Wasikun Tinubu zuwa ga MDD da Amurka domin boye takardun FBI na bogi ne

Shugaba Bola Ahmed Tinubu na Najeriya. Photo Source: X/Tinubu.
Getting your Trinity Audio player ready...

Da’awa: Masu amfani da kafafen sada zumunta sun yi ikirarin cewa Shugaba Tinubu ya aike da wasiku (duba nan da nan) zuwa ga Sakatare-Janar na Majalisar Dinkin Duniya da Shugaban Kasar Amurka, yana rokon kada a saki bayanan hukumar FBI da suka shafi zargin safarar miyagun kwayoyi da wasu batutuwa.

Wasikun Tinubu zuwa ga MDD da Amurka domin boye takardun FBI na bogi ne

Hukunci: Ƙarya ce. Binciken DUBAWA ya gano cewa wasikun na bogi ne. Binciken kimiyyar na’ura mai kwakwalwa da aka gudanar a kan wasikun tare da tuntuɓar Fadar Shugaban Najeriya sun nuna cewa takardun ba na gaskiya ba ne.

Cikakken Bayani

Babbar Kotun Amurka da ke Gundumar Columbia na ci gaba da shari’a kan neman ‘yancin samun bayanai (FOIA) da suka shafi bayanan hukumomin tsaron Amurka na karshen shekarun 1980 da farkon 1990 wadanda suka ambaci sunan Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu. Wani mai rajin fito da bayanai a Amurka, Aaron Greenspan, wanda ya kafa PlainSite, shi ne ya shigar da karar yana neman samun bayanan bincike daga Hukumar Binciken Manyan Laifuka ta Amurka (FBI) da Hukumar Yaki da Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi (DEA).

A daidai lokacin da jama’a ke bibiyar shari’ar da ake yi a kotu, masu amfani da kafafen sada zumunta sun fara yada hotunan wasiku da aka ce Shugaba Tinubu ne ya rubuta kuma ya sanya wa hannu.

Ikirarin ya ce shugaban na Najeriya ya rubuta wa Shugaban Kasar Amurka da Sakatare-Janar na Majalisar Dinkin Duniya, António Guterres, yana rokon a dakatar da sakin takardun da ake zargin sun danganta shi da binciken miyagun kwayoyi na baya da kuma mutuwar Moshood Abiola da Janar Sani Abacha.

Wani bangare na ɗaya daga cikin wasikun da aka wallafa a Facebook (wadda aka adana a nan) da ake ikirarin an aike wa Mista Guterres na cewa, “Idan aka yi la’akari da dangantaka mai karfi a da ke tsakanin Najeriya, Majalisar Dinkin Duniya da Amurka, cikin girmamawa nake rokonka, Mai Girma, da ka yi amfani da matsayinka wajen tattaunawa da Gwamnatin Amurka, musamman ma Shugaba Donald J. Trump, don ya duba yiwuwar shiga cikin wannan lamari tare da soke ko rufe wannan kara.”

Ya zuwa ranar Alhamis, 24 ga Satumba, 2026, rubutun ya samu mutane 362 da suka nuna alamar so ko ban mamaki, sharhi 75, da kuma sake yadawa sau 34.

Wata makamanciyar takarda ta bayyana a dandalin X (wadda aka adana a nan) da aka aike wa Shugaban Kasar Amurka, mai taken “The Release of My FBI Case Must Be Handled with Caution” (Dole ne a kula sosai wajen sakin batun shari’ata ta FBI), tana rokon hukumomin Amurka da su nuna tawali’u su kuma boye takardun.

Masu amfani da wadannan kafafen da dama sun dauki wasikun a matsayin na gaskiya.

Farouk-Jibrin Okpanachi ya rubuta, “Taken wasikar ya bayyana komai. Ya amsa cewa ana yi masa shari’ar kwaya a Chicago.” 

Wani mai amfani da kafar kuma, Jezreel Abu, ya ce, “Je ka roke su ido-da-ido; taron UNGA na ci gaba da gudana.” 

Sai dai wani mai suna jamesagada (@jamesagada) ya bayyana cewa, “Wannan wasika a fili take ta bogi ce.”

An sake yada wasikun a shafukan sada zumunta daban-daban a nan, nan, nan, da kuma nan.

