|
Getting your Trinity Audio player ready...
|
Da’awa: Masu amfani da shafin Facebook sun wallafa bidiyon da ke da’awar wai ‘yan bindiga ne ke wa wata matar da suka sata fyade.

Hukunci: Yaudara ce. DUBAWA ta gano cewa bidiyon tsoho ne. Akwai kuma hujjojin da suka tabbatar cewa bidiyon tun Disemban 20202 ya ke kan shafukan sada zumunta.
Cikakken bayani
Wani infuluwensa a soshiyal mediya, Aminu Abdullahi, ya wallafa wani bidiyo a shafin Facebook ya na nuna wata matar da wasu masu dammarar bindigogi ke wa fyade. Infuluwensan ya kuma kara da cewa lamarin na nuna wani yanayi na yadda tashin hankalin ke cigaba da sauyawa ya kuma yi kira ga kungiyoyin kasa da kasa da su sa baki.
Da’awar (wanda za ku iya gani a nan) mutane sama da 303,000 sun yi ma’amla da shiwasu 1,600 sun yi tsokaci sa’annan wasu 1,600 su ma sun sake rabawa akalla ranar 20 ga watan Yunin 2026 sadda muka duba labarin.
Bidiyon ya yadu sosai cikin shafin Facebook kuma a duk sadda aka sa shi sai a hada da taken da ke nuna kamar kwanan nan ne abun ya faru.
Wannan da’awar dai ya janyo ra’ayoyi mabanbanta daga masu amfani da soshiyal mediya.
Wani mai amfani da shafin, Bello Ado ya yi tambaya ne dangane da martanin jagororin siyasa da masu ruwa da tsaki a harkokin tsaron jihohin Zamfara, Sokoto da Katsina, inda ya ce mahukuntan sun yi watsi da yankunan da abun ya shafa bacin yawan mutane masu karfin fada a jin da suke da su a gwamnatin kasar.
“TBai kamata a rika yada wannan labarin ba,” wani mai amfani da shafin, Zainulabidina Shehu, ya bayyana.
Haka nan kuma, wani shafin Facebook mai suna Hausaland Magazine ya wallafa wani hoto na wannan bidiyon ya na da’awar cewa wata mata ce mai shekaru 56 na haihuwa wadda ‘yan bindiga Filani ke wa fyade a karamar hukumar Sabon Birni da ke jihar Sokoto, a gaban ‘ya’yanta guda biyu.
Ganin yadda bidiyon ya yadu tare da da’awowi daban-daban ne ya sa DUBAWA tantance gaskiyar lamarin.
Tantancewa
Domin gane sahihancin bidiyon da ma sadda aka fara dauka, DUBAWA ta bi diddigin tarihin bidiyon a duniyar gizo.
Mun fara amfani da fasahar reverse image search wanda ke tantance hotuna, inda a nan ne muka gano sigogi daban-daban na bidiyon.
Mun gano wani da aka wallafa a shafin Nairaland wanda wani mai sunaagboifeanyi242 ya wallafa ranar 17 ga watan Disemban 2020.
Da muka cigaba da binciken mun gano cewa Nairaland ya yi amfani da wani labarin ne shi ma wanda aka wallafa ranar 16 ga watan Disemban 2020 wanda aka wallafa a wani shafi shi kuma mai suna Gist Lobby, inda a nan ma aka yi amfani da bidiyon da aka yi ta yadawa.
DUBAWA ta sake gudanar da bincike na mahimman kalmomi dan gano ko bidiyon na da wata alaka da abin da ya faru a jihar Sokoto ko ma dai wani yanki a Najeriya, amma bamu sami wani labari mai sahihanci da ke da alaka da wannan lamarin da ya afku a 2026 ba.
Duk da cewa ba’a kai ga gano ko ma fayyace ainihin yadda aka kai ga samun wannan bidiyon ba, sigogin farkon da aka gano sun tabbatar mana cewa wanann bidiyon wanda ake rabawa tsoho ne.
A Karshe
Da’awar da ake yawo da shi ana cewa ‘yan bindiga ne ke wa wata matar da aka sace fyade yaudara ce. Mun bi diddigin bidiyon mun gano cewa tsoho ne kuma tun shekarar 2020 ya bayyana a yanar gizo..
Wannan aiki an aiwatar da shi karkashin Cibiyar koyon Aikin Jarida da Kirkire-kirkire da Ci gaba (CJID) tare da tallafin Kungiyar Tarayyar Turai.
