African LanguagesHausa

Abubuwan da ya kamata a sani kan barkewar cutar kwalera a Najeriya kwanan nan

Getting your Trinity Audio player ready...

Cikakken bayani 

A cewar Hukumar Lafiya ta Duniya, WHO, Kwalera cuta ce da ke kawo gudawa bayan an ci abinci ko ruwan da ke dauke da kwayar cutar da ke haddasa ta, wadda ake kira bacterium Vibrio cholerae. Cholera na cigaba da kasancewa babban barazana ga lafiyat al’umma kuma alama ce ta rashin daidaito tsakanin mutane da kuma rashin cigaba a yanayin zamantakewa.

Gwamnatin jihar Lagos ta yi kira da a kara tsaurara matakan kariya daga kamuwa da cutar kwalera bayan da aka sami rahotannin mace-mace daga barkewar cutar a wasu yankunan kasar. A cikin  sanarwar, kwamishinan lafiya na jihar Akin Abayomi ya yi bayani kamar haka:

“Ya ce mun kaddamar da shirin da ke sanya ido a yankunan jihar, tare da mataikin gidanar da bincike kan ruwan sha dan gano inda gurbataccen ruwa ya fito a yankunan Lekki, Victoria Island. Muna tunanin mai yiwuwa za’a sami barkewar cutar, amma an riga an dauki kadan daga cikin wuraren da ake samun ruwan sha a jihar duk an kai su gwaki. Ya zuwa 28 ga watan Afrilun 2024, Najeriya ta yi rahoton cewa mutane 815 ake kyautata zaton suna dauke da cutar, yayin da 14 suka riga suka rasa rayukansu a jihohi 25.

Kwalara na iya janyo zawo, kuma idan har aka bar cutar ba magani, tana iya kai wa ga hallaka. Hadarin barkewar annobar kwalera ya fi kamari ne a yakunan da ke fama da talauci, a lokutan yaki ko kuma idan bala’i ya tilastawa mutane zama a wuri daya ba tare da cikakken tsabta ba.

Ana iya samun kwalera a ciki da waje. Kwalarar da ce ciki shi ne wanda aka gano cewa cutar na wurin na tsawon shekaru ukun da suka gabata, tare da hujjojin da ke nuna yaduwarta (ke nan a wurin cutar ke yawo ba wai wani ya shigo da shi ba ne). Barkewar cutar kwalera kuma na iya faruwa a kasashen da suka saba fama da ita da ma kasashen da ba safai ake ganin cutar ba.

Abubuwan da ke haifar da Kwalara

Wata kwayar cutar bakteriya da ake kira Vibrio cholerae ce ke haifar da cutar Kwalara. Cutar ta kan yi kamari ne idan har wannan kwayar cutar ta bakteriya ta sake wani abu mai kama da guba a cikin hanjin dan adam. Wannan gubar ce ke sanya mutun ya yi ta katsa har ya zubar da duk ruwan da ke jikin shi, da gishiri da ma sauran sinadaran da jikin dan adam ke bukata domin ya yi aiki yadda ya kamata.

Ba lallai ne kwayar cutar ta sa duk wadanda suka yi ma’amala da ita ciwo ba, amma suna iya fitar da shi a bayan gida ko da bai musu lahani ba, kuma idan har bayan gidan ya hadu da abinci ko ruwa, wani na iya dauka daga wurin. Gurbataccen ruwa ne ainihin inda ake samun kwayar cutar. Ana iya samun kwayar cutar a saman wurare, a ruwan rijiya, a kifi, a kayan lambu ko ‘ya’yan itace har ma da hatsi.

Abubuwan da ke da hadari

Kwalera ba za ta iya rayuwa a wajen da ke da gafi ba, ko a cikin cikin mutun ma idan har akwai irin sinadaran da ke da gafi ba za ta dade ba. To sai dai akwai mutanen da ba su da wannan sinadarin a cikinsu, kamar kananan yara da tsoffafi, da ma mutanen da ke shan magungunan da ke hana wannan sinadarin fitowa a cikinsu, dan haka irin wadannan mutanen za su fuskanci hadarin kamuwa da cutar.

Wanda ke zama tare da wanda ke dauke da cutar ma zai fuskanci hadarin kamuwa da ita. Kwalara ta fi yaduwa ne a wuraren da zai yi wuya su kasance cikin tsabta ko kuma ma dai a sami tsabtataccen ruwan sha. A na yawan samun irin wannan yanayin a sansanonin ‘yan gudun hijira, kasashen da ke fama da taluaci, yankunan da ake fama da yunwa, ko yaki ko kuma bala’i.

Alamu

A cewar shafin Mayo Clinic, yawancin wadanda sukan kamu da kwayar cutar kwalara (Vibrio cholerae) ba su ma sanin yadda aka yi suka kamu da cutar. To sai dai kwayar cutar kan tsaya cikin bayan gidan da za su rika yi na tsawon akalla kwanaki 14, suna iya yada cutar cikin ruwa ko abinci.

Wasu daga cikin alamun sun hada da gudawa, laulayi, amai, da kishin ruwa. Wasu karin alamun kuma sun hada da gajiya, fadawar idanu, bushewar baki, matsanancin kishi, bushewar fatar jiki wanda idan aka tsungula aka rike ya kan dauki lokaci kafin ya koma yadda ya kamata, sa’anan kuma da kyar mutun ke fitsari, zuciya bai bugawa yadda ya kamata, sa’anna jini zai sauka.

Gudawar da ke da alaka da kwalara ta kan zo ne kawai cikin sauri kuma ya kan sa mutun rasa ruwan da ke jikin shi da saura, kimanin lita daya cikin sa’a daya. A dalilin kwalara sai mutun ya yi fari kamar ruwan da aka wanke shinkafa.

