Getting your Trinity Audio player ready...
|
Da’awa: Wani faifan bidiyo da aka yada a shafin WhatsApp ya nuna wani malamin Islama da ake zargin yana hukunta dalibai biyu da bulalar icce ne kamar yadda shari’ar musulunci ta tanada.

Hukunci: Yaudara ne. Binciken DUBAWA ya gano cewa wani mazaunin Maiduguri ne ke dukan ‘yan matan dalibai, saboda sun shiga harabar gidansu domin ciro mangwaro. Mutumin ba malamin islamiyya ba ne kuma ba shi da alaka da wata makarantar islamiyya.
Cikakken Bayani
Wani faifan bidiyo mai tayar da hankali da ke nuna wani mutum da ake zargin malamin addinin Islama ne yana dukan dalibai biyu bisa hukuncin shari’a ya rika yawo a kafar sadarwa ta WhatsApp, lamarin da ya janyo bacin rai da nuna damuwa daga al’umma.
Bidiyon mai tsawon minti 1 da dakika 30 ya yadu a Facebook (nan da nan) da kuma shafin X. Da yawan mutane sun nuna kaduwa da kyamar yadda malamin ke cin zarafi yaran da ake zarginsa da aikatawa yayin da suke neman a yi wa yaran da abin ya shafa adalci.
“Wannan makarantar Islamiyyah ce a Maiduguri, Arewacin Najeriya (Ile keu), wannan malamin yana amfani da dokar Shari’a a nan, iyaye ba za su iya yin komai a nan.” Bayanin da aka rika yadawa a shafin Facebook tare da bidiyon.
Wasu masu amfani da shafukan sada zumunta a X sun soki lamarin tare da yin Allah wadai da wanda ake zargin malamin addinin Islama ne.
“Yaran da suka taso kamar haka za su girma su zama ‘yan ta’adda saboda za su yi tunanin abin ba komai ba ne,” in ji @jadumzee.
“Musulunci abin kyama ne,” @ifezy007 ya rubuta.
Yaduwar wannan da’awar da kuma bacin ran da ya haifar ya sa DUBAWA ta yi bincike kan bidiyon don tabbatar da gaskiyarsa.
Tantancewa
DUBAWA ta sanya bidiyon a cikin manhajar tantance bidiyo ta InVid don fitar da hotunan faifan bidiyon, sannan ta bincika wani ɓangaren bidiyon ta hanyar amfani da shafin nema na Google Reverse Image Search.
Sakamakon hotun da muka zakulo
Sakamakon binciken ya kai mu ga irin wannan bidiyon da aka yada sau da yawa a shafukan sada zumunta a cikin watan Maris 2025.
Rahotanni sun tabbatar da cewa lamarin ya faru ne a unguwar Pompomari da ke Maiduguri babban birnin jihar Borno.
Sai dai kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito, ‘yan matan biyu Hauwa da Hajara Goni suna kan hanyar makaranta ne a lokacin da suka yanke shawarar diban mangwaro a wani gida mallakin wani Muhammed Shettima. Sun ce sun nemi izini daga wani yaro a gidan kuma ba su jima ba kawai sai Muhammad ya ci karo da su.
Ya yi barazanar fille kan ‘yan matan, amma matarsa ta roke shi ya kyale su, ta mika masa sanda domin ya yi musu bulala.
“Ya kulle kofa, ya fito da wata yanka, ya yi barazanar kashe mu, amma matarsa ta hana shi, ta kawo masa wasu sanduna,” kamar yadda suka shaida wa Daily Trust.
Jaridar ta ruwaito cewa daga baya Muhammed ya bude kofar, amma da matarsa ta ga daya daga cikin ‘yan matan ta yi fitsari a wando, sai ta ce wa mijinta ya kara yi musu bulala wanda hakan ya sa daya daga cikinsu ta suma. Wani direban a daidaita sahu wanda ya san dan uwan yaran ya taimaka ya kai su gida saboda tausayi.
Punch da Vanguard suma sun ruwaito irin wannan labari.
Rundunar ‘yan sandan jihar Borno ta kuma fitar da bayanai game da wannan lamari a ranar 22 ga Maris, 2025.
Sanarwar da ta yi wa taken “KARIN BAYANI: An kama Ma’aurata kan Bidiyon Cin zarafin Yara a Maiduguri.”
A Karshe
Wannan da’awar Yaudara ce. Duk da cewa faifan bidiyon na gaskiya ne, kuma lamarin ya faru a Maiduguri, amma wasu ma’aurata ne suka lakada wa wasu ‘yan matan biyu duka saboda debo mangwaro a harabar gidansu, ba wai malamin islamiyya ba.