Da’awa: Wata mai amfani da shafin (Facebook user) ta wallafa (post) wani bayani inda tayi da’awar cewa shan tsimi na ganyen abarba na magani ko tsayar da gudawa.

Hukunci: Babu wata sheda da ta nuna cewa ganyen na abarba na tsayar da gudawa, kwararru sun nunar da cewa shan maganin nan na ruwan gishiri da sukari da kaucewa cin wasu nau’ika na abinci da neman shawarwari masana shine mafita.
Cikakken Sakon
Ciwon Gudawa da ake kira Diarrhoea a Turance shine yin bayan gida ruwa-ruwa da ake kira zawo, kuma yana kama yara da manya saboda cin abinci ko ruwa mara tsafta ko da ya lalace. Yawanci manya kan yi zawayi ko da sau daya a shekara su kuwa yara sau biyu a shekara kamar yadda bayanan cibiyar lafiya ta kasa suka nunar, cutar ta gudawa da ake kira diarrhoea na iya zama ta kankanin lokaci, ko ta yi muni yadda za ta iya daukar kwanaki biyu ko uku ko ma sama da haka.
Wata mai amfani da shafin Facebook (Facebook user) ta wallafa (post) wani bidiyo da ke nuna cewa idan aka jika ganyan abarba a ruwa aka sha yana maganin gudanawa tsakanin yara da manya. Ta nemi masu amfani da shafin su wanke ganyen abarbar su mitstsika shi kafin a tafasa a ruwa. Ta kara da cewa manya na iya shan kofi guda na ruwan sau biyu a rana tsawon mako guda, ta kuma gargadi masu amfani da tsimin kada su ba wa mace mai ciki da yara kanana kasa da shekaru biyu.
“Bara na koya maku yadda za ku yi maganin gudawa kuna zaune a gidanku. Idan kuka ci wani abu da ya bata maku ciki ko abinci mara kyau, sai ku nemi ganyen nan da ke kan ayaba da lita daya ta ruwa, ku tafasa su na tsawon kimanin mintuna 15, sai a bari yayi sanyi a sha kofi daya, a sha sau biyu a rana tsawon mako guda, nan da nan za ka ga gudawar ta tsaya.’’
Ta kara da cewa “idan yaronku ya kai shekara biyar yana iya shan kashi daya bisa hudu na kofi wannan magani sau biyu duk rana tsawon mako guda. Kada a bari yara kasa da shekaru biyu su sha wannan magani ko ma mace mai ciki.”
Ya zuwa ranar 9 ga Afrilu, 2024 wannan wallafa ta samu masu nuna sha’awa su 39 da wadanda suka kunna suka gani 2000.
DUBAWA ya ga muhimmanci da ke akwai na tabbatar da gudanar da bincike ganin yadda hakan ka iya shafar lafiyar yara da su kansu manyan.
Tantancewa
Bincike (Research) kan alfanu da ke tattare da ganyen abarba da likitoci kamar Farid Hossain, Shaheen Akhtar, da Mustafa Anwa, sun bayyana cewa jijiyoyi da abarbar kanta ana amfani da su magani wajen hana kumburi. Bayanan da aka tattara sun nunar da cewa ana hada tsimi da jijiyar abarba don maganin gudawa.
Wata makala (article) da shafin Healthline ya wallafa ya duba alfanun abarba da ganyenta ta fuskar maganin gargajiya da magunguna na zamani madadin na bature, an kuma gano cewa abin da ake matsa daga ganyen na abarba yana maganin rage kiba da taimakawa wajen saukin narkewar abinci da maganin hana kumburi da sauransu. Abin lura anan shine irin wannan bincike an yi sune sama-sama, maana ba a zurfafafa ba.
Ra’ayin Kwararru
A lokacin da aka tambayi Johnson Udodi, jami’in lafiya a babban asibitin Tarayya na Abuja yace idan jiki ya rasa ruwa ana mayar da shi ta hanyar amfani da ruwan gishiri da sukari na fakiti da wasu magungunan kashe kwayoyin cuta na antibiotics. Dr. Udodi yace waccan da’awa dauke hankalin mutane ce daga amfani da hanyar da ta dace wajen tsayar da gudawa ko zawayi.
“ Rashin ruwa da sauran sinadarai a jiki idan yayi yawa yana jawo rasa rai, kamar yadda muka gani bayan barkewar annobar kwalara a wasu sassa na Najeriya. Idan aka rasa ruwan jiki ana maye gurbinsa ne da ruwan gishiri da sukari wanda ake hadawa a gida da wanda ake hadawa a kamfani, wannan dai shine mafi dacewa idan za a yi maganin cutar gudawa.”
“Wannan hanya ce mai sauki a kokari na kare rai. Likitoci sau tari su kan bayyana amfani da magungunan kashe kwayoyin cuta na antibiotics, kuma ana samun sauki cikin sauri, babu dai isassun shedu da ke nuna cewa hade-haden tsimin abarbar yana maganin wannan cuta kamar yadda mai da’awar ta nunar.”
Ya kara da cewa “Wannan da’awa na iya dauke hankalin masu neman maganin gudawar daga daukar matakin da ya fi dacewa wato shan maganin hadin ruwan gishirin da sukari, sannan a nemi kulawar likitoci.”
Haka itama Nneka Ogbodo,babbar likita a Asibitin Babban Birnin Tarayya Abuja tace ita a nata bangare ba ta taba ganin wata matsaya da aka cimma ba, cewa ganyen na abarba na maganin gudawa koma yana da wata fa’ida a jikin dan Adam. Tace gudawa cuta ce da cikin sauki ake iya maganinta amma kuma cikin sauki a aikata abin da ba daidai ba. Shan ruwan gishiri da suka ri shine mafi kyau a maganin cutar gudawa sannan a nemi kulawar likitoci.
“Bani da wata masaniya kan amfani da abin da aka matsa daga ganyen abarba cewa na da wata fa’ida a jiki, mutane su kula da irin bayanan da suke gani a kafafan sada zumunta domin wani maimakon shawo kan ciwo sai ya haifar da wata babbar cuta.”
“Cutar gudawa, cuta ce da ba wahala za a iya shawo kanta, amma kuma idan ba a lura ba tana iya haifar da babbar matsala, idan ba a ba da kulawar da ta dace ba. Shan maganin ruwan gishiri da sukari na da amfani sosai a irin wannan yanayi kafin samun kulawar likita. A cewarta
Karshe
Babu wata hujja da ta tabbatar da cewa ganyen da ke kan abarba na maganin gudawa. Kwararru sun ba da shawarar amfani da hadin sinadarin gishiri da sukari wanda aka hadawa a kamfani ko wanda aka hada a gida. Kaucewa cin wasu nau’ika na abinci da shan magunguna da suka dace sune hanyoyi na maganin cutar gudawa.
An fitar da binciken karkashin shirin gano gaskiya na DUBAWA 2024 da shirin kwararru na Kwame KariKari da hadin gwiwar Premium Times / UNILAG, don dabbaka “gaskiya”a aikin jarida da inganta ilimin aikin jarida a fadin kasar.