Yadda ake amfani da shafukan Facebook a yada bidiyo na karya da ya shafi tsaron Najeriya wadanda ake hadawa da fasahar AI

How Facebook pages use AI-Generated videos to spread false security narratives in Nigeria
Hotunan da aka kirkiro da fasahar AI a shafukan Facebook Asalin hoto: Facebook.
Getting your Trinity Audio player ready...

A watannin baya-bayan nan ana ganin karuwar bidiyo da ake yada su a shafin Facebook bisa da’awar ‘yanbindiga sun kai farmaki ko sun kona kauyuka ko kai farmaki ga jami’an tsaro da ma yin garkuwa da mutane a sassa daban-daban na Najeriya. 

Da dama irin wadannan bidiyo suna kama da na gaskiya inda za ka ga dubban mutane sun kalla da yadawa da tsokaci saboda mutane sun dauka abubuwa ne na gaskiya da suka shafi tsaro.

DUBAWA ta fara gudanar da bincike kan irin wadannan bidiyo farawa da wanda aka yada a shafin Facebook na Emmanuel Okechukwu Aja, ya yada bidiyo (kamar a nan) inda yayi da’awar cewa ‘yanfashin daji sun kona gari a jihar Kaduna.

Tantancewa ta farko ta nunar da cewa asalin bidiyon an hada shi ne da fasahar AI, ba abu ne da ya faru a zahiri ba.

DUBAWA ta gano cewa wannan bidiyon ya kasance daya daga cikin tarin bidiyo da ake hadawa da fasahar ta AI ana bayyana lamura da suka shafi tsaro a sassa daban-daban na Najeriya.

Abubuwan da aka gano sun kara nuna yadda ake amfani da fasahar ta AI a harzuka zukatan al’umma a dangane da kalubalen tsaro da ake fama da shi. 

Domin gano irin girman wannan matsala, DUBAWA ta nazarci shafukan sada zumunta na Facebook guda uku saboda yadda ake yada abubuwa da suka shafi tsaro. Wadannan shafuka akai-akai su kan yada abubuwa da suka shafi tsaro da yawan lokaci da suke yadawa da ma yadda ake yawan samun masu tsokaci.

A binciken an hada da nazari na bidiyo da aka hada da AI da aka wallafa a shafin da nazari kan abubuwan da suka shafi wallafar kamar (yawan wadanda suka kalla da masu tsokaci da wadanda suka sake yadawa) da kara nazartar asalin hotuna da amfani da manhajoji da ake iya gano asalin bidiyo da aka hada da AI.

Wani shafin Facebook na da tarin mabiya saboda yadda yake yada bidiyo da ya shafi tsaro wadanda aka hada da fasahar AI.

A ranar 7 ga watan Yuli,2026 wani shafin Facebook mai suna Emmanuel Okechukwu Aja  ya yada wani bidiyo da aka (ajiye a nan) wanda yake da’awar ‘yanfashin daji sun sanya wuta a wani gari a jihar Kaduna.Wannan bidiyo da aka yi masa take na daban, ya nuna gine-gine an sanya masu wuta, al’umma na gudu suna kauracewa muhallansu inda yace ai hari ne da aka kai a baya-bayan nan.

Ya zuwa ranar 8 ga watan Agusta,2026 wannan wallafa ta samu wadanda suka kalla 10,000 da samun masu tsokaci shida, wasu daga ciki sun nuna cewa bidiyon na gaske ne.

Evangelist Olufunke Aiyedehin tayi tsokaci da cewa “Ubangiji ka rusa duk masu kai wannan hari su lalata gari.”

Wani mai amfani da shafin, Alapotiowo Thomas, yayi tsokaci inda ya nuna shakku yana mai cewa “Mutane me yasa a ko da yaushe suna son yada abubuwa na shedanci? Yadda kake tunani a zuciya a kullum shine abin da za ka samu, akanka ba wai akan al’ummar da ke kauyenku ba.

