African LanguagesHausa

Bayanan mai amfani da shafin X kan adadin masu cutar HIV ba daidai ba ne

Getting your Trinity Audio player ready...

Da’awa: Wani mai amfani da shafin X yayi da’awa daban-daban kan adadin ‘yan Najeriya da ke dauke da cutar HIV da yadda ake fadakar da su da yadda ake samun yara masu dauke da cutar da yadda ake yada ta.

Bayanan mai amfani da shafin X kan adadin masu cutar HIV ba daidai ba ne

Hukunci: YAUDARA CE. Daya daga cikin da’awar karya ce, yayin da dayar kuma ke zama ba cikakkiya ba, babu bayanai da ake da su sabbi kawo yanzu, bayanan da ake da su a can baya ma ba cikakku ba ne.  

Cikakken Sako

Cuta mai karya garkuwar jikin dan Adam (HIV) ko ma cutar (AIDS) na ci gaba da zama barazana ga fannin lafiya a Afurka, musamman a kudu da saharar Afurka, yayin da ake da kimanin mutane miliyan (25.7 million) na rayuwa da kwayoyin cutar ta HIV. Kasar Afurka ta Kudu ita ke kan gaba da yawan  masu fama da cutar ta HIV inda kabilar Eswatini ke kan gaba da mafi yawa na masu cutar (highest prevalence). Kimanin kaso 26 cikin dari na al’ummar.

Najeriya ma na fama da matsanancin hali a dangane da cutar, inda ake da kiyasin kaso 2.1%  na manyan mutane da ke dauke da cutar, wannan adadi na nufin akwai mutane kimanin miliyan biyu na dauke da kwayoyin cutar HIV a Najeriya ya zuwa 2023.

Kokari na kawar da HIV/AIDS na samun ci gaba duba da kokari da gwamnatoci ke yi da taimako da ake samu a tsakanin kasa da kasa. Ya zuwa shekarar 2020 kasashen Afurka da dama sun cika buri na kaso ( 90-90-90 target) yayin da aka samu kaso 90 cikin dari na mutanen da ke dauke da kwayoyin cutar HIV sun san matsayinsu suna karbar magani, suna kuma samun sauki. Ana daukar matakai da dama da suka hadar da ba da kai ayi wa maza kaciya don radin kansu da rage yada cutar daga uwa zuwa jaririnta.

 A Najeriya an samu yawaitar wayar da kan jama’a inda suke zuwa ana yi masu gwaji dama rage nuna wa masu cutar kyama, yayin da ake da kaso 89% na masu dauke da kwayoyin wannan cuta sun san matsayinsu. Duk da samun wannan nasara samun magungunan na (ART) na ci gaba da zama kalubale duk da cewa an gwada mutane kaso 77% suna karbar magani.

Wani mai amfani da shafin X mai suna Kwena Molekwa yayi wata da’awa a dangane da yawan masu cutar HIV a Najeriya inda yayi martani da zargin Afurka ta Kudu da zama ja gaba a mutane da suka fi yawa da ke dauke da cutar, wannan martani ya samu mutane sama da 9000 da suka kalla da martani 78 da masu tsokaci bakwai da wadanda suka sake wallafawa su hudu ya zuwa ranar 11 ga Satumba, 2024. 

Wani mai amfani da shafin Facebook, Put South Africans First, shima ya fitar da tasa wallafar a ranar 16 ga Agusta,2024 wanda ya samu martani 18, da tsokaci 14 da wadanda suka sake yadawa 6 ya zuwa ranae 11 ga Sarumba,2024.

DUBAWA ta gudanar da bincike kan da’awar guda biyu don gano gaskiyar bayanan. 

Da’awa ta  1:’Yan Najeriya 90,000 suke da masaniya suna dauke da cutar HIV a kasar da ke da yawan jama’a sama da mutum miliyan 200.

Hukunci: KARYA CE. Bayanai da aka tattara na hadin gwiwa na Majalisar Dinkin Duniya kan cutar ta HIV/AIDS (UNAIDS) sun nunar da cewa “yan Najeriya  1.9 million suke dauke da cutar ya zuwa 2021. Sannan kaso 1.7 miliyan sun san matsayarsu na dauke da cutar wanda ke nufin kaso 89 cikin dari sun sani cewa suna dauke da kwayoyin cutar ta HIV. 

Da’awa ta 2: Najeriya ke kan gaba da yawan yara da ake haifa da kwayoyin cutar  HIV/AIDs

Hukunci: BABU ISASSUN SHEDU. Najeriya ta samu akalla yara da aka haifa masu dauke da kwayar HIV 21,000 a 2020, adadin da ke nuna kaso 14% daga bayanan da shirin na UNAIDS ya gano, sai dai wannan bai nuna irin kokarin da kasar ta yi ba a baya-bayan nan wajen dakile bazuwar cutar a fadin kasar, kokarin da ake ganin zai iya tasiri a irin adadin da za a fitar.  Babu kuma wasu bayanai sabbi kan wannan da’awa.

Karshe

Duk da kasancewar Najeriya a gaba da yawan wadanda ke kamuwa da cutar ta HIV/AIDS a duniya, da’awar cewa akwai karancin wayar da kai da yawan yara jarirai da ke dauke da cutar yaudara ce.

Show More

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
Translate »