African LanguagesHausa

Bayani: Hatsarin da ke tattare da shan magungunan inganta aikin abinci a jiki da sauran kwayoyin kare garkuwar jikin ba tare da izinin likita ba

Bayan da ta zo mataki na biyu cikin jerin kasashe 10 na farko na kasashe wadanda al’ummominsu ke da mafi karancin shekaru na rayuwa a duniya, tsarin kiwon lafiyar Najeriya ta cigaba kasancewa abun damuwa ga masu ruwa da tsaki a fannin.

Yawancin lokuta a kan shawarci ‘yan Najeriya su kula da lafiyarsu – jiki da kwakwalwa –  domin tsawaita rayuwa da kuma kaucewa irin cututtukan da kan bukaci magunguna kowace rana. A wani rahoton Lancet, sun ce tsarin kiwon lafiyar Najeriya ba ta shirya tinkarar matsalar karuwar cututtukan da ba za’a iya rabawa ba, da ma irin karuwar da ake gani a adadin mace-mace.

Wannan ne ya sa da dama a kasar suka koma ga amfani da wadansu abubuwa na daban wadanda mafi yawancin lokuta suke tattare da hatsari, domin kiyaye lafiyarsu

A ‘yan kwanakin nan, shafukan soshiyal mediya sun cika da alfannun da ke tattare da amfani da kwayoyin da ke inganta abinci da garkuwar jiki saboda ana ganin kamar ba su da wani lahani

Sai dai kwararru sun ce ba haka ba ne.

Bisa bayanan Euromonitor, wani  rahoto a kasidar likitoci na New Zealand, ya nuna cewa cinikin da aka yi kan ire-iren magungunan ya karu da kashi 105 cikin 100 tsakanin 2007 da 2021, kuma a cikin magungunan an fi bayar da fifiko ga wadanda ake zargin suna bayar da kariya musamman daga farkon barkewar cutar COVID-19. 

Wani binciken da BMC Geriatrics suka yi inda suke nazarin tasirin maganin bitamin D (wanda ake sha idan mutun bai shiga rana yadda ya kamata) sun kwatanta yadda talla ke habaka yawan masu sayen magunguna bitamin iri-iri dan yin amfani da su ba tare da izinin likita ba ko kuma ma kulawarsu.

Mene ne multivitamins? 

Multivitamins magunguna ne daban-daban wadanda aka hada cikin magani daya. Yawanci sinadarai ne da akan samu daga abincin da ake ci yau da kullun da kuma sauran albarkatun abincin da ke kewaye da mu.

A cewar shafin Healthline, – wani shafin da ke tsokaci kan kiwon lafiya – yawancin  mutanen da ke shan multivitamins suna yin haka ne dan inganta lafiyarsu, su kare kansu daga karancin sinadaran da ke da mahimmanci ga jiki ko kuma dai su cike gibin da suke da shi a irin nau’o’in abincin da suke ci.

Wani rahoton kuma daga Cibiyar Lafiya ta kasa ko kuma National Institutes of Health ta yi gargadin cewa ire-iren magungunan ba za su iya cike gibin nau’o’i daban-daban na abincin da ya kamata a ce ana ci ba.

Sai dai ya amince da batun cewa wasu magungunan na iya inganta lafiya baki daya su kuma taimaka wajen shawo kan wasu matsalolin lafiya. Alal misali, Calcium da Vitamin D na taimakawa da karfin kashi wajen rage yiwuwar karaya; folic acid na rage samun matsalar haihuwar jarirai da nakasa; yayin da Omega-3 kuma, wanda ake samu daga man kifi ke taimakwa da cututtukan da kan shafi zuciya.

To sai dai shan wadannan magungunan musamman na wani tsawon lokaci na tattare da hadari idan har ba likita ne ya ce a sha ba.

Rahoton Cibiyar lafiyar ta NIH ya bayyana cewa akwai wadansu magungunan da za su iya kara hadarin zubar da jini ko kuma idan har aka sha ana gab da yin tiyata yana iya hana jikin karbar magungunan da akan bayar dan rage radadin zafin ciwon bayan an yi aiki.

“Multivitamins din kuma idan har aka hada su da wasu magungunan wadanda da ma ake sha saboda wata lalura ta daban, suna iya kawo matsala… misali vitamin C da vitamin W suna iya hana magugngunan cutar daji aiki yadda ya kamata.”