DUBAWA ta nazarci wannan bidiyo ta hanyar amfani da Hive Detect, manhajar fasahar AI da ke gano asalin abubuwa da aka wallafa, wannan manhajar ta gano wannan bidiyo mai tsawon dakika 10 kaso 99.6% ya nuna cewa an hada shine da AI, sannan ya nunar da cewa kaso  0% a muryar an hada ta da fasahar ta AI, a sharhin manhajar ta nunar da cewa anyi amfani da fasahar ta AI ne baki daya wajen hada wannan bidiyo.

.

Yadda ake amfani da shafukan Facebook a yada bidiyo na karya da ya shafi tsaron Najeriya wadanda ake hadawa da fasahar AI

Hoto na sakamakon da aka samu daga HIVE.

Baya ga nazari na AI, DUBAWA bata samu wata kafar yada labarai ko da guda daya ba ko bangaren jami’an tsaro da mahukunta a yankin da suka ba da tabbaci na cewa an kai harin a yankin na jihar ta Kaduna a wannan lokaci da aka wallafa bidiyon.

DUBAWA ta kuma nazarci irin ayyukan da wannan shafi ke yadawa. 

Wannan shafi na da tarin mabiya sama da 69,000 ya kuma nuna cewa inda aka kirkiri shafin Asaba ne a Najeriya, kuma bayanan shafin sun nunar da cewa mai shafin ya fara amfani da Facebook a ranar 30 ga Janairu,2026.

Yadda ake amfani da shafukan Facebook a yada bidiyo na karya da ya shafi tsaron Najeriya wadanda ake hadawa da fasahar AI

Hoto da aka dauka na wannan shafi.

Ya zuwa ranar 9 ga watan Satumba, 2026 DUBAWA ta nazarci bidiyo 23 da aka wallafa a wannan shafi kuma sun nuna cewa suma bidiyo da aka wallafa an hada su ne daga AI. Akasari wadannan bidiyo suna magana ne kan lamuran da suka shafi tsaro da suka hadar da kai hari a kan al’umma da sanyawa gari wuta da sauran wasu abubuwa da ake cewa an yi sune a sassa daban-daban na Najeriya.

Jadawali 1: Wasu daga cikin bidiyo da aka hada daga AI da aka sanya su a shafin Facebook 

LambaKwanan wataLinkTakaitaccen bayani kan bidiyoYawan kallon da akai masa
1. 09/09/26https://web.facebook.com/share/r/1Sj8bedAaK/Bidiyo da ya nuna cewa an kai farmakin ‘yanfashin daji kan coci a Legas.884
2.08/09/26https://web.facebook.com/share/r/1CT2VeptUE/Da’awa cewa sojoji sun yi aikin ceto na wasu mutane a Najeriya.680
3.07/09/26https://web.facebook.com/share/r/1EyY2NrTn5/Sojojin Amurka a daji don yakar ‘yanfashin daji a Najeriya.3,600+
4.06/09/26https://web.facebook.com/share/r/14sz1mvHRa1/Sojojin Amurka sun isa Najeriya a kokari na yaki da masu fashin daji.6,000+
5.05/09/26https://web.facebook.com/share/r/19Mbycfgki/Mayaka sun kai farmaki a wani kauye a Legas.3,000+
6.04/09/26https://web.facebook.com/share/r/19UpGzm3Vd/‘Yanfashin daji sun kai farmaki a wani kauye a Legas.2,600+
7.01/09/26https://web.facebook.com/share/r/14ofU2jPTtN/‘Yanfashin daji sun kai farmaki ga matafiya a Legas2,800+
8.31/08/26https://web.facebook.com/share/r/19K8pRrYsN/‘Yanfashin daji sun kai hari wata majami’a a Legas.14,000
9.30/08/26https://web.facebook.com/share/r/1QJQZHvtxE/‘Yanfashin daji sun kai hari a wani kauye a Legas2,000+
10.25/08/26https://web.facebook.com/share/r/1Db5Gcmp5m/‘Yanfashin daji sun kai farmaki ga mazauna kauye a Najeriya.3,200+
11.24/08/26https://web.facebook.com/share/r/1CHYZRMebg/‘Yanfashin daji sun kai hari banki a Najeriya.887
12.22/08/26https://web.facebook.com/share/r/1GzuG9hUAt/‘Yanfashin daji  sun kai farmaki ga wani taron bikin aure 4,000+
13.21/08/26https://web.facebook.com/share/r/1GmuCB6bzF/‘Yanfashin daji sun kai hari a wata kotu a Najeriya 4,400+
14.18/08/26https://web.facebook.com/share/r/14hY8huTSTd/‘Yanfashin daji sun kai hari majami’a a Legas.4,600+
15.17/08/26https://web.facebook.com/share/r/1BvUHGex2h/‘Yanfashin daji sun kai hari ga matafiya a Legas4,900+
Yadda ake amfani da shafukan Facebook a yada bidiyo na karya da ya shafi tsaron Najeriya wadanda ake hadawa da fasahar AI

