|
Getting your Trinity Audio player ready...
|
Da’awa: Gwamnan jihar Neja Umaru Bago na da’awar cewa wani rahoton da UNICEF ta fitar na hasashen wai a shekara ta 2027 ba za’a sami dalibi namiji ko daya ba a azuzuwan farko na makarantun sakandaren da ke kananan hukumomin Shiroro da Munya a jihar domin yaran duk sun bar makaranta suna hakar ma’adinai yanzu

Hukunci: Karya ce. UNICEF ta fadawa DUBAWA cewa ba ta gudanar ko ma bayar da izinin gudanar da binciken da ya duba tasirin da aikin hakar ma’adinai ya ke yi kan zuwa ko kasancewa a makarantun da ke kananan hukumomin Shiroro da sauran wasu a jihar Neja ba.
Cikakken bayani
Kwanann nan ne gwamnan jihar Neja Umaru Bago ya yi da’awar cewa wani rahoton UNICEF ya yi hasashen cewa nan da shekara mai zuwa ta 2027 a wasu daga cikin yankunan jihar ba za’a sami yara maza a azuzuwan farko na makarantun sakandare ba sakamakon yadda suka shiga aikin hako ma’adinai a jihar.
Bago ya yi wannan furucin ne yayin da ya ke wata hira a tashar gidan talibijin na Channels a shirin siyasar da sukan yi ranar lahadi mai suna Sunday Politics.
Wannan hirar ta zo ne a daidai lokacin da ake nuna damwa dangane da mutuwar yara 37n da ake zarginsu da hakar ma’adinai ta haramtaciyyar hanya, a hannun jami’an NSCDC na jihar Nejar.
An kama yaran da ake zargin ne bayan da aka kai wata samame na neman masu hakar ma’adinan ta bayan fage a yankunan M.I. Wushishi da Lukoto a ranakun 15 da 16 na watan Satumban shekarar 2026. A cewar tashar talibijin na Channels Television, yara matasa 67 aka kama inda daga baya 37 daga cikinsu suka rasa rayukansu. Har yanzu ana gudanar da binciken gano abubuwan da suka yi sanadin mutuwarsu.
Da ya ke bayani kan tasirin da hakar ma’adinan ke yi kan al’ummomin jihar, Bago ya ce: “MUn san cewa hakar zinari yanzu ya zama ruwan dare. Rahoton UNICEF kan kananan hukumomin Shiroro da Munya ya ce a shekara ta 2027 ba za’a sami namiji ko daya ba a ajin farko na makarantun sakandaren da ke yankin. Kun gane? Saboda dukansu sun daina zuwa azuzuwa yanku sun koma hakar ma’adinan karkashin kasa. Kuma wannan babbar matsala ce a gare mu.”
Tashar ta Channels ta kuma yi rahoton da ya bayyana gwamnan ya na wannan furucin. Dan haka ne DUBAWA ta yanke hukuncin gudanar da bincike kan wannan lamarin domin ya na da mahimmanci ga al’umma musamman ganin yadda ake la’akari da tshar a matsayin daya daga cikin tashoshin da ke da nagarta wajen watsa labarai.
Tantancewa
Ganin yadda a kai tsaye gwamnan ya ambato UNICEF, DUBAWA ta fara ta yuntubar ofishin UNICEF a Najeriya dan jin ko ta gudanar da bincike kan tasirin hakar ma’adinan a kan daliban sakandaren da ke zuwa makaranta a karamar hukumar Shiroro da wadanda ke kusa da ita a jihar Neja.
Haka nan kuma mun tambayi kungiyar ko za ta iya nuna mana rahoton ta kuma fayyace mana inda ya yi wannan hasashen na rashin dalibai maza a azuzuwan farko na makarantun sakandare sakamakon hakar ma’adinai.
Da ta ke mayar da martani ta bakin wakilinsu na musamman kan sadarwa Samuel Kaalu, UNICEF Najeriya ta ce ba ta taba gudanar da bincike irin wannan ba.
