African LanguagesHausaMainstream

Tsoffin hotuna ne ake amfani da su wajen kwatanta harin da aka kai jihar Filato

Da’awa: Ana danganta hotunan da ke nuna wasu maza suna dakon abun da ake kyautata zaton gawawwaki ne a kan babura da harin baya-bayan nan da aka kai a jihar Filaton Najeriya.

<strong>Tsoffin hotuna ne ake amfani da su wajen kwatanta harin da aka kai jihar Filato</strong>

Sakamakon binciken: Karya! Wadannan hotunan tsoffi ne kuma ba su yi mafari daga harin da aka kai wasu yankunan jihar Filato a watan Disemban 2023 ba.

Cikakken bayani

Ga mutanen da ke rayuwa a kananan hukumomin Bokkos, Barkin Ladi, da Mangu, a jihar Filato, bukin Kirisimeti ba zai mu su da farin ciki ba. A maimakon haka lokaci ne da suka wasu da kyar suka tsira da rayuwarsu garin tserewa daga maharan da suka afka musu.

Ranar jajibirin Kirisimeti, 24 ga watan Disemban 2024, ‘yan bindiga suka shiga al’ummomi 17 suka hallaka mutane akalla 195 suka kuma kona musu gidajensu.

Shugaba Bola Tinubu ya kwatanta harin a matsayin “jahilci da kuma abun tsoro” sa’annan ya yi alkawarin cewat “wadannan wakilan mutuwa da zalunci da makokoki za su fuskanci shari’a.”

Harin ya kuma sake tayar da damura dangane da matsalar rashin tsaron da ke cigaba da kalubalantar kasar.

Bayan harin, labarin karya da na yaudara suka fara bulla dangane da batun a soshiyal mediya, inda mutane suka fara yada bayanai daban-daban. Wannan ne ya sa masu binciken gaskiya suka yanke shawarar tantance bayanan kuma sun yi nasarar karyata wasu labaran kamar yadda aka gani a nan da nan

DUBAWA ta kuma sake gano wani batun mai kama da wannan. Inda wani mai amfani da shafin Facebook, ya wallafa hotunan wasu masu babura suna dauke gawawwaki cikin tabarma da sauran kayayyakin sa wa. Mai shafin sai ya ce wadannan mutanen wani kauye ni a birnin Jos. Har ila yau ya kuma sake zargin cewa haka ne aka yi bukin sabuwar shekara a yankin.

Sakamkaon kashe-kashen da aka yi a jihar Filato kuma ganin cewa Jos ne babban birnin jihar, batun ya dauke hankalin ‘yan Najeriya da dama wadanda suka zaci lallai hotunan na da alaka da harin a zahiri.

Shi ya sa DUBAWA ta gudanar da bincike dangane da batun. 

Tantancewa

DUBAWA ta yi amfani da manhajar da ke tantance asalin hotuna,  inda ta gano cewa biyu daga cikin hotunan ba su da alaka da harin na Disemban 2023.

Sakamakon binciken ya nuna cewa an fara wallafa hotunan ne ranar hudu ga watan Oktoban 2022, a shafin  Arewa Daily News da ke Facebook dan nuna wani harin da aka kai a wata al’ummar jihar Taraba.

Rahoton ya yi bayanin cewa wasu maharan da ba’a san ko su wane ne ba sun hallaka wadansu makiyaya 12 a Gundumar Zude Pangri da ke karamara hukumar Bali a jihar Taraba.

An yi labarin cewa maharan masu dauke da bindigogin AK47 sun shiga kauyen suka kira makiyayan a matsayin za su yi hira da su, amma kuma da suka isa wurin sai suka bude musu wuta. Daga nan ne 12 suka hallaka yayin da sauran suka nemi hanyar tserewa.

Wannan labarin tare da hotunan ya kuma bulla a wannan shafin da wannan da wannan. Wannan bidiyon da ke nuna yadda ake kai gawawwakin inda za’a rufe su a wani kauyen da ke kusa da wurin shi ma ya bayyana a wani shafin ranar biyar ga watan Oktoban 2022.

A Karshe

Hotunan da ake dangantawa da hare-haren da aka kai jihar Filato a watan Disemban 2023 daga 2022 aka dauko su ba 2023 ba.

Show More

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button
Translate »