wani ko jami’in da ke aiki a matakin tarayya ba tare da izinin shugaban kasa ba.”
Tilas ne shugaban kasa ya kira taron majalaisar ministoci kafin ya cigaba. A cewar babi na 6 sashi 148 (2c). Daga 21 ga watan Yunin 2023, shugaban kasa bai riga ya amince da majalisar ministocin da za su iya ba shi shawara ba.
Haka nan kuma, shugaba Tinubu a halin da ake ciki yana birnin Paris inda ya ke halartar wani taron koli dangane da sabbin hanyoyin kulla hadaka na samun kudi wanda shugaban kasar Faransa, Emmanuel Macron ya shirya ya ke kuma karbar bakunci.
Wannan rahoton ya ce an fara sabon albashin ne daga daya ga watan Janairun 2023 a karkashin gwamnatin shugaba Buhari. Sai dai reshen gudanarwar gwamnati da majalisun dokokin kasar guda biyu ba su samu ba, amma reshen shari’a da wasu ma’aikatan sun ci gajiyar wannan karin.
Ta bakin jami’in hulda da jama’arsa, (PRO) Christian Nwachukwu, hukumar ta yi tsokaci dangane da rahoton inda ta fito ta bayyana cewa Tinubu bai amince da karin albashin ba
A karshe
Yayin da ya kasance lallai gaskiya ne hukumar ta yi tayin kara albashin ‘yan siyasar Najeriya da kashi 114 cikin 100, dole sai reshen da ke gudanar da gwamnati da majalisun dokokin kasar sun amince da tayin, kuma kawo yanzu ba’a riga an kammala hada su bu. Shi PRO din na hukumar ta RMAFC ya fayyace cewa shugaban kasar bai amince ba tukuna, dan haka rahoton ba daidai ba ne.