“UNICEF ba ta taba gudanar da bincike ko ma bayar da izinin gudanar da bincike kan tasirin hakar ma’adinai kan yanayin zuwa makarantar yaran da ke zuwa hako ma’adinai a karamar hukumar Shiroro da wasu kananan hukumomin da ke jihar NEja ba,” Kaalu ya bayyana cikin wani sakon imel din da ya turawa
Ko da shi ke ya bayyana cewa UNICEF ta tallafawa wani binciken da aka yi wa taken “Tasirin Rashin Tsaro kan Samar da Ilimi a jihohin Katsina, Zamfara da Neja.”
Bisa bayanan Kaalu, UNICEF ta tallafawa ma’akatar kula da ilimin firamare da sakandare wajen gudanar da wannan binciken.
“Wannan binciken ya gudana ne a kananan hukumomin Shiroro, Munya da Rafi, inda ya yi nazarin tasirin rashin tsaro, a ciki har da maharan daji, yin garkuwa da jama’a da ma hare-haren kan makarantu da rigingimun da akan samu tsakanin al’ummomi kan zuwa makaranta da cigaba da karatu,” ya bayyana.
DUBAWA ta yi bitar rahoton, wanda aka wallafa shi cikin watan Yulin 2025.
An shirya wannan rahoton ne wa ma’aikatun ilimin jihohin Katsina, Zamfara da Neja tare da tallafin kudi daga UNICEF. Haka nan kuma ta wallafa rahoton tare da gargadin cewa UNICEF ce ta bayar da kudin gudanar da binciken, amma ra’ayoyi, fassara da mai dai dauk sauran abubuwan da aka bayyana cikin rahoton na marubutan ne kuma ba lallai ne su wakilci ra’ayi ko matsayar kungiyar ta UNICEF ko na ma’aikatar ilimin jihar ba.
Rahoton ya yi nazarin yadda rashin tsaro ya shafi ilimi a jihohin uku. Shiroro na daya daga cikin kananan hukumomi ukun da binciken ya yi la’akari da su, wadanda suka hada da Munya da Rafi.
Rahoton ya kuma yi bayani kan harkokin hakar ma’adinan da ake yi a jihar Neja bisa la’akari da yadda rikicin ke yin tasiri kan ilimi. Haka nan kuma ya ce gano ma’adinan karkashin kasa a yankunan musamman zinari ya kara janyo matsala a wasu al’ummomin kuma akwai hujjojin da ke nuna cewa lallai hakan ma’adinan ya yi sanadin da wasu iyayen suka janye yaransu daga makarantun wasu ma har sun canza wuraren zama.
Sai dai rahoton ba binciken da UNICEF ta yi musamman kan tasirin ayyukan hakar ma’adinai kan zuwa makarantan dalibai a jihar.
Mafi mahimmanci, DUBAWA ba ta sami wani bayani cikin rahoton da ke goyon bayan furucin gwamnan ba. Ko da shi ke a waje guda kuma, rahoton ya nuna cewa maza, duk da cewa tashin hankalin ya shafe su, sun fi fadawa hannun kungiyoyin ‘yan bindiga wadanda ke daukarsu a matsayin mambobi ko kuma shiga aikin bauta da zarar suka rasa matsugunnensu.
A Karshe
Da’awar gwamna Bago na cewa UNICEF ta ce ba za’a sami yara maza a azuzuwan farko na makarantun sakandaren da ke wasu yankunan jiharsa a shekara ta 2027 ba gaskiya ba ne.
Kungiyar UNICEF da kanta ta fadawa DUBAWA cewa ta taba gudanarwa ko kuma ma bayar da izinin gudanar da binciken kan tasirin hakar ma’adinai kan daliban da ke makarantun kanana hukumomin Shiroro da kewaye a jihar Neja ba.