Hotunan wasu bidiyo da aka hada da AI aka wallafa a wannan shafi

Bincike ya gano cewa jihar Legas ake yawan fada a wannan shafi, sai dai babu wata kafar yada labarai sahihiya data goyi bayan wannan da’awa da ake yi a wadannan bidiyo.

Wannan shafi na da nasa mabiya da bin abubuwan da ake wallafawa, bidiyonta da aka fi kalla ya samu mutane sama da 257,000, wanda aka fi yadawa kuwa shine ya samu 159 da masu tsokaci 164. Abin da ke nuna cewa wadannan bidiyo da ake tsara su suna samun masu kallo da dama a shafin na Facebook.

Labaran Peterking ana hada su da AI inda ake nuna kamar jagoran ‘yanta’adda na magana.  

Wani shafin na Facebook mai suna, Peterking Stories, na amfani da fasahar AI wajen hada labaran bidiyo da ke nuna abubuwa da suka shafi tsaro, inda za a nuna kamar mutum na gaske na magana wanda a zahirin gaskiya wadannan mutane basu ce komai ba.

A ranar 26 ga watan Mayu,2026 wannan shafi ya wallafa wani bidiyo da aka hada shi da fasahar ta AI inda aka nuna shugaban ‘yanfashin daji na cika baki yana kalubalantar jami’an tsaro kan irin nasarori da ya cimma. Ya zuwa ranar 9 ga watan Agusta,2026 wannan wallafa ta samu wadanda suka nuna sha’awa 580 da masu tsokaci 45 da wadanda suka yada bidiyon 153.

Yadda ake amfani da shafukan Facebook a yada bidiyo na karya da ya shafi tsaron Najeriya wadanda ake hadawa da fasahar AI

Hoton wannan shafi

Wannan shafi an kirkire shi a ranar 6 ga watan Afrilu, 2026 kuma an nuna cewa garin  Nkwerre, na jihar Anambra anan ne aka kirkiri shafin. DUBAWA bayan nazartar wannan shafi ta lura cewa a kwai bidiyo da dama da suka shafi aikin jami’an tsaro da aka wallafa a kansa, kamar kai harin ‘yanfashin daji da taho mu gama da jami’an tsaro. 

Wannan shafi da tun da fari ana kiransa da sunan“Peterking’s World” an sauya masa suna zuwa “Peterking Stories & fact” a ranar 22 ga watan Janairu, 2024 daga baya aka sake sauya masa suna zuwa “Peterking stories”.

A cikin wadannan bidiyo da aka nazarce su sun hadar da wannan a nan da nan inda aka nuna Isiya Kwashen Garwa, danfashin daji da ake nema ruwa a jallo, a wannan bidiyo Garwa ya kalubalanci dakarun sojan saman Najeriya.

DUBAWA ta bibiyi wannan bidiyo ta gano ya samo asali ne daga wata yarjejeniyar zaman lafiya da aka kulla a Katsina kamar yadda rahoton Zagazola Makama a ranar 14 ga Satumba,2025 ya nunar. Wannan ya nunar da cewa hoton na nan watanni  kafin wannan shafi ya koma wallafa bidiyo da aka hada su da fasahar ta AI.