Kariya

Hanyoyi da ya yawa ne ake amfani da su wajen shawo kan kwalara da rage hadarin mutuwa. Sa ido. Tsabtataccen ruwan sha, tsabta, da fadakarwa da shan magani da allurar rigakafi duk hanyoyi ne da za’a iya dauka dan kaucewa daga cutar.

Ku wanke hannuwa a kai- akai da sabulu da ruwa, musamman bayan an yi amfani da bayi sa’annan kyma kafin a taba abinci. A sa sabula a goga hannaye biyun a tare na tsawon dakiku akalla 15 kafin a dauraye. Idan har babu ruwa da sabulu, ana iya amfani da sinadarin goge hannun nan wanda ke dauke da giya.

Ana iya amfani da ruwan cikin kwalba ko kuma wanda aka dafa a gida dan ya kashe cututtuka. Ana iya ma amfani da ruwan cikin roba a wanke hakora.

Shayi ko lemun kwalba da na gwangwani yawanci ana iya amfani da shi, amma a tabbatar an goge jikin kafin a bude. Ka da a sa kankara a cikin ruwan ko lemu sai dai idan mutun ne da kansa ya yi kankarar dan haka ya tabbatar da tsabtar ruwan da ya yi amfani da shi.

Idan har zai yiwu a ci abincin da aka dafa da kyau, abinci mai zafi, a kuma guji cin abincin da ake saidawa a kan titi. Idan har ka siya abinci daga wajen wani a kan titi, ku tabbatar cewa an karbi abincin da zafin shi.

Magani

Kwalara cuta ce da za’a iya warkarwa. Yawancin mutane suna iya samun waraka da zarar suka sha ruwan gishiri da sukari. Wanda ake kira ORS.

Marasa lafiyan da suka rasa ruwa sosai a jikinsu na iya suma dan haka suna bukatar a yi mu su karin ruwa. Irin wadannan kuma dole a basu magani dan ya rage illar gudawar, ya rage tsawon lokacin da za su dauka suna rasa ruwa a jinkinsu da ma yawan lokacin da kwayar cutar zai dauka kafin ya gama fita daga cikin wanda ke dauke da kwayar cutar.

Duk wanda ya kamu da cutar ya yi kokari ya ga likita da zarar ya fara ganin irin wadannan alamun saboda a ganio ko mene ne a kuma bayar da maganin da ya fi dacewa.

Kwamishinan lafiya na jihar Legas shi ma ya shawarci al’ummar Legas da su nemi karin bayani daga ma’aikatar lafiyar, da cibiyar kula da yaduwar magunguna da sauran cibiyoyin lafiya masu nagarta dan samun bayanai masu sahihanci dangane da kariya, magani da kulawa.

Ra’ayin kwararre

Mun kuma yi magana da Subulade Owo, wani jami’in lafiya wanda ke da kwarewa a matakin kariya da na shawo kan yaduwar cututtuka. Ya yi mana bayanin cewa Kwalara kwayar cuta ce da ake samu a bayan gidan wadanda ke dauke da citar. Wadansu watakila suna dauke da cutar amma ba za su sani ba tunda jikinsu ba zai nuna alamun ba, wadansu kuma alamun ba za su bayyana sosai ba, a yayin da wasu kuma alamun za su bayyana da tsanani.

Kwalarar ta kan yadu ne a wuraren da basu da tsabta, da unguwanni masu cunkoso. Ya kuma ce yawanci kwalara na da alaka da rashin tsabtataccen ruwan sha da unguwannin talakawa.

Mr Owo wanda ya ce gwamnati da al’umma duk suna da hannu wajen daukar matakan kariya. Ya ce ya kamata gwamnati na da tsarin lura da gidaje da unguwanni mai kyau. Ya kamata suna sanya ido a kan yadda ake zubar da shara dan tabbatar kowa na mutunta dokokin yin hakan.

Ga al’umma ya jaddada bukatar tsabta “unguwannin da ke fama da cunkoso su tabbatar sun girka kwamitoci wadanda za su rika lura da tsabtar unguwanninsu su tabbatar an tsabtace ko’ina an kuma haramta bayan gida a waje, ya bayyana.

Daga karshe ya bayyana cewa mutanen da ke dauke da alamu kada su zauna a gida kawai su rika ba kansu magunguna, su je asibiti a duba su dan a basu magungunan da suke bukat, sa’annan allurar rigakafi na iya taimakawa wajen dakatar da yaduwar cutar

Wata ma’aikaciyar lafiyar, Kedei Ibang, ta bayyana cewa kwalara cuta ce da ke da saurin yaduwa kuma ya kan fi yin lahani ne a hanjin mutun ya kuma janyo amai da gudawa.

Ita ma ta jaddada mahimmancin kariya da kuma karbar magunguna a kan kari

“Idan kun yarda ku je asibiti da zarar kuka lura da cewa kun kama cutar kwalara. Ana iya maganin shi da ruwan gishiri da sukari dan mayar da ruwan jikin da mutan ya rasa. Ana kuma iya bayar da magani dan rage illar kwayar cutar, kuma da shan magani a gida gara zuwa asibiti a duba,” ta bayyana

A Karshe

Kwalera cuta ce da ake iya kare kai daga kamuwa da ita, ana kuma ita maganinta. Ta tabbatar da tsabta da tsabtace abinci da ruwan sha, da kuma zuwa asibiti da zarar aka ga alamu ana iya kare yaduwar cutar a kuma kiyaye al’umma baki daya.

Show More

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button