African LanguagesHausa

Dino Melaye bai taya Peter Obi yakin neman zabe a bidiyonsa ba

Zargi: Wani bidiyon da ake ta yadawa a shafukan sada zumunta na soshiyal mediya musamman WhatsApp na nuna Dino Melaye yana bayyana goyon bayan sa ga dan takarar shugabancin Najeriya a jam’iyyar Leba, wato Peter Obi, gabannin zabukan na 2023

DUBAWA ta gano cewa bidiyon Melaye ba shi da dangantaka da Peter Obi masu tayar da zaune tsaye ne su ka gyara bidiyon ya fito kamar yana magana a kan Obin, alhali kuma yana wani batu ne daban wanda bai shafi dan takarar ba

Cikakken bayani

Yanzu dai watanni kadan suka rage kafin a gudanar da zabukan 2023 a Najeriya. Kamar yadda aka riga aka zata shafukan soshiyal mediya sun riga sun cika da mahawarori na siyasa. Daya daga cikin abubuwan da suka karfafa hakan shi ne wani hoton bidiyon da ake ta yadawa musamman a WhatsApp, inda ake zargi dan siyasa kuma tsohon sanata Dino Melaye ya bayyana kyawawan abubuwa dangane da dan takarar shugabancin Najeriya a karkashin inuwar jam’iyyar Leba wato Peter Obi.

A cikin bidiyon, Mr Melaye wanda da ma yake da tarihin tayar da zaune tsaye ya ce Mr Obi ne dan takarar da zai fi hada kan ‘yan Najeriya. Inda ya kara da cewa a cigaba da kira ga jama’a da ma jan ra’ayin kowa dan su shiga gwagwarmayar ganin cewa ya sami goyon bayan da ya ke bukata.

“Ina so in ce, yanzu lokaci ne na tunani. Ina bayar da karfin gwiwa ga wannan gangamin. Gangamin da Mr. Peter Obi ya fara. Ya kamata ya fara bi makaranta zuwa makaranta, al’umma zuwa al’umma,  kuma daga kungiya zuwa kungiya a cikin wannan kasar ta mu domin girka sabuwar Najeriya,” Mr Melaye ya bayyana a cikin bidiyon mai tasawon dakiku 38.

Bincike ya nuna cewa bidiyon ya fara fita ne a manhajan tiktok a shafin @lolabaerose inda aka yi mi shi taken 

“Godiya gare ka Mr Dino domin yadda ka ke fadin gaskiya ko da yaushe”

Tuni wannan bidiyon ya ja hankalin ma’abota shafukan sada zumuntar inda har wani mai amfani da shafin @tapcurrent ya ce watakila ma jam’iyyar PDP ta hade da jam’iyyar ta Leba yana mai cewa: 

Hahahahhaha, sun fara sauya gaskiya, kada ku yi mamaki idan har PDP ta ce za ta hade da jam’iyyar Leba.

Wani mai amfani da shafin shi ma @user Kingh, a fakaice cewa ya yi shi kan sa Mr. Melayen mai yiwuwa zai koma jam’iyyar ta Leba. “Dino mai zai koma jam’iyyar Leba cikin wannan makon kuma shi zai lura da wannan bangaren zaben,” a cewar sa.

To sai dai akwai shakku dangane da sahihancin wannan bidiyon domin ko a kwanaki biyun da suka gabata sai da Dino ya sake jaddada goyon bayansa ga dan takarar shugabancin kasar a inuwar jam’iyyar PDP wato Atiku Abubakar, wanda kuma ya kara sanya alamar tambaya kan zargin.

Tantancewa: 

DUBAWA ta fara da tantance bidiyon a manhajar Deepware, wanda ake amfani da shi wajen tantance nagartar bidiyoyi. Sakamakon wannan binciken ya nuna cewa bidiyon ba na bogi ba ne.

Baya ga haka, DUBAWA ta sake amfani da wata manhajar tantance bidiyoyin wato InVid wadda ke bin hotunan bidiyon dalla-dalla. Sakamakon wannan binciken ne ya nuna yadda aka yanka bidiyon aka gyara shi ta yadda zai fadi abin da masu gyarawar su ke so ya fada, wanda kuma ya banbanta daga bayanain da ya yi a ainihin bidiyon.

Ranar daya ga watan Yulin 2022 Mr Melaye ya yi wani bidiyon kansa inda ya yi bayani na tsawon mintuna 6:23 mai taken “Obi mutumi ne nagari amma ba zai iya hada kan ‘yan Najeriya ba:”

A cikin bidiyon, Melaye ya fara da bayyana goyon bayan sa ga jam’iyyar PDP da dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar wato Atiku Abubakar sa’annan ya nuna cewa takarar Obi a jam’iyyar Leba ba wani abun a zo a gani ba ne gabannin zaben na 2023.

Mr Melaye ya bayyana cewa Atiku mutumi ne mai hadin kai ya kuma kara da wadansu kyawawan halayen da ya mallaka masu fa’ida wanda ya nuna cewa shi ne dan takarar da ya fi dacewa da mukamin shugaban kasa.

“Dan haka muna bukatar dan Najeriyan da ya ganin banbanci. Wanda zai sami yardar jama’a daga kowani bangaren kasar, wanda yankunan arewaci da kudanci za su yi amanna da shi kuma wannan mutumin ba tare da ko kyafta ido ba shi ne Atiku Abubakar”, a cewar Melaye a cikin bidiyon.

Lallai Mr Melaye ya yi wannan furucin a cikin bidiyon. To sai dai dangantawar da ake yi da Mr Obi ba a yanzu ba ne, furucin ya zo ne a lokacin da Peter Obi ya kasance dan takarar mataimakin shugaban kasar Atiku, a shekarar 2019 lokacin da ‘yan takaran biyu suka yi takarar mukamin shugaba da mataimaki a karkshin inuwar jam’iyyar PDP.

Bacin hakan bidiyon na tsawon dakiku 38 an gutsuro shi ne daga bidiyon na ainihi wanda ke da tsawon minti 6:25, an fara gutsuran bidiyon ne daga minti 4:30 zuwa minti 4:58.

Mr Melayen da kansa ma ya wallafa bidiyon a shafinsa na tiwita da taken:

“Kalla ……….. SDM. Mr Obi mutun ne nagari amma ba zai iya hada kan ‘yan Najeriya ba. Mahimmancin hadin-kai ya fi rage yawan kudaden da ake kashewa wajen gudanar da gwamnati.”

A Karshe

Bidiyon da ke yawo a shafukan soshiyal mediya ana zargin wai Dino Melaye ne ya ke nuna goyon bayansa ga dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar Leba wato Peter Obi, gabannin zabukan na 2023 ba gaskiya ba ne. An yanko wani bangare ne na wani bidiyon mai tsawo aka yi amfani da shi wajen kaga labarin karya.

Show More

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button