DUBAWA ta nazarci wannan bidiyo mai tsawon dakika 22 ta hanyar amfani da  Hive Detect. Wannan kayan aiki ya nunar da cewa asalin bidiyon shedu sun nuna da kaso  95.4% na AI ne, abin da ke nuna cewa alamu sun nuna an hada shi da fasahar AI, da nuna 0.8 na yiwuwar an sanya murya da aka hada da fasahar ta AI.

Yadda ake amfani da shafukan Facebook a yada bidiyo na karya da ya shafi tsaron Najeriya wadanda ake hadawa da fasahar AI

Hoto da aka dauka daga sakamakon na HIVE.

Wannan shafi ya dauko asalin bidiyon, sai yayi amfani da fasahar ta AI wajen hada bidiyo wanda ke nuna mutum na magana.

Yadda ake amfani da shafukan Facebook a yada bidiyo na karya da ya shafi tsaron Najeriya wadanda ake hadawa da fasahar AI

Hoto da aka dauka daga manhajar da ke nuna ko an dauki murya ne daga AI, Wannan sakamako ya tallafawa binciken DUBAWA inda ya tabbatar da cewa an hada muryar ne da AI ba wai shugaban ‘yanbindigar ne yake magana ba a zahiri.

Jadawali 2: Bidiyo na AI da aka gano daga shafin Facebook  

LambaKwanan WataLink Bayani kan abin da ya kunsaAdadin yawan kallonsa
1.20/04/2026https://www.facebook.com/share/r/1Cc9J1fn9n/Shugaban ‘yanfashin daji Isiya Kwashen Garwa  na kalubalantar sojojin sama na Najeriya 87,000+
2.19/04/2026https://www.facebook.com/share/r/1Fi1QkUBo1/Shi dai wannan shugaban ‘yanfashin dajin na kalubalantar sojan Najeriya 165,000+

Wannan jadawali ya nuna bidiyo 2 na AI na shugaban ‘yanfashin daji.

Wani shafin na Facebook mai suna, MilitaryK-9, wanda ke da mabiya sama da 94,000 ya wallafa bidiyo a ranar 18 ga watan Nuwamba,2025 da ke nuna dakarun sojan Amurka na shiga jirgin sama. 

Yadda ake amfani da shafukan Facebook a yada bidiyo na karya da ya shafi tsaron Najeriya wadanda ake hadawa da fasahar AI

Hoto na shafin a Facebook. Tushe/Facebook

Taken labarin da aka rubuta yayi da’awar cewa dakarun sun kama hanya zuwa Najeriya don ba da kariya ga mabiya addinin Kirista.  

Wannan wallafa ta samu wadanda suka kalla sama da 937,000 da masu tsokaci 1,100 da sama da mutane 1,000 da suka yada.

DUBAWA ta lura cewa a jikin bidiyo ana ganin alamar Sora da ake gani a Cartoon abin da ke nuna cewa an hada abin da fasahar AI, Mun sake nazartar wannan bidiyo mai tsawon dakika 10 ta hanyar amfani da Hive Detect, wanda ya nuna cewa kaso 99.7%  ya nuna cewa an hada bidiyon ne da fasahar AI. 

Nazartar bangaren bidiyon ya nunar da  99.9% an yi shine da AI, da aka duba batun na Sora2 shima ya nuna da kaso 99.7%.  

Yadda ake amfani da shafukan Facebook a yada bidiyo na karya da ya shafi tsaron Najeriya wadanda ake hadawa da fasahar AI

Hoton sakamako da aka samu daga HIVE.

Wannan bidiyo an wallafa shi ana tsaka da muhawara ta yiwuwar kai dakarun sojan Amurka zuwa Najeriya a ranar 1 ga Nuwamba,2025

Lokacin da shugaban kasar Amurka Donald Trump ya ba da umarni na ci gaba da shiri kan yiwuwar kai dauki a Najeriya, saboda a cewarsa ana gallazawa mabiya addinin Kirista.

