African LanguagesHausa

Shin da gaske ne an yi yunkurin kashe Shugaban Kasar Rasha Vladimir Putin a kwanan nan?

Getting your Trinity Audio player ready...

Da’awa: Wani mai amfani da Facebook ya yi da’awar cewa Ukraine ta kai wa shugaban shugaban Russia hari a cikin motarsa a birnin Moscow.

Shin da gaske ne an yi yunkurin kashe Shugaban Kasar Rasha Vladimir Putin a kwanan nan?

Hukunci: Gaskiya ne. Jaridar The Sun da kuma The Express sun tabbatar da cewa an yi yunkurin kashe shugaban kasar Vladimir Putin, amma fashewar ta shafi daya daga cikin motocinsa ne kawai.

Cikakken Bayani

Tun a watan Fabrairun 2022 ne ake ci gaba da gwabza fada tsakanin kasar Ukraine da kasar Rasha, bayan da Rasha ta fara mamaye wasu sassa na kasar Ukraine, yakin da a yanzu ya shafe shekaru uku.

A yanzu dai ana ci gaba da zaman tattaunawar sulhu a kasar Saudiyya domin lalubo hanyar da za a tsagaita bude wuta, wadda ake tunanin za ta kai ga kawo karshen yakin baki daya.

Ana tsaka da haka wani mai amfani da shafin Facebook (Alhaji Abdulrahman Shakundum) ya wallafa wani bidiyo wanda yake sharhi, a ciki ya yi da’awar cewa Ukraine ta kai wa Shugaban Rasha Vladmir Putin hari a cikin motarsa. Bidiyon ya nuna yadda wata mota ke ci da wuta yayin da jami’an kashe gobara ke kokarin kashe wutar.

A saman bidiyon ya rubuta cewa “Kutaya putin da addu a” yayin da ya fadi cewa ba a san halin da shugaban na kasar Rasha yake ciki ba bayan wannan harin da aka kai masa.

Zuwa ranar Talata 1 ga watan Afrilu, 2025, sama da mutane 1,000 suka dannan alamar so, 59 su ka yi sharhi yayin da 138 suka yada shi.

Wasu mabiyansa irin su Muhammad Alfa sun yarda da wannan labarin domin har rubutawa ya yi “Da yarda Allah yana Raye ko kwarzani.” Sai dai Isah M Hassan bai yarda ba domin ko yace wannan karyar banza ce.

Shi kuwa Abdul Yusuf ya yi martani tare da zargin cewa “Wannan aikin America ne Ba Ukraine ba, Sunyi anfani da sulhu wajen ganin bayan shi”

Hakama a kwanannan a manhajar tantance labarun gaskiya, an bukaci DUBAWA ta bincika gaskiyar labarin da ke cewa an yi yunkurin kashe shugaban kasar Rasha Vladimir Putin, wannan ne ya sa DUBAWA yin bincike domin tabbatar da sahihancin labarin.

Tantancewa

Dubawa ta fara bincike a sashen nema na Google, inda ta gano cewa jaridar The Sun da The Express sun wallafaa faifan bidiyon a ranar 29 ga Maris, 2025. Kafofin yada labarai sun ruwaito cewa fashewar wani abu a motar Putin kirar limousine a birnin Moscow. 

Jaridar The Sun ta ruwaito cewa hotunan da aka dauka kusa da wurin sun nuna cewa gobarar ta tashi ne daga injin kuma ta koma cikin motar kirar Aurus Senat wadda kudinta suka kai Yuro E275,000. Bayan tashin gobarar, ma’aikatan gidajen cin abinci dake kusa da wurin sun yi kokarin kai dauki domin kashe wutar.

Jaridar Hindustan Times ita ma ta ruwaito lamarin. 

Wannan dai ba shi ne karon farko da ake yiwa shugaban kasar Rasha kisan gilla ba. Putin da kansa ya bayyana cewa ya tsallake rijiya da baya a yunkurin kashe shi.

A Karshe

Da’awar mai amfani da Facebook din gaskiya ne. Kafofin yada labarai masu inganci sun tabbatar da faruwar lamarin.

Show More

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
Translate »