Da’awa: Wani shafin Facebook mai suna @Culture Collective ya fitar da wata wallafa inda yace birnin New York ya cimma nasara a karon farko an yi maganin cutar sikila.

Hukunci: Yaudara ce. Ko da yake mara lafiyar a birnin New York, Sebastien Beauzile, an yi nasarar yi masa aikin maganin sikila ta hanyar amfani da dashen kwayar halittar jini, wannan ba shi za a bayyana ba a matsayin karon farko na magance cutar ba, akwai marasa lafiya da aka yi masu maganin cutar tun a shekarun 1980 ta hanyar dashen bargo.
Cikakken Labari
Cutar Sikila cuta ce da ake gadonta matsala ce ta jini wacce ke shafar yanayi da jini ke da shi da halayyarsa, wannan na sanyawa jinin baya tafiyarsa yadda ya dace babu isasshiyar iskar oxygen a jikinsa, hakan kuma na sanyawa a samu karancin jini da ma wasu cutuka daban-daban.
Bayanan ilimi na lafiya ya tattara abun da ya shafi tarihin wannan cuta inda a karon farko wani masani a wannan fanni Baamurke James B. Herrick a 1910 ya ba da rahoton gano kwayar halittar jini wacce ke kama da jaririn wata maimaikon cikakken wata wanda ake iya kira rawul bayan gwada jinin wani mara lafiya daga yankin Karebiya. Nazari na daga baya kuma sai ya nunar da cewa wannan rashin lafiyar gadonta ake yi abu ne da ya shafi kwayoyin halittar jini da na gado.
Wannan matsalar ta rashin jinin ta fi zama sananniya daga mutanen Afurka ana kuma samu a mutanen Yankin Gabas ta Tsakiya da Indiya da yankin Meditareniya da yankin Latin Amurka. Yaro na gadar cutar ne daga kwayoyin halitta daga bangaren iyayensa biyu.
A baya-bayan nan shafin na @Culture Collective ya yada wannan da’awa a shafin Facebook cewa wani mara lafiya a birnin New York an warkar da shi daga cutar amosanin jini ta Sikila a karon farko.
Taken labarin wanda aka makala hoton wani matashi ya nuna cewa “Samun sauyi a fagen rayuwa! Birnin New York shine na farko da ya samar da waraka daga cutar sikila abin da zai samar da fata ga miliyoyin al’umma.”
Ya zuwa ranar 23 ga Disamba,2025 wannan wallafar ta samu wadanda suka nuna sha’awarsu (likes) 5000 da tsokaci (comments) 201 da wadanda suka sake yadawa (reposts) 851.
Daga bangaren masu tsokaci @MaryAnn Duncan Ganzel ta mayar da martani da cewa “Abin mamaki! Ina fatan wannan labarin gaske ne.”
@Shirley James ta yada cewa, “Dan ‘yaruwata na da wannan ciwo,
Yanzu shekarunsa sun kai 20, yana fama da wannan cuta a Trinidad, ina zaune a Kanada, Ina addu’ar samun sauki.”
@Margarita Villaronga yayi tsokaci ne da cewa “gaskiya wannan labari ne mai dadi.”
@Edwin Jernigan ya kara da cewa , “Ina tayaka murna, ina da shekaru 62, ina jira da fatan samun waraka.”
@Arturo Villanueva ya alamta cewa, “Na yi amanna cewa wannan ya faru ne a 2024, amma duk da haka labari ne mai dadi ko ma daga ina ya fito.
@Shana Gordon na martanin cewa, “Wannan babban labari ne.”
@Eberle Gongora tayi tambaya da cewa, “Ta yaya zan samu wannan waraka? Ina da wannan cuta ta sikila ana yi min sauyin jini bayan watanni uku zuwa biyar.”
@Lois Best ta bayyana fatanta ne, “Ina fatan wannan magani zai zama na kowa da kowa ne.”
Ganin cewa wannan batu na da alaka da lafiya, kuma ganin abu ne da zai dauki hankali shirin DUBAWA ya ga dacewar gudanar da bincike.
Tantancewa
DUBAWA ta fara da bincikar rahotanni ko za a samu wata kafa sahihiya da ta tabbatar da samun wannan labari cewa an warkar da mai cutar ta sikila a birnin New York.
Mun samu tarin rahotanni daga kafafan yada labarai na kasa da kasa da wallafe-wallafe na masana kiwon lafiya, dukkanin wadannan rahotanni sun yi magana ne kan wani mara lafiya guda daya wanda aka warkar da shi ta hanyar dashen kwayoyin halitta na (gene) wanda aka yi aikin a New York.