Duk da haka DUBAWA ta gaza gano sheda da ke nuna cewa dakarun sojan Amurka ne ke tafiya zuwa Najeriya kamar yadda aka yi da’awa a ranar 19 ga Nuwamba,2025 , kwana guda bayan wannan wallafa gwamnatin Najeriya ta bayyana cewa kasar bata bukatar wani tallafi na dakarun soja daga ketare sai dai tallafi ta bangaren Amurka ta basu bayanan sirri da tallafi ta bangaren fasaha da hadin gwiwa da ba da kayan aiki na sojoji.

Lokacin da aka fitar da wannan wallafa ta zo a daidai lokacin da ake ci gaba da muhawara ko akwai yiwuwar sojan na Amurka za a kaisu kasar, abin da ya sanya ake ganin ko akwai alamun kanshin gaskiya a batun. An dai yi amfani da fasahar ta AI aka zambada karya aka nuna sojoji cikin kayan dakarun Amurka za a kaisu aikin da babu shi a zahiri.

Wannan shafi an kirkire shi a ranar 5 ga watan Fabrairu, 2024, wanda sunansa na asali shine Belklef Zamani Comedy, wanda daga bisani aka sauya masa suna zuwa MilitaryK-9 a ranar 14 ga Janairu,2026. An bayyana birnin Manchester na Burtaniya a matsayin inda aka kirkiri shafin, tushe kuma daga Najeriya.

Yadda ake amfani da shafukan Facebook a yada bidiyo na karya da ya shafi tsaron Najeriya wadanda ake hadawa da fasahar AI

Hoto na bayanan gaskiya a game da wannan shafi. Tushe/Facebook

Nazarin DUBAWA ya nunar da cewa abubuwan da ake nunawa an samo sune daga AI, inda ake nuna abubuwa da suka shafi lamura da suka shafi hargitsi na tsaro, abin da ya hada da fafatawa da dakarun tsaro na Najeriya da harin ‘yanbindiga da tashin bama-bamai, dama wasu abubuwa da suka shafi rikici tsakanin Isra’ila da Iran da ma Amurka, mun lura cewa abubuwan da aka wallafa a bayan nan ya nuna cewa an hada da ‘fasahar AI’.

Wasu daga cikin wadannan bidiyo sun samu masu kallo da dama inda guda daga cikinsu ya nuna an kalla sau  966,000.

Jadawali 3: Hotunan bidiyo da aka hada da fasahar AI a shafin Facebook

Lamba Kwanan Wata Link Bayani kan abin ya kunsaAdadin kallo
1.18/11/25https://www.facebook.com/share/r/1BvVoRr6RX/Dakarun sojan Amurka a hanyar kai dauki ga mabiya addinin Kirista a Najeriya937,000+
2.09/1125https://www.facebook.com/share/r/1BpDwomMWs/‘YanNajeriya na murna da zuwan dakarun Amurka966,000+

Jadawali da ke nuna bidiyo guda biyu da aka hada da AI bisa da’awar sojan Amurka a Najeriya.

Yadda ake amfani da shafukan Facebook a yada bidiyo na karya da ya shafi tsaron Najeriya wadanda ake hadawa da fasahar AI

Wasu daga cikin bidiyo da aka hada da AI kamar yadda aka watsa a fejin

DUBAWA ta gano bayyanar irin wannan a shafukan Facebook uku: Ana amfani da fasahar ta AI ko wasu bidiyo da aka yi masu dabaru don nuna halin tsaro da ake ciki da wasu kalubale na tsaro kamar a zahiri. Abubuwan da ake nuna sun hadar da harin ‘yanbindiga da ayyukan dakarun tsaro tsakanin kasa da kasa.

Duk da cewa bincike bai bayyana cewa wadannan shafuka suna aiki tare ba, amma ayyukansu ya nuna mabanbantan yadda ake amfani AI a yada labari da ya shafi tsaro ka dauka kamar da gaske.