Ganin cewa wannan ikirari ya shafi huldar diflomasiyya ta kasa da kasa, manyan shari’u a kotu, da kuma manyan shugabannin kasa, DUBAWA ta tantance gaskiyar lamarin.

Tantancewa

DUBAWA ta gudanar da bincike ta amfani da muhimman kalmomi a shafin Google, shafukan intanet na Fadar Shugaban Najeriya, da kuma shafukan labarai na gidajen yada labarai na kasa. Binciken bai samu wata kafar yada labarai mai inganci a cikin gida Najeriya ko a kasashen ketare da ta ruwaito cewa Shugaba Tinubu ya aike da irin wadannan wasiku zuwa ga Gwamnatin Amurka ko Majalisar Dinkin Duniya ba.

Binciken da DUBAWA ta yi a kan wasikun ya nuna cewa sun saba wa ka’idojin rubuta takardun gwamnati ta fuskoki daban-daban. 

Takardun suna dauke da tambarin da bai dace da na gwamnati ba, inda aka hada hoton fuskar Shugaba Tinubu, tambarin rigar makamai ta kasa, da kuma manyan bakake, maimakon ainihin takardar da Fadar Shugaban Kasa ke amfani da ita.

Bayan haka, sa hannun da ke jikin wasikun bai yi daidai da sa hannun da Shugaba Tinubu ya saba yi a takardunsa na aiki da sakonnin gwamnati ba.

Wasikun Tinubu zuwa ga MDD da Amurka domin boye takardun FBI na bogi ne

Photo collage of viral letters and official letter of President Tinubu

Haka kuma, sakin takardu a karkashin dokar FOIA ta Amurka ya ta’allaka ne a kan dokokin tarayya da kuma hukuncin alkalai a shari’un kotu. Lauyoyin Shugaba Tinubu da ke Amurka sun gabatar da hujjojinsu na neman kariya a karkashin sashe na 7(C) na dokar FOIA a rubuce kai tsaye ga kotu, ba ta hanyar rubuta wasiku ga shugabannin kasashen waje ba.

DUBAWA ta binciki hotunan wasikun guda biyu ta hanyar amfani da manhajar VeraAI da ke cikin InVID-WeVerify wadda ke gano hotunan da na’ura mai kwakwalwa ta kirkira.

Manhajar ta fitar da hujjoji masu karfi da ke nuna cewa wasikar da aka ce an aike wa Sakatare-Janar na Majalisar Dinkin Duniya ta bogi ce, wato an kirkire ta ne ta hanyar amfani da fasahar AI.

Wasikun Tinubu zuwa ga MDD da Amurka domin boye takardun FBI na bogi ne

Ma’aunin bincike na VeraAI

Ga wasikar da aka aike wa Shugaban Kasar Amurka kuma, VeraAI ta ba da sakamakon da bai kammala ba, inda ta ga alamu marasa karfi na kirkirar AI. 

Sai dai kuma, lokacin da aka duba takardar a kafar isFake.ai, wadda ke binciken hotuna da rubuce-rubucen AI, binciken ya nuna cewa mai yiwuwa wasikar da aka ce an aike wa Shugaban Amurka na’urar AI ce ta hada ta, musamman ganin yadda rubutun yake.

Wasikun Tinubu zuwa ga MDD da Amurka domin boye takardun FBI na bogi ne

Sakamakon IsfakeAI 

DUBAWA also contacted the Senior Special Assistant to the President on Media and Public Enlightenment, Abdulaziz Abdulaziz, who dismissed the letters.

DUBAWA ta tuntubi Babban Mataimaki na Musamman ga Shugaban Kasa kan Kafafen Yada Labarai da Fadakarwa, Abdulaziz Abdulaziz, wanda ya karyata wasikun.

“Wadannan na bogi ne; abu na farko da ba daidai ba shi ne tambarin kan takardar,” in ji shi, yayin da yake kiran jama’a da su yi watsi da su.

A Ƙarshe

Ikirarin da ke cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya rubuta wasiku zuwa ga Sakatare-Janar na Majalisar Dinkin Duniya da Shugaban Kasar Amurka yana rokon kada a saki takardun FBI kariya ce.