Bacin haka, bincike ya nuna cewa shan magungunan ba tare da izinin likita ba na iya kara hadarin samun matsala. Misali, shan vitamin A da yawa na iya janyo ciwon kai, da lahani ga hanta, ko rage karfin kasusuwan jiki, sa’annan yana iya janyo nakasa a jarirai, kafin a kai ga haifan su. Shan iron da yawa kuma na iya janyo amai, kuma shi ma yana iya janyo lahani ga hanta da sauran gabobin jiki masu mahimmanci.

Bayanan da muka yi a sama, mun dauko shi ne daga shafin BMC Geriatrics. Binciken ya kuma nuna yadda shan vitamin D zai iya lalata yanayin calcium a jikin mutun wanda shi ma zai iya janyo cutar da za ta iya lahani ga mahimman gabobin jiki. A cewar bayanan “yawan vitamin D a jiki na iya janyo amai, kishi, rage kiba da hawan jini, da jin ciwo a koda da sauran cututtukan da ka iya kai ga mutuwa nan da nan.

A wata hirar da DUBAWA ta yi da wani kwararre kan magunguna a jami’ar Legas (UNILAG) Francis Agbaraolorunpo, ya bayyana cewa tsarin kiwon lafiya a Najeriya ne ke sa mutane amfani da magungunan da likita bai rubuta mu su ba.

Ya ce da ma irin sinadaran da ke cikin magungunan daga abinci ne ya kamata a samu, amma kuma ga yawancin wadannan nau’o’in abincin sun yi tsada sosai ba za su iya saye ba, shi ya sa ya fi mu su sauki su je su sayi ire-iren wadannan magungunan su sha.

Ya kara bayyana cewa wasu sukan yi amfani da multivitamins din ne a sadda suke bukata a maimakon tuntubar likita saboda tsawon lokacin da za su jira kafin su ga likitan da ma yawan kudin da za su kashe, inda ya ce idan har sun yi amfani da magungunan na wani takaitaccen lokaci ne ba lallai ne ya kasance hadari ba ko kuma ma ya janyo mu su wani hadari.

“Yawanci mata da ‘yan mata ne ke bukatar multivitamins saboda jinin da suke yi wata-wata. Idan suka rasa jini, sukan rasa sinadarin iron dan haka akwai bukatar sake inganta shi, kuma jikin ba zai iya mayar da sinadarin da kan shi ba dole sai da tallafi. Akwai matan da sukan fara samun alamun karancin sinadarin iron din a jikinsu, kuma yawanci abun da ya sa sukan sha magungunan da kansu ke nan ba tare da izinin likita ba.

“Mata masu juna biyu da wadanda ke shayarwa suna raba sinadaran da ke jikinsu da ‘ya’yansu ne, kuma yawancinsu ba za su sami damar cin irin nau’o’in abincin da jikinsu ke bukata ba.”

Domin sake tantance wannan batun, Mr Agbaraolorunpo ya ce akwai wadansu magungunan wadanda idan aka sha su da yawa sukan yi lahani ga gabobin jikin mutun. Wadannan sun hada da sinadarin da ke dauke mai.

Ya kuma yi gargadin hadarin da ke tattare da shan vitamin din na wani tsawon lokaci.

“Bari in yi bayani dalla-dalla: vitamins sun rabu gida biyu. Akwai wadanda ruwa ke ja akwai kuma wadanda maikon jikin mutun ke ja. Wadanda ke shiga maikon da ke jikin mutun sun hada da Vitamin A, K, D da E. Duk wadanda ke shiga maikon jikin mutun suna iya zama a wurin dindindin ba tare da sun fira ba kuma wannan na iya kasancewa guba ga jikin domin ba zasu tafi ta dadi ba. Dan haka idan har mutun ya yi amfani da magungunan ba bisa ka’ida ba, suna iya yi wa jikin yawa har su yi lahani a mahimman gabobi..

“Yawancin lokuta ba lallai ne wadannan magungunan su kasance suna dauke da sinadaran da yawa ba wata sa’a dan kankani ne amma duk da haka, ka da a yi amfani da su a wuce watanni shidda.”

A waje guda kuma ya ce ya lura cewa yawancin wadanda suke son sayen magungunan domin samun sinadaran da jikin ke bukata a maimakon cin nau’o’in abincin da ke dauke da sinadaran wadanda kuma suke ganin kamar magungunan na iya maye gurbin abincin da ake ci na iya shiga matsala da nau’o’in magungunan da kan makale a cikin jikin mutun.

Dangane da yadda ya shafi tsofaffi, likitan ya ce bukatar wadannan sinadaran na multi vitamins kan karu da yayin da mutun ke kara shekaru. Sai dai a cewar sa, shan magungunan ba tare da izinin likita ba na da hadari sosai.

