Getting your Trinity Audio player ready...
|
Da’awa: Rabi’u Kwankwaso na NNPP ya yi ganawar sirri da jigon APC Wamakko kan komawa jam’iyyar.

Hukunci: Yaudara ce. Bincike Dubawa ya gano cewa Wamakko bai gana da Kwankwaso ba, tsohon hoto ne da aka yi 2020 ake yadawa.
Cikakken Bayani
Ana ci gaba da rade-radin sauya shekar madugun siyasar Kwankwasiya kuma tsohon dan takarar shugaban kasa karkashin jam’iyyar NNPP a zaben 2023, Rabi’u Musa Kwankwaso, zuwa jam’iyyar APC mai mulkin Najeriya, lamarin da jam’iyyar APC ta ce abin farin ciki ne.
Sai dai bangaren NNPP sun bayyana cewa jigon nasu, kuma tsohon gwamnan jihar Kano bai da nufin zuwa jam’iyyar ta APC, kamar yadda shugaban jam’iyyar na jiha Hashimu Dungurawa ya bayyana.
Duk da haka wasu rahotanni na cewa ana ci gaba da tattaunawa ta karkashin kasa domin komawar Kwankwaso zuwa jam’iyyar ta APC.
Ana wannan sai wani labarin ya karade shafukan sada zumunta cewa, Sanata Aliyu Wamakko kuma makusancin Shugaba Bola Tinubu ya yi wata ganawar sirri da Kwankwano da kuma wanda ya yi wa Peter Obi takarar mataimakin shugaban kasa karkashin jam’iyyar LP Yusuf Datti Baba-Ahmed.
Wani shafin Facebook na NNPP Kwankwasiyya ya yi da’awar cewa wannan ganawar an yi ta ne a gidan Sanata Wamakko dake Asokoro a Abuja.
Zuwa ranar 25 ga watan Afrilun 2025, sama da mutum 50 ne suka yi sharhi akan labarin, inda mutum 56 suka yada shi.
Daga cikin masu sharhin, wani Auwalu Sabiu Nafada ya ce “neman kamun kafa yaje” amma Mohammed Hamza cewa ya yi “wannan fa tsohon hotone tun ana covid”.
Rudanin da mutane suka shiga akan wannan labarin ne ya sa DUBAWA yi bincike domin tabbatar da sahihancinsa.
Tantancewa
DUBAWA ta saka hoton a shafin neman hotuna na Google domin gano asalin wannan hoton da ake yada wa.
Mun gano cewa hoton an fara wallafa shi ne a ranar Talata 15 ga watan Satumban 2020, a shafin Facebook na Rabi’u Musa Kwankwaso.
Kwankwaso wanda ke tare da Yusuf Datti da Wamakko a cikin hoton, ya wallafa cewa ya kai “ziyarar ta’aziyya zuwa ga iyalan Sanata Aliyu Magatakarda Wamakko bisa rasuwar diyarsu, Sadiya Wamakko”.
Shima Sanata Wamakko ya wallafa wani hoton a shafinsa na Facebook wannan ranar, inda yake sanar da cewa ya karbi bakuncin Kwankwaso wanda ya zo domin yi masa ta’aziyya.
Hakam mun tuntubi mataimaki na musamman ga Sanata Wamakko akan yada labarai, Bashar Abubakar ya shaida min cewa labarin ganawar sirri tsakanin jagororin ba gaskiya ba ne.
“Lalle ba gaskiya ne ba. Mun gode” in ji
A Karshe
Yaudara ce, Kwankwaso bai ganawar sirri da Wamakko ba a kwanan nan.