Karya ce! Sarkin Musulmi bai goyi bayan raba Najeriya ba

Sultan of Sokoto
Sarkin Musulmi, Sa'ad Abubakar. Hoto: The Guardian.
Getting your Trinity Audio player ready...

Da’awa: Wani mai amfani da Facebook ya yi ikirarin cewa Sarkin Musulmi, Muhammadu Sa’ad Abubakar, ya ce Arewacin Najeriya ba ya tsoron rarrabuwar Najeriya, kuma idan Kundin Tsarin Mulkin Najeriya ya ba da dama, to a bar ‘yan kabilar Ibo su tafi.

Karya ce! Sarkin Musulmi bai goyi bayan raba Najeriya ba

Hukunci: Karya ce. DUBAWA ba ta samu wata shaida da ke nuna cewa Sarkin Musulmi ya yi wannan furuci ba, kuma jami’in yada labarai na fadarsa ya karyata ikirarin.

Cikakken Bayani

Wani mai amfani da Facebook, mai suna @CALID VOICE ECO, a ranar 7 ga Yuni, 2026, ya yi zargi a cikin wani bidiyo (wanda aka ajiye a nan) cewa Sarkin Musulmi, Muhammadu Sa’ad Abubakar, ya ce Arewa ba ta tsoron raba Najeriya.

Rubutun da aka dora a kan bidiyon na cewa, “ba ma tsoron rarrabuwar Najeriya. Idan Kundin Tsarin Mulkin Najeriya ya amince da hakan, a bar ‘yan Ibo su tafi.”

Bayanin bidiyon a dandalin na Facebook da yaren Pidgin ya ce: “If unah no da fëær make unah release Nnamdi Kanu”, ma’ana “Idan har Arewa ba ta tsoron wani abu, to ku saki Nnamdi Kanu.”

Ya zuwa ranar 15 ga Agusta, 2026, bidiyon ya samu mutane 996,000 da suka kalla, 16,000 da suka nuna sha’awa, sharhi 709, da kuma mutum 1,400 da suka sake yada.

Wasu amfani da Facebook sun bayyana goyon baya da kuma nuna kokonto game da rubutun a sashen sharhi. 

Wani mai amfani da kafar, Akudinawa Edorji, ya rubuta cewa, “kada ku damu da wannan” yana nufin Sarkin Musulmi. Wata mai suna Akinsanya Deborah kuma ta rubuta, “Ibo da Yarbawa tafiya za su yi, dole ne Najeriya ta rabu don zaman lafiya ya wanzu, don Allah. Idan ba ku jin tsoro, to a sake Inamdi Kanu yanzu.”

Wani mai amfani da kafar, Iheanacho Lucas, wanda shi ma ya goyi bayan mai ikirarin, ya rubuta, “me ya sa kuke tsoron barin ‘yan Ibo su tafi? Gara ku sunkuyar da kai don kada su tafi.” Wani mai amfani da kafar, Zakari Aliu, ya bayyana cewa, “kiyayyarka da zage-zagenka sun yi yawa. Don Allah ka kiyaye don a samu zaman lafiya!…”

Tasirin da wannan magana ke da shi a kan yanayin siyasa da kabilancin Najeriya da kuma babban matsayin mutumin da aka danganta kalaman da shi ya sa DUBAWA ta tantance gaskiyar lamarin.

Tantancewa

DUBAWA ta gudanar da bincike mai zurfi a shafin Google game da wannan magana da aka jingina wa Sarkin Musulmi, amma ba ta samu wata hujja mai karfafa hakan ba.

Kalaman Sarkin Musulmi na baya-bayan nan da kafafen yada labarai suka wallafa sun mayar da hankali ne a kan daina cin mutuncin addinai tare da yin kira ga zaman lafiya.

“Ya kamata Kiristoci su daina zagin Musulmi, su kuma Musulmi su daina zagin Kiristoci, domin hakan na da muhimmanci ga zaman lafiya tare. Ya kuma jaddada cewa Kiristoci da Musulmi daidai suke a gaban Allah”, in ji shi.

A ranar 18 ga Agusta, 2026, a wani taron karawa juna sani da aka shirya wa ‘yan jarida, Sarkin Musulmi ya yi kira da a ci gaba da kokarin tabbatar da zaman lafiya a Najeriya.

Haka zalika, mun gano wani rahoto na ranar 8 ga Agusta, 2026, da jaridar The Cable ta wallafa, inda Sarkin Musulmi ya yi tir da kisan wani jami’in sojan Najeriya dan kabilar Ibo.

Wani bangare na rahoton ya bayyana cewa Sarkin ya nuna rashin amincewarsa da kiyayya da nuna wariya da ake yi wa ‘yan tsirarun Musulmi ‘yan kabilar Ibo a yankin Kudu maso Gabas, tare da yin kira ga Gwamnatin Tarayya da rundunar soji da su gudanar da bincike. 

Sanarwar, wacce Bashir Adefaka, mataimaki na musamman ga Sarkin Musulmi kan harkokin yada labarai ya fitar, ta kara da cewa “rashin binciken kisan duk wani dan Najeriya” zai zama babbar koma-baya ga ginin kasa.

DUBAWA ta kuma tuntubi Sarkin Musulmi ta hanyar jami’in yada labarai na fadarsa, Aminu Haliru, wanda ya yi watsi da wannan ikirari tare da bayyana cewa karya ne.

Haliru ya ce, “wannan ba gaskiya ba ne. Mai Alfarma ba zai taba yin irin wannan magana ba.” 

Ya bayyana Sarkin Musulmi a matsayin mai gina kasa kuma mai fafutukar tabbatar da zaman lafiya da hadin kan al’umma a tsakanin ‘yan Najeriya, ba tare da la’akari da kabilarsu, addininsu, matsayinsu na rayuwa, yankinsu, ko jam’iyyun siyasa ba.

A Karshe

Ikirarin da ke cewa Sarkin Musulmi ya ce Arewacin Najeriya ba ya tsoron raba Najeriya Karya ce. Ba mu samu wata shaida da ke nuna cewa ya fadi hakan a yanar gizo ba, kuma jami’in yada labarai na fadarsa ya karyata ikirarin.