Tsohon shugaba Goodluck Jonathan. Asalin hoton: The Guardian Nigeria News.
|
Getting your Trinity Audio player ready...
|
Da’awa: wani mai amfani da shafdin X yayi da’awar cewa tsohon shugaban Najeriya Goodluck Jonathan zai yi takarar shugabancin kasa a zaben shugaban kasa da za a yi a shekara mai zuwa.

Hukunci: Yaudara ce! Ya zuwa yanzu babu a hukumance cewa Jonathan zai yi takara ta shugaban kasa a zaben shugaban kasa a 2027.
Cikakken Labarin
Yayin da zaben 2027 ke kara karatowa a Najeriya magoya bayan ‘yansiyasa na kara zafafa muhawara musamman a shafukan intanet inda ake samun wadannan ‘yansiyasa mabanbanta na yada da’awa kala-kala.
Daya daga cikin irin wadannan da’awa ita ce ta shafin na X (da aka ajiye nan) inda wasu magoya bayan jam’iyyar ADC wato ADC Vanguard suka yi da’awar cewa Shugaba Goodluck Jonathan zai yi takarar shugabancin Najeriya a zaben da za a yi da zai zo a nan gaba.
ADC Vanguard ta yada wani bidiyo mai tsawon dakika 30 wanda ya nuna magoya baya na maurna da shewa bayan da suka ga tsohon shugaban na Najeriya.
Ya zuwa ranar 7 ga watan Mayu,2026 wannan wallafa ta samu wadanda suka kalla (views)589,300 da wadanda suka nuna sha’awarsu (Likes)5,900 da wadanda suka yi tsokaci (comments)954. Haka kuma an yada a shafin Facebook kamar yadda ake gani a nan.
Wannan wallafa ta samu masu tsokaci kala-kala tun bayan da aka yada ta.
Africa Update (@EngrDaniel) bai amince da wallafar ba inda ma yake cewa,
“Bai taba cewa yana takara ba; sai dai ya fadawa taron jama’a cewa siyasa ba wasan kwamfuta ba ne, kuma bai ce zai yi takara a ADC ba, ya dai yi magana ga dandazon jama’ar.”
Wani mai amfani da shafin, Corgito (@Shaddai_001), wanda ya nuna rashin gamsuwarsa da da’awar ya rubuta cewa “Shin me yasa wannan yayi kama da labarin karya.?”
Duba da yadda ake martani game da wannan labari hakan ya sanya DUBAWA ganin dacewar gudanar da bincike na gano gaskiyar labarin.
Tantancewa
Mun gudanar da bincike ta hanyar amfani da wasu muhimman kalmomi , amma babu wata kafar yada labarai sahihiya da ta ba da bayani kan wannan labari duk kuwa da girman mutumin da aka ce yayi wannan kalami.
Sai muka binciki bidiyon inda muka gano wanda ke zama mai tsawo nasa a shafin Instagram na gidan talabijin na Arise. A bidiyon an masa take da cewa “Wani gungun mutane yayi kira ga Jonathan yayi takarar shugaban kasa a 2027.”
A cikin bidiyon Jonathan ya fadawa gungun matasan a Abuja cewa sai yayi tuntuba ne kafin amincewa yayi takara a zaben na 2027.
“…Kunzo yau kun bukaci na yi takara, na jiku. Takarar shugaban kasa ba wasan kwamfuta ba ne, zan yi tuntuba mai fadi,” a cewarsa.
Wasu kafafan yada labaran kamar African Independent Television (AIT), Daily Times, da Galaxy Television, suma duk sun yi rahoton..
Kafin dantakara a hukumance ya bayyana aniya ta takara a Najeriya, dole sai mutum ya fito ya bayyana aniyarsa ta takara a bainar jama’a , sannan ya samu inda zai tsaya takara sannan a mika shi ga hukumar zabe mai zaman kanta (INEC).
Babu daya daga cikin wadannan da ya faru a dangane da takarar ta Jonathan ya zuwa lokacin rubuta wannan rahoto. Shima Jonathan bai bayyana ba a shafinsa na X da Instagram.
A Karshe
Da’awar cewa Goodluck Jonathan zai yi takarar shugaban kasa a 2027 yaudara ce! Duk da cewa masu goyon bayansa sun bukace shi ya fito , a karankansa bai bayyana aniya ta tsayawa takara ba a hukumance ko wata jam’iyya ta ce ta tsayar da shi takara ba.