Mr Agbaraolorunpo ya yi bayanin cewa wadansu mutane na iya samun sinadarin iron da yawa yayin da suke amfani da multivitamins wanda kuma zai iya lalata hantar mutun da ma wasu karin gabobin masu mahimmanci.

Ya ce ko da shi ke ana iya sayen ire-iren magungunan ba tare da izinin likita ba, daga  lokaci zuwa lokaci, a duk sadda za’a sayi wadanda ke da hadari a tabbatar an sami izinin likita. 

“Hasali ma akwai wani mara lafiya wanda na ke gani da ke wanda jikinsa ba ya karbar wasu magungunan da ke dauke da sinadaran multivitamin, dan haka sai muka duba tarihin kiwon lafiyarsa. Wasu jikinsu ba ya domin wanda ke jikinsu ya isa, dan haka jikin uai ki karin da ake so a yi mi shi.”

Likitan ya kuma ce tilas a dauki matakan kariya idan ana so a bai wa tsofaffi magungunan, ya ce a fara da gwajin da zai tantance karfin mahimman gabobin jikinsu irin su hanta, da koda. Mr Agbaraolorunpo ya ce tilas a yi haka domin idan mutun na tsufa gabobin jikin shi ma na tsufa kuma su ne za su tace maganin da za su sha, dan haka dole a tabbatar cewa yana da karfin tace maganin.

“Magunguna ba su tsayawa a jikin mutun dindindin. Da wadanda suka riga suka yi shekaru da yawa, dole a yi hattara wajen ba su magunguna musamman a yi la’akari da yawan maganin da kuma tsawon lokacin da za su dauka suna sha. Ka da a yi amfani da multivitamin yadda ake so ko kuma ba tare da bin ka’ida ba. Misali idan mai shekaru sosai ya yi korafin ciwon kafa, ka da kai tsaye a yi tunani ba shi sinadarin calcium wanda ke kara karfin kashi, a maimakon haka a je a duba wajen likita kila alama ce ta wata cuta ta taban. Domin idan ba a duba ba aka fara bayar da calcium din tamkar ana dura mi shi siminti ne. Abin da likitoci ke yi shi ne gwada abun da ya ke riga ya ke cikin jikin mutun idan ya isa, to ba sai an kara ba.

“Yawancin magungunan da ake amfani da su haka sinadarai ne wadanda ke ciki gibi ko inganta nau’o’in abinci ko kuma wadanda ke wanke gabobin jikin da manyan kamfanoni ke saidawa. Sai dai kowane jiki ya banbanta bisa la’akari da yawan nau’o’in abinci da sinadaran da ya ke da shi a jiki da kuma yawan da ya ke bukata. Domin idan ya yi yawa jikin zai ki karba.”

Kwararren ya bayyana cewa abun da ya fi kawai shi ne a je a ga likita, wanda zai rubuta maganin da za’a iya sha na tsawon watanni uku kacal amma zai bayar da shawarar cin abincin da zai gina jiki da kuma kiyaye kai daga sha ko cin abubuwan da ka iya mayar da hannun agogo baya. Sai dai ya fada hakan tare da jaddada cewa matsalar tsadar asibiti da magunguna ne zai sa mutane so dauki wadannan magungunan ba tare da izinin likitocin ba.

“Ba lallai ne zuwa ganin likita ya yi tsada ba. A tunani na shi ya sa mu ke daukar inshora ta lafiya amma dai idan ana batun gaskiya ba kowa ne a Najeriya zai iya samun inshorar ba. Da inshora ya kamata a ce mutane sun iya zuwa ganin likita, wanda zai rubuta magungunan da za’a sha na watanni uku, Wajibi ne a ga llikita ko da ana so a sha magani na wata daya ne.”

Ya ce kalubalen zai kasance idan aka hada magunguna iri biyu amma kuma wasu sinadaran da suke dauke da su iri daya ne, hakan zai kara yawan sinadaran ta yadda za su yi yawa a jiki. 

Mr Agbaraolorunpo ya ce akwai hanyoyin gargajiya na inganta garkuwar jiki wadanda za’a iya amfani da su ba tare da sayen magungunan multivitamins ba. Wadannan sun hada da: cin abinci yadda ya kamata, hutawa akai-akai da kuma cin kayayyakin lambu. Bacin haka, wani karin kalubalen kuma shi ne sayen magungunan jabu daga kasuwa, dan haka wannan ma na bukatar taka tsan-tsan.

Show More

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button