Al’ummar kasa da kasa na masu binciken gaskiya wadanda suka gudanar da babban taron su ranar Alhamis 30 ga watan Yuni a birnin Seoul na Koriya ta Kudu, sun zabi binciken da DUBAWA ta yi dangane da maganin gargajiyar Baba Aisha a matsayin wanda ya lashe gasar ire-iren binciken da ke kawo sauyi na shekarar 2023.
An sanar da wannan sakaakon ne yayin da ake taron GlobalFact10, wanda taro ne na shekara-shekara na mambobi fiye da 100, na al’ummar masu binciken wadanda aka fi sani da Gamayyar Kungiyoyin Kasa da kasa na Masu Binciken Gaskiyar Bayanai wato International Fact-Checking Network wato IFCN
Binciken DUBAWA wanda aka yi wa taken “Baba Aisha, likitan karyar Najeriya cinye kudin jama’a kawai ya ke yi domin maganin shi ba ya aiki,” ya yi takara ne da wasu rahotannin binciken guda hudu a rukunnin binciken da suka yi tasiri wajen kawo sauyi a al’umma.
Wadanda aka zaba tare da DUBAWA sun hada da kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP (Faransa/Amurka) Myth Detector (Georgia) da Taiwan Cibiyar binciken gaskiyar bayanai na FactCheck Center (Taiwan)
Kadan daga cikin yadda wannan binciken ya yi tasiri shi ne yadda mahukunta suka ce masana’antar suka kulle, suka fara farautar duk wadanda ke sayar da irin wadannan magungunan a kan titi da ma yadda Hukumar kula da Ingancin Abinci da Magunguna na NAFDAC ta sa aka kama shi kan shi wanda ke sarrafa maganin na Baba Aisha.
Dan jaridan da ya gudanar da wannan binciken, wanda aka shafe watanni biyar anan hadawa, Kemi Busari, ya ce babbar nsararsa a matsayin dan jarida shi ne ya yi abun da zai yi tasiri har ya kawo sauyin da zai amfani jama’a.
“Na yi matukar farin ciki da na da abokan aiki na ne muka sami wannan lambar yabon. Wannan shaida ce da ke nuna cewa mutane a duniya na mutunta dan aikin da muke yi daga wannan kusurwar tamu, kuma muna fatan zamu cigaba da yin wannan aikin na binciken gaskiyar bayanan dan taba rayuwar mutane a Najeriya da yankin yammacin Afirka baki daya.
“Ina so in jaddada cewa lambar yabo na farko shi ne da ni da abokan aiki na a matsayinmu na ‘yan jarida za mu iya kawo sauyi mai ma’ana wanda zai taba rayukan jama’a.”
Busari ya kuma yaba da irin yunkurin da hukumar NAFDAC ta yi tun bayan da aka wallafa binciken.
“Tun bayan da muka wallafa wannan binciken, mahukuntan su ke bin kadin duk batutuwan da muka bayyana, kuma muna gatan cewa za’a hukunta duk wadanda abun ya shafa domin a tsabtace mana al’ummarmu a kare al’ummominmu daga ire-iren wadannan magungunan masu lahanin gaske,” ya kara da cewa.
Gamayyar Kungiyoyin Kasa da kasa na Masu Binciken Gaskiyar Bayanai na da matsuguninta a Cibiyar Poynter, da ke Miami, Florida a Amurka. A shekarar 2015 aka kaddamar ta ita domin sada tsakanin kungiyoyin binciken da ke tasowa a wancan loakacin a kasashen duniya da dama, kuma har wa yau yana kan gaba wajen ganin an samar da bayanai masu gaskiya dan yaki da matsalar yaduwar bayanan karya. IFCN ta ce “ta na taimakwa masu binciken gaskiyar bayanai ta hanyar sadarwa, kara wa juna dani da hadin kai…. Sa’annan kuma ta na inganta wanzuwar binciken a kungiyoyi fiye da 100 a duniya baki daya ta hanyar fadakarwa da horasawa da kuma shirye-shirye na kasa da kasa.”
IFCN tana kuma sanya ido kan abubuwan da ke tashe a al’ummar bincien dan ta bayar da tallafi yadda za ta iya da ma gudunmawa ga irin mahawarorin da ake yi, tare da tallafawa sabbin shirye-shiryen da za su kawo cigaba a aikin jarida.