|
Getting your Trinity Audio player ready...
|
A watan Nuwamba,2025 tattaunawa ta yi tsauri kan batun cewa akwai kisan kiyashi na mabiya addinin Kirista a Najeriya. Yayin da wasu ke cewa mabiya addinin Kirista suke kan gaba wajen yi masu kisan kare dangi a harin da masu tsaurin kishin addinin Islama ke kaiwa, wasu kuma da dama sun yi watsi da wannan da’awa inda suke cewa masu tsaurin kishin addinin suna kai harin ne ga Kirista da Musulmai da masu bautar gargajiya.
Ana tsaka da wannan muhawara ne sai wasu daidaikun mutane suka rika yin da’awa wacce ba a tantance ba kan wannan batu, DUBAWA ta duba sahihanci na wadannan da’awowi. Wadannan da za a zayyano a kasa sune biyar mafiya yin shuhura cikinsu. wadannan da’awowi.
- Wani mai amfani da shafin X ya nuna wani dan kunar bakin wake da aka kama
Ana tsaka da wannan muhawara kan cewa ana yi wa mabiya addinin Kirista kisan kare dangi a Najeriya, wani mai amfani da shafin X ya nuna wani mutum ya bayyana kansa da cewa yana kokari na kai hari ne na bam a majami’a. Mai amfani da shafin na X yace an tsara ne don a alakanta abin da mabiya addinin Musulinci.
Sai dai, DUBAWA a bincikenta ta Google kan hoton ta fahimci cewa wannan bidiyo an yada shi a shafin Facebook a watan Fabrairu,2020.
Wallafar da Kennis 104.1FM ta dora ta nuna cewa a ranar Lahadi 1 ga Fabrairu,2020, wani mai suna Nathaniel Samuel dan shekaru 30 an kama shi da ababen fashewa a majami’ar Living Faith Church, da ke a Sabon Tasha wacce aka fi sani da suna Winners’ Chapel. Nathaniel ya bayyana cewa shi mabiyin addinin Kirista ne ba Musulmi ba, sabanin abin da al’umma ke da’awa.
DUBAWA ta kuma gudanar da bincike ta hanyar Google don gano harin da aka kai majami’a a Kaduna sai ta gano jaridar Punch ta wallafa labari cewa an kama wani da ake zargin dan kunar bakin wake ne mai suna Nathaniel Samuel. Jaridar ta Punch ta kara da cewa a na’urar CCTV ne aka gano wani motsi na Nathaniel a cikin majami’ar inda jami’an tsaro suka damke shi.
Ana iya kara karantawa a nan.
- An yi garkuwa da Rabaran Ezekiel Dachomo a jihar Kaduna
Fitaccen faston nan Ezekiel Dachomo, ya kasance fitacciyar fuska idan ana magana kan batun kisan kiyashi na mabiya addinin Kirista a Najeriya. Yana yada bidiyo na kisan ada akewa mabiya addinin Kirista a jihar Plateau. Wannan batun ne ya sanya a ke maganarsa anan.
Sai a binciken DUBAWA ta fahimci cewa babu wata kafar yada labarai sahihiya da ta ba da rahoto kan wannan batu. A karin bincike sai muka ga bidiyon da aka dora a shafin YouTube na kafar yada labaran News Central inda ta nuna tattaunawa da Dachomo inda yake tattaunawa da ‘yarjarida Blessing Mosuga a ranar 11 ga Nuwamba, 2025. Lokaci a nan na da muhimmanci kasancewar mai amfani da shafin na Facebook ya yada wannan bidiyo kwana guda kafin tattaunawar.
Kari kan wannan a da’awar ya nunar da cewa an kama Dachomo a jihar Kaduna sai dai kuma shi yana zaune ne a jihar Plateau inda yake zama jagora na shiya a Church of Christ in Nations (COCIN).
DUBAWA ta tuntubi malamin majami’ar inda ta tabbatar da cewa babu abin da ya same shi.
