|
Getting your Trinity Audio player ready...
|
Cikakken Bayani
A watan Yunin 2026, wani gajeren bidiyo ya nuna wani jami’in ‘dan sanda sanye da kakin aiki yana daga hannu don gaisawa da wasu mutane a kan babura dauke da makamai yayin da suke wucewa.
Rundunar ‘Yan Sandan Najeriya ta yi gaggawar fayyace cewa an dauki bidiyon ne a kan hanyar da ta hada kananan hukumomin Musawa da Matazu a Jihar Katsina.
A wata sanarwa da rundunar ta wallafa a shafinta na Facebook, ta bayyana cewa mahayan dauke da makamai ba ‘yan bindiga ba ne, mambobin kungiyar ‘yan sintiri ne ta Vigilante Group of Nigeria (VGN) da maharba da ke halartar wani samamen hadin gwiwa na jami’an tsaro.
Sai dai wannan bayani ya fuskanci shakku sosai daga jama’a.
Dubban masu sharhi a yanar gizo (a nan, nan, nan, da nan) sun yi watsi da bayanin, tare da nuna kokonto a kan bayanin ‘yan sandan.
Wannan rashin yarda ba haka kawai ya faru ba. Sabanin da aka shafe shekaru ana samu tsakanin kalaman hukumomi da shaidun da ke biyo baya ne suka haifar da hakan.
Matsalar rashin yarda ta faɗaɗa
Shakkun da al’umma ke yi wa hukumomin gwamnati ya bayyana a cikin bayanan kididdigar kasa baki daya.
Binciken Hadin Kan Al’umma na Najeriya na 2026 da Cibiyar Binciken Ra’ayoyin Jama’a ta Africa Polling Institute (API) ta gudanar ya nuna cewa kashi 72% na ‘yan Najeriya sun bayyana rashin yarda ko karancin yarda da gwamnati, wanda ya ragu daga kashi 83% a shekarar 2025.
Haka zalika rashin amincewar ya bayyana a sauran muhimman hukumomi. Kashi 77% sun nuna karancin yarda ko rashin yarda da Majalisar Dokoki ta Kasa, yayin da kashi 73% suka bayyana karancin yarda ko rashin yarda da bangaren shari’a. Idan aka kwatanta, kashi 49% sun nuna karancin yarda ko rashin yarda da shugabannin addini yayin da kashi 55% suka bayyana karancin yarda ko rashin yarda da shugabannin gargajiya.
Wadannan alkaluma sun fayyace manyan dalilan da suka sa kalaman hukumomi ke fuskantar tirjiya cikin gaggawa a yanar gizo.
Ga hukumomin tsaro, hakan zai iya yin illa sosai. Idan al’umma suka cire tsammani, bayanan hukuma, gargadi, karin haske da kiran hadin kai, duk za a iya yin watsi da su a matsayin labaran karya.
Abubuwan da ba za a manta da su ba
Wani abu da ya faru a Jihar Kaduna watanni biyar kacal a baya, na ƙara bayyana inda shakkun al’umma ya samo asali.
A ranar Lahadi, 18 ga Janairu, 2026, ‘yan bindiga suka kai hari a wasu coci-coci guda uku a Kurmin Wali, Karamar Hukumar Kajuru, inda suka sace Kiristoci 177 a lokacin ibadar safiya.
Yayin da mutanen gari suka bayyana tashin hankali da suke ciki, Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Kaduna da jami’an karamar hukumar sun musanta lamarin, tare da cewa rahotannin jita-jita ce kawai da ba ta da tushe da aka kirkira don sanya tsoro.
Gaskiya ta fara fitowa fili cikin ‘yan kwanaki, yayin da shugabannin coci da kungiyar Kiristocin Najeriya (CAN) suka fitar da jerin sunayen da ke dauke da sunaye da iyalan waɗanda aka sace.
A cewar wani rahoto na kafar yada labarai ta BBC, sai a lokacin ne jami’an tsaro suka dauki matakin fara neman mutanen da aka sace. Aikin ya ci gaba da gudana na makonni, inda a tsawon lokacin wasu daga cikin wadanda aka sace suka tsere yayin da aka sako sauran daga baya.
Wannan dabi’a ta musanta zarge-zarge masu tsanani kafin daga baya a amince da su tana faruwa har a bangaren soji.
Lokacin da rahotanni suka nuna cewa an soke fareti na bikin cika shekaru 65 da samun ‘yancin kan Najeriya saboda zargin wani yunkurin juyin mulki a kan gwamnatin Shugaba Bola Tinubu, kakakin tsaro ya fito ya yi watsi da rahotannin a matsayin kagaggen labari mai cike da mugunta, kamar yadda Daily Post ta ruwaito.
Duk da haka a cikin ‘yan watanni, hukumomi sun kaddamar da kotun soji a hukumance a Abuja don gurfanar da gwamman hafsoshin da ke da hannu a ciki.
Wani sabani makamancin haka ya sake bayyana a watan Disamba na 2018, lokacin da wani bincike da jaridar Premium Times ta gudanar ya bayyana cewa jami’an ‘yan sandan kwantar da tarzoma (MOPOL) 167 sun gudu daga sansanin horar da yaki da ‘yan ta’adda da ke Buni Yadi, Jihar Yobe, don gujewa tura su fagen daga domin yaki da Boko Haram.