Silas Jonathan, kwararren masani kan yadda ake gano labaran karya kuma manajan bincike na fasahar zamani a cibiyar (DAIDAC), yace bidiyon AI da suka shafi tsaro suna da tasiri ga mutane su yarda da su, duba da halin fargaba da ake ciki saboda matsalar tsaro.

Yace labaran da ke taba zuciya da aka bayyana a bidiyo ana saurin yada su kafin ma a tantance, kuma damar da ake da ita a shafukan sada zumunta suna taimakawa wajen yada irin labaran su kai wurare da dama.

“Idan ana yawan yada irin wannan, yana sauya tunanin mutane kan halin da ake ciki na tsaro, da fahimtarsu lamarin da ke kara sanyawa matsalar ta tsaro a ga ta yadu fiye ma da yadda lamarin yake a zahiri,” a cewar Silas.

Yayi gargadin cewa ci gaba da ganin irin wannan na sanyaya gwiwar al’umma su rasa karfin gwiwa da gwamnati da ‘yanjarida da masu gano gaskiyar labari kasancewar “suna yin komai na karya” sai a samu matsala mutane su shiga shakku shin menene gaskiya menene kuma karya.

Kwararren masani kan fasahar ta AI yayi gargadi kan amincewa da bidiyo da ake gani tamkar gaskiya.

Sharfadi Bature, kwararren masani kan AI, yayi gargadi ga masu amfani da shafukan sada zumunta su yi taka tsantsan kan irin bidiyon da ake yi da AI masu kama da na gaske, kasancewar sannu a hankali bidiyo da ake yi da AI a yanzu suna zama tamkar abu na zahiri da ake amincewa dasu.

Ya ba da shawara a rika tantance asalin bidiyo da inda aka yi shi da lokaci a kuma duba ko wata kafar yada labarai sahihiya ta yi amfani da shi ko jami’an tsaro ko wata kafa mai zaman kanta. 

Ya kuma ba da shawara ta duba wasu abubuwan da basa tafiya daidai kamar yadda ake motsi wanda bai kama da na halitta ba, da wata irin inuwa ko wata alama ta soja wacce ba haka ta asali take ba.

“Babban kalubalen shine kallo kadai ba zai sanya kace abu ko bidiyo na gaskiya ba ne,” a cewar Sharfadi.

Ya kara da cewa irin wadannan bidiyo da ake hadawa suna kawo shiga rudani da jawo tashin hankali da zubar da kima yayin da ci gaba da bazuwar irin wadannan bidiyo na AI ke iya sawa mutane su yi watsi bidiyo na gaske suna tunanin shima na karya ne.

Bayanansa sun kara karfafa shawarar Silas cewa a rika tantance bayanai kafin a yada su, kwararren masanin kan yadda ake gano labarai na gaskiya ya bukaci ‘yanjarida da masu aikin binciken gano gaskiyar labari su mayar da hankali kan kallo na tsanaki da harhada shedu ba kawai su dogara da manhaja da ke iya gano abin da aka kirkira da AI ba.

“Abin lura shine a tantance da’awa da abin da ake fadi akanta ba kawai abin da idanu ya gani ba,’’ a cewar Silas.

Karshe

Bincike da DUBAWA ta gudanar ya gano cewa akwai shafukan Facebook da dama da suke yada irin wannan bidiyo da ake hadawa da AI, suna rika kirkirar labarai suna dangantawa da tsaro a sassa daban-daban na Najeriya.

Ba kawai ma batun yada labaran na karya ba, bincike ya gano yadda ake amfani da wasu kafafen yada labaran na zamani a yaudari al’umma kan abin da ya shafi tsaro da ma jan hankali na masu tsokaci a shafukan na sada zumunta.

 “An gudanar da wannan aiki karkashin Cibiyar koyon Aikin Jarida da Kirkire-kirkire da Ci-gaba (CJID) bisa daukar nauyin Kungiyar Tarayyar Turai.”