A cewar rahotanni matashi dan shekaru 21 mazaunin Long Island Sebastien Beauzile, ya karbi shirin kula da lafiya na sauyin kwayoyin halitta (gene) da ake kira Lyfgenia a ranar 17 ga Disamba,2024 a asibitin yara na Cohen Children’s Medical Centre da ke New Hyde Park a New York. Kafin yi masa aiki bayanai sun tabbatar da cewa wannan matashi ya rayu da wannan cuta tun yana karamin yaro a tarihinsa ya rayu da alamomin cutar.
Asibitin yara na Boston yayi bayani a wani nazari cewa Lyfgenia tsarin samar da waraka ne ta hanyar dashen halittar jini wanda ya samu amintar hukumar abinci da magunguna ta Amurka wajen yin maganin cutar sikila. Karkashin wannan tsari likitoci na daukar jinin mara lafiya ne su je su zauna a dakin gwaji ayi masa gyara irin na masana a samu jini me kyau kafin mayar da shi jikin mara lafiya. Wannan na sanyawa jikin mara lafiya ta hanyar bargo ya rika fitar da lafiyayyen jini ba irin wanda masu cutar sikila suke fitarwa ba.
A watan Maris 2025, Forbes ta fitar da rahoto da ya nunar da cewa wannan tsari da aka bi aka yi wa Beauzile magani ya nuna cewa hanyar magance cutar tana aiki inda ake samar da jini mai kyau a jikin mara lafiya.
Kafar yada labarai ta CBS News ta fitar da rahoto cewa wannan tsarin kula da lafiya anyi amanna cewa shine na farko da aka yi a New York wanda aka yi ta hanyar yin dashe na (gene) sai dai yayi bayani cewa wannan hanyar maganin an yi ta ne ga mara lafiya guda daya, wanda kuma bai zamo hanyar da za a magance wannan cuta ga kowa ba wanda ke da cutar ta sikila.
A shekarar 1984 nazari da aka wallafa a dakin karatu na abubuwan da suka shafi ilimin kiwon lafiya, ya nunar da cewa warkar da mai cutar sikila ba a New York aka fara ba. Nazari ya nunar da cewa likitoci na cibiyar cutar kansa ta Fred Hutchinson ta Seattle, Amurka ta yi nasarar magance wannan cuta ta hanyar dashen bargo karkashin kulawar Dr Donnall Thomas.
Sauran marasa lafiyan sun samu waraka ta hanyar amfani da wannan tsari.
Mahangar Kwararru
DUBAWA ta tuntubi Aminu Babale,na asibitin koyarwa na Malam Aminu Kano wanda ke duba marasa lafiya kananan yara kan wannan cuta. Yace cutar da ke zama gadonta ake yi yana da wahala a magance ta.
Yace “Magance cutar sikila na nufin kawar da duk alamun cuta da gyara matsalar da ke jikin jinin, ba kawai a ce an magancewa mutum cuta ba.Dashen jinin da aka yi na wani mutum ne guda da aka yi nasara a kasar waje, inda aka gyara halittar jini da ke a jikin mai wannan cuta.”
Aminu ya kara da cewa aikin dashen na da sarkakiya, mataki ne ake bi daki-daki likitoci na daukar kwayar halittar jini ta mara lafiyar sai a je dakin gwaji a gyara shi a kuma dawo da shi jikin mara lafiyar bayan gyara.
DUBAWA har ila yau ta yi magana da Ezra John, likitan yara a cibiyar kula da marasa lafiya ta tarayya (FMC), Gombe yace wannan dashen jini da ake ga masu cutar sikila ba a taba yi ba a Afurka. Irin wannan aiki na bukatar dakin gwaji babba da ma’aikata kwararru, da bin ka’idoji masu tsauri wadanda ba kasafe ake da su ba.
“Dashen bargo shine hanyar magance cutar sikila a Najeriya hanyar da ake bi ana bukatar lura sosai kan wane mara lafiya za a yiwa da kayan aiki na musamman da bibiya sosai. Wannan hanyar magance cutar na ba da karfin gwiwa amma tana da tsada ba kuma kowane mara lafiya ba ne ke da wannan dama, don haka muna bukatar kayan aiki da zuba jari.’ a cewarsa.
A Karshe
Binciken DUBAWA ya gano cewa batun warkar da Sebastien Beauzile gaskiya ne ta hanyar dashen jini a New York a 2024 amma wannan ba shine karon farko ba da ake warkar da cutar a bayanan da aka tattara.
