African LanguagesHausa

Ba haka ba ne! NYSC ba ta shirin sauya wa masu yi wa kasa hidima rigar inifam

Getting your Trinity Audio player ready...

Da’awa: wani mai amfani da shafin Facebook na da’awar cewa Hukumar NYSC na so ta dinkawa masu yi wa kasa hidima sabbin inifam

Ba haka ba ne! NYSC ba ta shirin sauya wa masu yi wa kasa hidima rigar inifam

Hukunci: Karya ce! Shafin da hukumar ke amfani da shi a hukumance bai yi wani bayani kamar haka ba. Sa’annan binciken mahimman kalmomin dada muka yi bai nuna mana labarin a shafukan kafofin yada labarai masu sahihanci ba.

Cikakken bayani

Hukumar Kula da Masu yi wa kasa hidima (NYSC) shiri ne da gwamnatin Najeriya ta samar a zamanin mulkin sojoji dan damawa da matasan Najeriyar da suka kammala karatun jami’a da sauran makarantun da akan kammala bayan sakandare wajen gina al’umma da bunkasa kasa.

Wani mai amfani da Tiktok Classy Pee ya wallafa a shafinsa cewa hukumar na so ta dinka sabbin inifam ma masu yi wa kasa hidimar. Hoton da ya hada da labarin ya nuna wani mutun ya na sanye da sabbin kayayyakin da ake da’awar za’a fara amfani da su, wanda kuma ya nuna irin banbance-banbancen da ke tsakanin tsohon da sabon.

Wannan hoton bidiyon da aka yi wa taken “proposed new NYSC kits” ya sami alamar likes gida 2,543 an yi tsokaci 504 yayin da aka kuma sake raba labarin sau 134 tun bayan da aka wallafa labarin ranar daya ga watan Yunin 2024. Wannan bidiyon dai ya shuhura a shafukan Facebook da TikTok

@Lola___, yayin da take mayar da martani dangane da hoton da ta gani a TikTok cewa ta yi, “Yanzu da ya kai lokaci na na yin NYSC inifam din ya zama irin na ‘yan banga.

Wani mai amfani da shafin kuma @bignelly, ya bayyana rashin gamsuwarsa ya rubuta cewa, “Ni dai gara in sa tsohon in gama kafin a canza. Ba na son wannan.” Mutane da dama kuma sun yi tambaya ne kan sahihancin wannan bayanin baki daya a wurin tsokacin. 

Yadda wannan labarin ya shiga ko’ina ne da ma hukumar da ake magana a kai ya sa muka dauki nauyin tantance batun.

Tantancewa

Shafin NYSC na da wani gefe inda ake iya ganin duka sabbin abubuwan da hukumar ke yi, amma da muka duba wurin babu wani abun da ke bayani kan rigunan na NYSC wanda ya fara sa mu shakkar sahihancin wannan bayanin.

Haka nan kuma mun lura cewa rigunan da aka nuna kamar an yi amfani da manhajar AI ne wanda ke kwaikwayon dabi’un dan adam. Dan haka kusan kowa zai iya yin wannan zanen ko kirkiro irin wannan hoton dan ya yaudari jama’a 

DUBAWA ta kuma yi binciken mahimman kalmomi dan ganin ko za ta sami karin bayani daga dangane da batun, musamman a sauran kafafen yada labarai masu sahihanci, amma ba mu sami komai ba, wanda ya kara sa mu shakka.

Daga nan mun kuma duba shafin hukumar ta NYSC a X da sauran shafukan da ta mallaka a sochiyal mediya dan ganin ko ita da kanta ta yi labari kan sabbin kayayyakin, inda a nan ma ba mu sami wani labari makamancin hakan ba.

Daga nan ne DUBAWA ta tuntubi ofishin hulda da manema labarai na hukumar NYSC dangane da wannan da’awar. Ofishin ya tabbatar mana cewa zai gudanar da bincike. Ba da dadewa ba bayan nan, NYSC ta fitar da sanarwar da ke karyata labarin.

Sanarwar ta ce duk abubuwan da ake rabawa masu yi wa kasa hidima a lokutan da suka je NYSC na nan yadda suke babu abin da aka canza. Sun kuma yi kira ga al’umma da su yi watsi da duk wani bayanin da aka yi dangane da sabbin kayayyakin a shafin TikiTok, kuma suna cigaba da yunkurin rarrabawa kayayyakin da ake bukata a duka sansanonin 37 da aka saba taron farko na yin NYSC din, a shirye-shiryen da ake yi na karbar rukunin B na shekarar 2024.

“Wannan gargadi ne ga infuluwensas na soshiyal mediya da su daina amfani da tambarin NYSC a kan shafukansu dan suna iya bata wa hukumar suna ta yin hakan, kuma buga da kara duk wadanda aka kama za su fiskanci sharia,” a cewar sanarwar

A Karshe

Da’awar cewa hukumar NYSC ta canza inifam ba gaskiya ba ne. Sanarwar da jami’in hulda da kafafen yada labarai ya fitar ua nna cewa hukumar ba ta da niyyar sauya kayan NYSC din.

Show More

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button