Hedikwatar rundunar ta yi watsi da rahoton a matsayin na bogi tare da zargin kafar yada labaran da yunkurin karya kwarin gwiwar dakarun.
Sai dai kuma, wannan martanin bai wuce sa’o’i 24 ba. Kwamandoji a Rundunar Sojin Kasa ta Najeriya suka tsare da dama daga cikin ‘yan sandan da ke gudu a Damaturu, kamar yadda Premium Times ta ruwaito.
Ga al’umma, irin wadannan abubuwa suna haifar da matsalar rashin yadda da ke faruwa saboda yawaitar faruwar abin. Da zarar hujja ta bayyana kuma ta saba wa bayanin da hukuma ta bayar, gaba daga kalaman wannan hukuma za a riƙa kallonsu da shakku, ko da kuwa na gaskiya ne.
#EndSARS da Chibok
Bayan harbe-harben da aka yi a watan Oktoban 2020 a lokacin zanga-zangar #EndSARS a Lekki da ke Legas, Rundunar Sojin Najeriya ta musanta cewa dakarunta na wurin, yayin da ta yi watsi da labarai da rahotannin faruwar lamarin a matsayin “labaran karya.”
Sai dai bincike da dama sun kalubalanci wannan bayani.
Binciken da Amnesty International Nigeria da kafar yaɗa labarai ta CNN suka yi sun binciki faifan bidiyo, fankon harsasai da shaidar inda lamarin ya faru da ke da alaka da sojoji.
A yayin zaman Kwamitin Bincike na Jihar Legas, sojoji sun riƙa sauya bayanan abubuwan da suka faru, daga musanta cewa sojoji na wurin, zuwa amincewa da tura su amma suka karyata amfani da alburusai masu kisa, sai kuma a karshe suka amince cewa an je da harsasai masu rai zuwa wurin zanga-zangar.
Irin wannan matsala ta samo asali tun ma kafin wannan lokaci.
A watan Afrilun 2014, kwanaki kadan bayan da Boko Haram suka sace dalibai mata daga Makarantar Sakandaren ‘Yan Mata ta Gwamnati da ke Chibok, Hedikwatar Tsaro ta fitar da wata sanarwa tana mai ikirarin cewa sojoji sun ceto kusan dukkan ‘yan matan da aka sace, inda guda takwas kacal suka rage a hannun ‘yan bindigar.
Sai dai shugabar makarantar, iyaye, da jami’an yankin sun kalubalanci ikirarin, lamarin da ya tilasta wa sojoji janye sanarwar tare da amincewa da cewa har yanzu ‘yan matan ba a gano su ba, kamar yadda Premium Times ta ruwaito.
Wadannan abubuwan duk sun taimaka wajen bayyana dalilin da ya sa al’umma za su iya kin amincewa da bayanan hukumomi ko da a ce bayanan gaskiya ne.
Ra’ayin masana
Kabir Lawanti, masanin harkokin sadarwa kuma babban malami a Sashen Nazarin Aikin Jarida a Jami’ar Ahmadu Bello (ABU), Zariya, ya bayyana cewa a duk lokacin da aka tabbatar da abu bayan hukuma ta musanta, barnar da hakan ke yi wa hukumar ta zarce ainihin abin da ya faru kansa.
“Yana haifar da abin da masana sadarwa ke kira karancin yarda, kuma jama’a na iya fara tambayar me kuma jami’an suka taba fada mana wanda ba gaskiya ba ne,” in ji shi.
Masu magana da yawun jami’an tsaro sukan danganta rashin son bayar da bayani ko musanta faruwar lamai da kare tsaron kasa. Sai dai kuma, Kabir Lawanti ya bayar da hujjar cewa faɗin gaskiya ba ya nufin tona asirin sunayen masu ba da bayanan sirri, zirga-zirgar dakarun soji, hanyoyin samun bayanan sirri ko dabarun yaƙi.
Yayin da yake nanata wannan bayanin, Caleb Ijioma, Babban Darakta na kafar tantance gaskiyar labarai ta Roundcheck, ya nuna cewa rugujewar amincin jama’a ba wai kawai kalamai marasa inganci na hukumomi ke haifar da shi ba, har ma da rashin kyakkyawar alaka tsakanin hukumomi da jama’a.
Ya jaddada cewa kare dabarun aiki ya bambanta matuka da boye bayanan da ya kamata a yi bayani a kansu don al’umma su sani
“Na yarda cewa a lokacin da ake gudanar da aiki, ba za ka iya bayyana dukkan cikakkun bayanai ba, amma jama’a suna bukatar a yi musu bayani na gaskiya. Me ya sa aka kama wadanda ake zargi? Ta yaya mutane suka mutu a tsare? Wane ne ya yi harbin? Dole ne hukumomi su rika fadin gaskiya kan muhimman abubuwan da suka faru.”
Masanan sun ba da shawarar cewa ya kamata hukumomin tsaro su sauya daga dabarun kare kansu a lokacin rikici su kuma rungumi tsarin dogara da hujjoji ta hanyar ba da fifiko ga faɗin gaskiyar lamari a kan yaudara, tare da bayyana cewa ana kan tantance labari a lokacin da ya dace maimakon yin gaggawar musantawa kai tsaye wadda daga baya za ta iya kasancewa ba haka ba.
