Zargi: Wani zargin da ake yadawa a WhatsApp na danganta cutar HIV da allurar rigakafin COVID-19 da ma ta cutar sankarau
Bincikenmu ya nuna mana cewa wannan zargin ba shi da tushe dan haka ba gaskiya ba ne
Cikakken bayani
Kwayar cuta mai karya garkuwar jiki wato HIV cuta ce da ke lalata duk wata kwayar halittar da ke kare jikin dan adam daga kamuwa daga cututtuka musamman kwayoyin jinin da aka fi sani da white blood cells a turance ko kuma CD4, wadanda su ne dama ke yaki da duk wata cutar da ta shiga jikin mutun a kowace gaba har sai ta tabbatar da cewa cutar ba ta nan kuma.
Ana iya samun kwyar cutar idan jinin wanda ke dauke da kwayar cutar ya hadu da na wanda ba shi da shi, ko kuma cikin maniya da ruwan da ke fita daga farjin na mace. Idan kuma ba’a kula da shi ba ya kan habaka ya kai fa AIDS ko kuma kanjamau.
Har yanzu kwayar cutar HIV abin fargaba ne domin ya zuwa yanzu, mutane fiye da milliyan 35 sun hallaka a dalilin cutar.
Kwanan nan wani sakon da aka yi ta yadawa a WhatsApp ya yi zargin cewa kafar yada labaran BBC ta ce kwayar cutar HIV na cikin maganin da ake allurar rigakafin COVID-19 da shi.
“BBC yanzu ta amince cewa akwai kwayar cutar HIV a cikin wadansu daga cikin magungunan da ake allurar rigakafin COVID-19,” kadan daga cikin sakon ya bayyana.
Sakon wanda ya ke dauke da wani adireshi na cewa wannan ne dalilin da ya sa ake samun rahotannin karuwar cutar HIV.
Wani hoto wanda shi ma ya yi yawo sosai ya na zargin wai jaridar The Times na zargin cewa Hukumar Lafiya ta Duniya WHO ta yi wa ‘yan Afirka fiye da miliyan 50 allurar rigakafin cutar sankarau a shekarar 1987 wadda ta janyo mu su HIV/AIDS.
Ganin yadda wannan labarin ya yadu sosai ya kuma dauki hankali ya sa DUBAWA ta ce za ta yi bincike ta tantance gaskiyar lamarin.
Tantancewa
Zargin Farko: Allurar rigakafin COVID-19 na dauke da kwayar cutar HIV
Adireshin da aka sanya a sakon WhatsApp din ya kai dubawa zuwa wani shafi mai suna praguetruth.cz wanda shi ma ya kasance ya yi irin wannan bayanin yana dangantawa da wani labarin da aka wallafa a wata kasidar Amurka dangane dakula da lafiya wadda aka fi sani da American Journal of Managed Care (AJMC) a shekarar 2020.
Da muka karanta labarin a AJMC mun gano cewa an gyara ainihin labarin wanda aka yi dangane da HIV da allurar rigakafin kwayar cutar Adeno ko kuma Adenovirus type-5 da ta COVID-19.
Wannan gyarar da aka yi ya nuna cewa duk alluran rigakafin daga aka bayar da izinin amfani da su ba su da wani lahani ga lafiyar dan adam kuma suna aiki yadda ya kamata.
Shafin tantance bayanai na Full Fact ma ya amince da hakan inda ya ce dama akwai allurar da aka so a yi tare da sinadarin protein din da aka samu da kwayar cutar HIV amma kuma ba’a yi amfani da shi ba.
Domin tantance ko lallai akwai wadanda aka ce sun kamu da HIV ta haka, DUBAWA ta yi amfani da mahimman kalmamomin da duk yadda aka yi za su bulla a ire-iren wadannan rahotannin amma ba ta ga wani labari dangane da cewa ma an sami karuwa a adadin wadanda ke kamuwa da cutar HIV ba.
A wani shafi mai suna hiv.gov wanda ke wallafa shawarwari a kan kari, dangane da manufofi, shirye-shirye da abubuwa masu amfani dangane da kwayar cutar HIV a Amurka, ya bayyana cewa a duniya baki daya, akalla mutane miliyan daya da rabi suka kamu da HIV a shekarar 2021. A cewarsu, bayan sun kwatanta wannan adadin da alkaluman da suka samu a shekarun baya sun kula cewa an samu raguwa a yawan mutanen da ke kamuwa da cutar a karon farko da kashi 32 cikin 100 tun daga shekarar 2010 sabanin zargin da aka yi da ke cewa aan sami karuwa.
Mun kuma sake gano cewa wannan zargin da ma wasu masu kama da shi, kamfanin dillancin labaran Reuters ta riga ta karyata su bayan da wani rahoton BBC ya bayyana yadda aka yi watsi da wata allurar rigakafi a kasar Ostraliya bayan da aka danganta ta da HIV.
Viral Facts Afirka, su ma masu tantance gaskiyar bayanai sun wallafa bidiyoiyn da suka karyata duk wani zargin da ke danganta HIV da allurar rigakafin COVID-19
Manajan sashen kula da bayanai kan kiwon lafiya na Afirka a Hukumar Lafiya ta Duniya (AIRA) Sergio Cecchini shi ma ya karyata zargin
“Zargin wai an gano kwayar cutar HIV a cikin allurar rigakafin COVID-19 karya ne. Akwai jita-jita da yawa dangane da wannan batun har ma da wadda ke zargin wai ana kamuwa da HIV daga allurar rigakafin ta COVID-19.
Zargi na Biyu: Allurar rigakafin Sankarau ta taba janyo yaduwar cuta mai karya garkuwar jiki wato AIDS
Bincikenmu ya nuna mana cewa babu wata dangatakar da ke tsakanin AIDS da allurar rigakafin cutar Sankarau. Mun gano cikakken binciken da shafin Full Fact ya yi mai karyata zargin baki daya.
Mr Sergion na hadakar Hukumar Lafiya ta Duniya ma ya ce wannan tsohon zargi ne kuma ba shi da gaskiya inda shi ma ya ja hankalinmu zuwa binciken da shafin Full Fact ya yi na karyata zargin.
“Wannan tsohon labari ne na cewa Hukumar Lafiya ta Duniya ta yi sanadiyar kamuwar butane miliyan 50 da cutar HIV kuma an karyata shi kamar yadda kuka gani a shafin Full Fact.
A Karshe
Binciken mu ya nuna mana cewa duk wadannan zarge-zargen ba su da tushe dan haka karairayi ne kawai.