Hausa

Bidiyon da aka yi wa taken gawawwakin filani a Arewacin Najeriya karya ne

Zargi: Wani bidiyo da ake yadawa a WhatsApp, wanda ke nuna hotunan wasu gawawwakin da aka kona yana zargin wai filani ne walkiya ya kona su, sadda suke kan hanyar zuwa kai hari wata al’ummar kiristoci a yankin Arewacin Najeriya.

Bidiyon da aka yi wa taken gawawwakin filani a Arewacin Najeriya karya ne

Cikkaken Bayanni

Kwanan na wani bidiyo mai tsawon dakiku 29 wanda aka yi ta raba wa a WhatsApp ya yi zargin cewa filani ‘yan bindiga ne walkiya ta fado daga sama ta kona su yayin da suke kan hanyar kai hari wata al’ummar kiristoci da ke yankin Arewacin Najeriya. Bidiyon ya nuna hotunan gawawwaki da dama da barabuzan kayayyaki da baburan da suka kone. Akwai kuma muryoyin da ke magana a wani harshen da ba za’a iya tantancewa ba, da wuta r gobara, da kuma wasu mutane masu kama da ma’aikata.

Bidiyon wanda ya yi kama da wani wajen da tankar mai ta fashe na dauke da kalaman da ke cewa “gawawwakin filani ‘yan bindiga bayan da walkiya ta fito daga sama ya kona su yayin da su ke hanyar zuwa kai hari wata al’ummar kiristoci a Arewa. Wannan ya nuna lallai Allah na amsa addu’o’in Coci. Hotunan na da tayar da hankali.

Tantancewa  

Na farko dai mun gano cewa an taba amfani da wannan bidiyon domin nuna dakarun Najeriya suna kai hari kan ‘yan bindiga a jihar Zamfara wanda Dubawa ta riga ta karyata.

Dan haka ne mai binciken wannan labari ya dauki hotunan bidiyon da aka fara wannan labarin, ya je kam komfuta ya sake musu bincike da manhajojin Tineye da INVID ba tare da samun nasara ba.

Da muka yi amfani da manhanjan Yandex sai muka gano cewa tun shekarar 2019 ake amfani da bidiyon domin ya bayyana a shafuka da dama a ciki har da Facebook. Daya daga cikin su ma wani ma’aikacin Random FB ne ranar 5 ga watan Satumba 2019 wanda aka yi wa taken. “Wannan tsokanan zai iya janyo yaki …. A Afirka ta kudu.

Wani labarin da aka wallafa a norskk square space ranar 18 ga wata Satumba 2021 da taken “Afika ta Kudu, kasar da ta gaza” na zargin cewa fada da kashe-kashe ba wani abu ba ne a al’ummomin  Africa kuma ko shi ma wasu daga cikin hotunan bidiyon daga nan aka dauka

Da muka duba kalmomi mun gani cewa a 2019 aka fara nadan bidiyon lokacin da wata tanka ta fashe ta yi sanadiyyar rayuka 60 ta kuma jikata da dama a kasar Tanzania. Tankar na kan hanyarta na zuwa Dar es Salaam ne, wadda it ace birni mafi girma kafin ta kife a garin Morogoro bisa bayanan da gidan talbijin na Aljazeera ya wallafa.

Rahoton ya bayyana cewa mazauna garin sun taru a wajen hatsarin dan su debi man da ya zube daga tankar ne sadda ta fashe, wutar kuma ta yi sanadiyyar rayukan mutane 60

A Karshe

Bidiyon da ke nuna hotunan wadanda suka kone ana zargin wai Filani ‘yan bindiga ne wadanda walkiya ta kashe su a kan hanyarsu na zuwa kai hari kan wata al’ummar kiristoci a yankin arewacin Najeriya karya ne. Tantancewar da muka yi ya nuna mana cewa wannan lamarin ya afku ne a Tanzania kuma tun a shekarar2019 aka dauki wannan hoton lokacin da wata tankar mai ta fashe a garin Morogoro.

Show More

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
Translate »