African LanguagesFact CheckHausa

Babu hujja kan ikirarin wani mai amfani da Instagram cewa sinadarin fluoride na sa yin furfura da wuri

Getting your Trinity Audio player ready...

Da’awa: Sinadarin fluoride da ke cikin man goge hakora na jawo furfura a gemu da wuri ga maza.

Babu hujja kan ikirarin wani mai amfani da Instagram cewa sinadarin fluoride na sa yin furfura da wuri

Hukunci: ƘARYA CE. Binciken DUBAWA ya gano cewa babu wata huja ta kimiyya, likitanci ko hukumar da ta danganta fluoride ko man goge hakora da farin gashin maza.

Cikakken Bayani

Fluoride wani sinadari ne da ake samu a cikin ruwa, ƙasa, abinci, da kuma yawancin kayan tsaftar hakora. Cibiyoyin kiwon lafiya na duniya irin su Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) da Kungiyar Likitocin Amurka (ADA) suna nanata cewa fluoride da ke cikin man goge hakora ba mai hatsari ne ba, muddin aka yi amfani da shi yadda ya kamata. Haka kuma yana taka muhimmiyar rawa wajen rage lalacewar hakora.

A cewar shafin yanar gizo Healthline, furfura wani lamari ne na halitta wanda ke fitowa saboda abubuwa kamar: tsarin halitta, shekaru, shiga damuwa, da ƙarancin wasu bitamin — musamman B12, baƙin ƙarfe (iron) da tagulla (copper).

Wani shafin Instagram mai suna northern_vine ya yada wani bidiyo (an adana nan) inda wani mutum ke cewa yawancin samari ba wai shekaru ne ke kawo musu farin gashi a gemunsu ba, sai dai fluoride daga man goge hakora.

Mutumin ya ce, ruwan man goge hakora da yake zuba a gemu lokacin wanke hakora yana shiga gashin gemu ne, kuma shi ke haddasa furfura da wuri.

Zuwa ranar Laraba, 19 ga Nuwamba, 2025, an kalli bidiyon sau 6,991 da an yi martani sau 185.

Wasu masu amfani da Instagram sun karyata ikirarin, wasu kuma sun yi barkwanci akai.

Wani @zumariouss ya rubuta: “Farin gashi halitta ne; ma har ɗan shekara 12 a gidansu suna da shi, wasu kuma suna kai 50 ba su da ko ɗaya.”

Shi kuwa @mcyareema ya yi raha yana cewa zai fara goge hakora sosai “domin ya fito da farin gashi.”

Saboda irin yaduwar bayanan ƙarya kan lafiya a kafafen sada zumunta, DUBAWA ta gabatar da bincike don tabbatar da sahihancin ikirarin.

Tantancewa

DUBAWA ta duba bayanan hukumomin lafiya na duniya da suka haɗa da  Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) da Kungiyar Likitocin Amurka (ADA) da Hukumar Yaƙi da Cututtuka Masu Yaɗuwa (CDC) da Hukumar Tantance Inganci Abinci da Magunguna ta Najeriya (NAFDAC).

Mun gano cewa hukumar ADA ta bayyana cewa yawan amfani sinadarin fluoride a lokacin da hakora ke girma na iya jawo raunin haƙora, wanda alamunsa suka haɗa da, farin layi a haƙori, ko ƙuraje a hakora idan sun tsananta.

Hukumar CDC kuma ta shawarci iyaye su rika tabbatar da yara sun zubar da man goge hakora ba tare da hadiyewa ba.

WHO ta bayyana cewa ɗaukar dogon lokaci ana amfani da fluoride zai iya jawo raunin haƙora, da bayyanar fatar dasashi.

Amma babu wani rahoto daga wadannan hukumomi da ya nuna cewa sinadarin fluoride na haifar da furfura da wuri.

Ra’ayin Masana

DUBAWA ta tuntubi Aliyu Argungu, masanin lafiyar fata a Asibitin Koyarwa ta Jami’ar Usmanu Danfodiyo da ke Sokoto, wanda ya bayyana cewa wannan da’awar ba ta da madogara.

“Ban taba ganin wani bincike ko wani rahoto da ya nuna fluoride na haddasa farin gashi ba. Kuma ban taba ganin wani mara lafiya da wannan matsalar ta same shi saboda fluoride ba” in ji Likita

Ya kara da cewa furfura na faruwa ne saboda yawan shekaru, gado, matsalolin fatar jiki, damuwa, ko kuma shan taba, amma ba fluoride ba.

Haka kuma wani Farfesa a fannin kimiyyar sinadarai, Sani Gumel na Jami’ar Bayero Kano (BUK), ya bayyana cewa farin gashi wata dabi’a ce ta halitta da mutum zai iya fara samu a ko wane lokaci bayan ya balaga.

“Babu wata hanya ta sinadari ko hujar kimiyya da ta nuna fluoride na haddasa farin gashi. Abubuwan da ke haddasa shi sun shafi tsufa da damuwa da raguwar sinadarin melanin a jiki, ba fluoride.”

A Karshe

Ikirarin cewa sinadarin fluoride daga man goge hakora yana haifar da furfura da wuri ba gaskiya ba ne.

Show More

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button
Translate »