Za’a iya kara karantawa a nan.
- ‘Yanta’addar Fulani sun yanke kan shugaban kungiyar mabiya addinin Kirista a Najeriya CAN reshen jihar Adamawa.
Ana tsaka da wannan dambarwa kan batun cewa ana yi wa mabiyan addinin Kirista kisan kare dangi a Najeriya, sai wani mai amfani da shafin Facebook ya yada wani bidiyo na Television Continental (TVC) wanda ya nuna cewa Fulani masu tststsauran kishin addini sun yanke kan shugaban kungiuyar mabiya addinin Kirista (CAN) reshen jihar Adamawa.
DUBAWA bayan gudanar da bincike ta hanyar amfani da wasu muhimman kalmomi ta ga wani bidiyo irin wannan na gidan talabijin na TVC.
DUBAWA ta lura cewa wannan bidiyo an wallafa shi a YouTube a 2020. A karamin bidiyon shugaban kungiyar ta CAN a Adamawa Steven Manza na ba da bayani cewa Boko Haram ta yanke kan Lawan Andimi, shugaban kungiyar ta CAN a karamar hukumar Michika, jihar Adamawa.
Sai dai a rahoto da kafar yada labaran Guardian ta fitar ta ba da rahoto cewa Kungiyar matasan CAN wato (YOWICAN) ta yi watsi da da’awar cewa batun yanke kan shugaban kungiyar CAN mai ci yanzu a jihar Adamawa karya ne.
Za a iya kara karantawa a nan.
- Gwamnati bata dauki mataki ba bayan kisan gilla a Owo
Ana tsaka da muhawara mai zafi kan batun kisan kiyashi na mabiya addinin Kirista a Najeriya, wani mai amfani da shafin Facebook yayi da’awar cewa ana tsara kai hare-hare ne a Najeriya a kokari na kawar da mabiya addinin Kirista a kasar, kuma gwamnatin Najeriya ta gaza daukar matakin shari’a kan batun, sai ya kafa hujja da kisan gillar da aka yi a majami’a a Owo inda yace an kashe sama da mutane 50 a harin, kuma har kawo yanzu babu wanda aka kama ko aka gurfanar a gaban shari’a.
Sai dai binciken DUBAWA ya gano cewa mahukunta sun kama wadanda ake zargi suna da alaka da kai harin da gurfanar da su a babbar kotun tarayya da ke Abuja. Wadanda ake zargin sun ce babu hannunsu a harin, an kuma kama su aka tsare a hannun jami’an tsaro na farin kaya na (DSS).
A watan Nuwamba,2025 hukumar tsaron ta DSS ta ba da tabbaci cewa ta gurfabar da wadanda take zargi da hannu a harin majami’ar ta Owo bisa zargin aikata laifin ta’addanci.
Za’a iya kara karantawa a nan.
- Bidiyon TikTok da ke nuna yadda aka kai hari tare da kona wani ginin coci a Arewacin Najeriya
A ranar Litinin 3 ga Nuwamba,2025 wani mai amfani da shafin TikTok ya yada bidiyo da ya nuna yadda wani gini ke ci da wuta sai yayi da’awar cewa wani ginin majami’a ne yake cin wuta a Arewacin Najeriya
A binciken DUBAWA a Google ya nunar da cewa akwai wasu bidiyon irin wannan a TikTok da Facebook da Instagram.
Wadannan bidiyo sun nuna cewa gobara ce ta tashi a kwalejin koyon aikin jinya ta Kwapong a kasar Ghana.
Mun ga rahoto da kafar yada labarai ta Modern Ghana ta wallafa a ranar 31 ga Oktoba,2025 wacce ta ba da rahoto na tashin gobara a wani bangare na kwalejin koyon aikin jinya ta Kwapong a lardin Asunafo ta Kudu a ankin Ahafo na Ghana dalilin da ya sanya dalibai suka fice don tsira.
Za’a iya kara karantawa a nan.
