African LanguagesArticleFeaturedHausa

Ana Zazzaɓi a Ƙasashen Turai Kuwa?

Getting your Trinity Audio player ready...

A ƙasashen Turai, ana zazzaɓi, amma ba irin zazzaɓin da muke fama da shi ba ne a Najeriya, da wasu sassa na ƙasashen Afirka ba. A Najeriya, sauro tana ɗauke da sinadarin da yake sanya zazzaɓi, bayan ya ciji mutum. Amma a Turai, akwai sauro, waɗanda suka fi namu girma kaɗan a idanu. Amma, abin tambayar a nan shi ne, a yaushe ake ganin su? Suna cizo kuwa? Suna sanya zazzaɓi?

Ƙasashen Turai wuri ne da suke da yanayi, wanda akasari, akwai sanyi sosai, yawancin lokuta. A lokacin sanyi, wanda yakan fara ne daga watan Disamba zuwa Watan Faburairu (wasu wurare ma, tun watan Nuwamba zuwa watan Maris), akan samu, sanyi ya yi tsanani sosai. Sanyi ya fi tsanani a ta gabashin ƙasashen Turai, kamar su Rahsa, Iceland, da dai sauransu. A ƙasar Jamus, ana sanyi sosai, kuma yakan kai daga digiri 4 zuwa 0, da kuma ƙasa da 0. Idan ya yi ƙasa da 0, akan ji sanyi mai tsanani. A irin wannan lokaci na sanyi, babu sauro, babu kuma hanyar ma da sauro za su iya rayuwa a irin wannan yanayi.

Amma a lokacin zafi a Jamus, wanda yakan fara tun daga watannin Yuli zuwa Agusta, akan samu ɓulluwar sauro, musamman a wasu wurare, kuma sukan yi cizo. Yawancin sauro, an fi artabu da su ne a jeji, ko kuma inda akwai lambuna, ko wajen shaƙatawa. Idan muka ɗauki Jamus alal misali, Jamusawa suna son shawagi a lambuna da kuma zuwa yawo cikin jejinsu. Ta haka ne, a wajen shan iska, musamman da yamma, akan samu sauro su yi cizo. Idan har hakan ya faru, waurin yakan ɗan yi fushi, wato ya ɗan kumbura na alamar cizon sauro, kuma kafin ɗan wani lokaci ƙalilan, wajen yakan baje. Duk da haka, sauronsu a nan, ba sa sanya zazzaɓi.

Sai dai kuma, akwai zazzaɓi da ake fama da shi a nan, mai kama da na cizon sauro. Jamusawa suna kiran wannan zazzaɓi da suna “Grippe.” Wato, duk wanda ya taɓa kamuwa da zazzaɓi na malariya, kuma ya zauna a Jamus, ko wasu sassa na ƙasashen Turai, kuma ya yi zazzaɓi na “Grippe”, zai ji shi ne, kamar irin na cizon sauro, wato cutar malariya. Dukkan ilahirin jikin mutum zai ɗau zafi, ciwon kai, da dai sauransu da duk mai malariya yake ji a lokacin fama da rashin lafiyar.

Duk da haka, a wajen Turawa, akwai banbanci. Dalilin kuwa shi ne, zazzaɓi mai ɗauke da sinadarin cutar sauro yana da illa matuƙa, tun da yana kisa. Kamar yadda aka ƙiyasta, kowace shekara, mutane sama da 500,000 suna mutuwa a ta dalilin sauro. Hakazalika, idan mutum ya shigo Jamus daga nahiyar Afirka, ko inda ya kamu da cutar cizon sauro, kuma ta bayyana cewa, yana ɗauke da zazzaɓin malariya, kuma aka kai shi asibiti, to akan killace mutum ne a wani ɗaki. Likitoci, idan za su shiga wannan ɗaki, sai sun yi shiga irin na lokacin Korona, wato dukkan jiki, daga kai har zuwa sawu, sai an sanya tufafin-kariya. Mai jinya kuwa, ba zai bar wannan ɗakin ba, sai ya sha magunguna da tasa-tasai, an kuma tabbatar babu wannan cutar ta malariya.

A taƙaice dai, duk da babu zazzaɓin malariya, akwai zazzaɓi mai suna “Grippe”, mai kuma jikkata mutum, idan mutum ya kamu da shi.

Umma Aliyu Musa Malama ce a jami’ar Hamburg da ke Jamus, kuma daga can Jamus din ne ta turo mana wannan gudunmawar

Show More

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
Translate »