African LanguagesHausa

Yarjejeniyar Maputo da dalilin da ya sa ‘yan Najeriya ke son aiwatar da ita 

Getting your Trinity Audio player ready...

A watan Yuli, 2003, Kungiyar Tarayyar Afurka(AU), kungiyar kasa da kasa da Najeriya ke zama mamba a cikinta ta amince da yarjejeniyar ta  Maputo Protocol a lokacin taron koli na Mozambique.

Yarjejeniyar an tsara ta ne da nufin samar da mafita kan kalubale da ke addabar mata a nahiyar Afurka, ciki kuwa har da cin zarafin mata saboda jinsinsu, tana ba da kariya ga hakkin matan da rayuwarsu da mutuncinsu.

Kamar yadda aka kwafo daga shafin Equality Now,; Yarjejeniyar ta Maputo tana da alfanu ga mata ‘yan Najeriya saboda tarin dalilai kamar : 

  1. Ya sanya kasashe su dauki hukunci a hukumance kan wasu laifuka da ke da jibi da nuna banbanci ga mata da duk wani abu da ke da alaka da nuna wa matan da yara mata banbanci.
  2. Wayar da kan mutane kan kare hakkin mata da kananan yara mata, an dora wa hukumomi nauyin kare hakkinsu daga duk wani nau’in cin zarafi da hana duk wani nau’i na ci da gumunsu, da wulakantar da su.
  3. Ba da tabbaci na kare hakkin mata da kananan yara mata , mutuncinsu da tsaronsu, ta haramta wasu hukumomi ci da gumunsu da nuna rashin imani da yi masu hukunci na rashin imani da wulakantarwa.

A ranar 19 ga watan Satumba, 2023, Najeriya kamar sauran kasashe 48 daga 55 (48 other countries out of 55,) da suka rattaba hannu kan yarjejeniyar da za ta ba su damar mutunta samar da daidaito tsakanin jinsi da kawo karshen duk wani nau’i na nuna wa mata banbanci.

A cikin hakkoki da suka rataya a wuyan jaridar ta DUBAWA kan aikin samar da ilimi da ya shafi Aikin Jarida (Media and Information Literacy (MIL). Mun rubuta wannan makala don ganin tasirin sauyin jinsi a Najeriya.

Babu wani abin azo a gani

Abin lura shine wannan ba shine karon farko ba da Najeriya ke shiga wata yarjejeniya da ta shafi daidaiton jinsi. Kasar ta fitar da tsare-tsare da dama national gender policies, wata gagarumar nasara ita ce amincewa da dokar kare hakkin mutane  ta Violence Against Persons Prohibition (VAPP) Act

Shekaru 22 daga bisani kuma kasar da ke zama kan gaba a mulkin dimukuradiyya a Afurka ta gaza (failed) wajen aiwatar da cikakkiya wannan yarjejeniya ta Moputo  a cikin gidanta, abin da ya sanya masana ke ganin rashin aiwatarwar ya sanya har kawo yanzu mata na ci gaba da fuskantar nuna kyama da cin zarafi a cikin al’umma. 

Duba da abin da ya faru a baya-bayan nan na zargin cin zarafi ta hanyar lalata (sexual harassment allegations) da Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan ta zargi shugaban majalisar dattawa  Godswill Akpabio, har ta kai ga dakatar da ita a majalisa  (suspension,)  irin wannan yunkuri ya sake nunawa karara yadda Najeriya ta gaza wajen ba da kariya ga al’umma kan abin da ya shafi cin zarafi da ya shafi jinsi.

Cin zarafi ta hanyar lalata abu ne da ke bazuwa kuma ke shafar al’umma a duk mataki na rayuwa da inda mutum ya fito ko aikinsa a Najeriya. A wata kididdiga da aka yi a 2019 (survey,) kaso 60 cikin dari na mata a Najeriya sun fuskanci wani nau’i na cin zarafi ta hanyar lalata.

Yadda dokokin da suka takaita a kan takarda a Najeriya ke kawo rauni a fafutukar yaki da cin zarafin mata ta hanyar lalata 

Duk da cewa an gabatar da wannan doka ne don kare mata, wasu abubuwan da suka shafi shari;a  ba a yinsu yadda ya kamata ko aiwatar da su. Yayin da aiwatar da wannan doka ke da rauni  remains weak, akwai kuma dalilai na al’ada da ke sanyawa wadanda aka ci zarafinsu basa iya neman hakkinsu.

 A kwai kuma wasu tarin tsare-tsare (provisions) a kotunan gargajiya da kotunan addinin Islama wadanda ke cin karo da dokokin da gwamnatin Tarayya ke fito da su.

Da take tsokaci a kan batun  Salami Zainab, mai sharhi kan bayanai a gidauniyar DOHS Foundation, da ke aikin bincike kan lamuran da suka shafi mata a Legas ta bayyana cewa ana samun gibi ne a tsare-tsaren  da rashin son aiwatarwa daga bangaren ‘yansiyasa cikin abubuwan da ke nakasu ga kokarin aiwatar da yarjejeniyar.

“Duk da cewa Najeriya ta aminta da wannan yarjejeniya, babu bin diddigi daga bangaren ‘yansiyasa don tabbatar da aiwatarwa da yarjejeniyar da ta shafi jinsi, “Yansiyasa sun fi mayar da hankali kan wasu abubuwa da suka shafi siyasarsu sabanin hakkoki da suka shafi jinsin mata.” kamar yadda ta fada wa DUBAWA.

Kamar  Zainab, Ifeoluwa Olayiwola, lauya da ke zaune a Legas ra’ayinsu ya zo iri daya “Tsarin shari’a da muke da shi yana da rauni ga dokoki masu cin karo da juna musamman a arewacin Najeriya inda ake da kotunan shari’a dana gargajiya wadanda a wasu lokutan ke cin karo da yarjejeniyar ta Moputo..”

Lauyar ta kara da cewa rashin aiwatar da yarjejeniyar ta Moputo ita ce ta jawo har Mista Akpabio ke karantsaye ga tsarin shari’ar ‘nemo judex in causa sua’ ma’ana ‘mutum ya zama alkali a shari;ar da ake masa.’ 

“Bara mu duba batun na ‘nemo judex in causa sua’ a shari’ar ta Natasha vs Akpabio. A wannan tsari bai kamata ace shi Akpabio shine alkali a shari’arsa ba, Ina ji cewa Sanata Natasha an take mata hakki anan.” A cewar lauyar.  

Ta kara da cewa  “Har sai an aiwatar da yarjejeniyar cikakkiya sannan za a rika samun adalci kan abin da ya shafi batutuwan da suka shafi cin zarafin mata dalilin lalata.”

Dukkaninsu dai sun jaddada bukatar da ke akwai ta ganin an aiwatar da wannan yarjejeniya ta Moputo a cikin gida Najeriya muddin ana so a cimma nasara a yakin da ake da cin zarafin mata a wuraren aiki.

A Karshe

Duk da cewa Najeriya ta karbi wasu tsare-tsare da suka shafi ba da kariya ga mata kan sha’anin lalata, rashin aiwatarwa na ci gaba da ba da damar aza ayar tambaya . Wannan kuma na kara sanyawa mata su ci gaba da fuskantar cin zarafi saboda masu aikata laifin ba a hukunta su yadda ya kamata. 

Show More

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
Translate »