|
Getting your Trinity Audio player ready...
|
Da’awa: Mai amfani da shafin X (@OjiUgo_nwa) ya wallafa wani bidiyo ya na da’awar wai mutanen da ke cikin bidiyon mambobin wata kungiyar ‘yan ta’adda da ke da alhakin yin garkuwa da mutane, fyade da wasu miyagun ayyuka ne a Najeriya.

Hukunci: Karya ce. Binciken da muka yi ya tabbatar mana cewa wata kungiya a Somaliya ce da aka yi rahotonta a shafin Calamda.net, kuma babu wata hujjar cewa ta na da alaka da ayyukan ta’addanci a Najeriya.
Cikakken bayani
Ranar lahadi 7 ga watan yunin 2026, mai amfani da shafin X OjiUgo (@OjiUgo_nwa), ya wallafa wani bidiyo (wanda aka adana a nan), ya na da’awar wai mazan da aka nuna a cikin bidiyon ‘yan wata kungiyar ‘yan ta’adda ne wadanda ke garkuwa da jama’a, fyade da karbar kudin fansa daga wajen wadanda suka kama. Mai amfani da shafin ya kuma hada da zargin cewa kungiyar a bayyane ta ke watsa harkokin ta’addacin da ta ke yi kai tsaye,har ma ta hada da bayar da kyaututtuka amma har yanzu ba ta gamu da hukuncin gwamnati ba.
Bidiyon ya nuna wadanda ke layin farko sanye da kayan sojoji yayin da sauran su kuma suke sanye da tufafi irin na yau da kullun. Haka nan kuma duk su na zaune ne a kasa rike da bindigogi, suna maimaita kalaman da kwamandansu ke bayarwa kamar dai masu karbar karatu. Kadan daga cikin su sun tsaya a gaban kyamara yayin da wata mata ke daukarsu hoto.
Daga 10 ga watan Yunin 2026 mutane sama da 7,004 sun yi ma’amala da bidiyon, an sake rabawa sau 155, ya sami alamar like 107, mutane 33 sun mayar da martani wasu 18 sun adana shafin.
Wannan da’awar ya janyo martanoni masu tsauri daga masu amfani da shafin wadanda suka yi Allah wadan irin wannan aikin.
“Omo, wannan tamkar dabbanci ne, gaskiya. Za su fille kan jama’a, suyi garkuwa da sojoji da kwamandojinsu/hatta janar, amma duk da haka mayakan saman Najeriya ba su taba gano inda suke buya sun hallaka su ba. Allah wadaran rundunar sojojin Najeriya. Su na nan suna mutuwa, su kuma jagororin kasar sun mayar da harkar ta’addancin siyasa,” in ji mai amfani da shafin X Jossy (@joejossy_76).
Wani shi ma mai amfani da shafin, Kamalu Onyioha Onyioha (@kamaluO42115) ya yi tsokaci kamar haka, “Yanzu da jihadi ke gangarowa yankin Kudu, ya kamata mu rika daukar matakan da za su inganta mana zaman lafiya a yankunan Najeriya musamman a yankin kudu maso gabashin kasar, kafin gonakinmu, matanmu, ‘ya’yanmu, mazanmu da al’ummominmu su kasance cikin irin wannan kididdigan.”
Wannan da’awar dai ta dauki hankali sosai a shafukan X, Instagram da Facebook, kamar yadda za ku iya gani a nan, nan da nan.
Ganin yadda wannan batun ke da sarkakiya musamman a yanayin rashin tsaron da Najeriya ke fuskanta, DUBAWA ta yanke shawarar tantance wannan bidiyon.
Tantancewa
Kamar ko yaushe mun yi amfani da manhajar tantance sahihancin hotunan bidiyo na InVID. Mun dauki mahimman hotuna su ma sun tantance su cikin googe reverse image search. Bincikenmu ya kai mu ga wani bidiyon da wata kungiyar Somaliya ta wallafa a tasharta na YouTube HMC Somali TV, tare da taken: “Dowladda oo Soo Bandhigtay Ciidamadii la wareegi lahaa Baydhabo,” wanda da aka fassara ya ke nufin “Gwamnati ta gabatar da dakarun da za su karbi aiki a Baidoa.”
Haka nan kuma, mun gano wani labari dangane da batun a shafin Calamda.net da kwanan watan 24 ga watan Maris, 2026.
Taken da aka yi wa labarin a harshen da suke amfani da shi a Somaliya ya yi bayani kamar haka: “Gurguurte Iyo Kooxdiisa Oo Lagu Eedeeyey In Dagaal Sokeeye Ka Hurinayaan Deegaannada ‘Koonfur Galbeed.” Mun yi amfani da Google Translate, wajen fassarawa kuma ya na nufin “Ana zargin Wata kungiyar masu tayar da kayar baya da asasa yakin basasa a yankunan da ke kudu maso yammacin kasar.”
Rahoton ya yi bayani sosai dangane da matsalolin tsaro da na siyasa a Somaliya, har da wani zargin da mahukuntan yankin kudu maso yammacin kasar suka yi wa gwmanatin tarayya na tura mayakan sa kai. Wannan rahoton bai yi magana a kan Najeriya ba kuma bai yi zargin ayyukan ta’addanci kamar yadda @OjiUgo_nwa ya yi da’awa ba.
Yankin Kudu maso yammacin Somaliya ya dade ya na fama da rikici da kungiyar Al-Shabaab. Yankin kan kasance sansanin atisayen sojoji da yawa, a nan ne ake gudanar da horaswa, da ayyuka, da harkokin wanzar da zaman lafiya na kasa da kasa, wadanda suka hada har da African Union Mission in Somalia wato tawagar wanzar da zaman lafiya ta Kungiyar Tarayyar Afirka. A lokuta da dama mun kula cewa ana yawan amfani da bidyoyin da suka fito yankin kudu maso yammacin Somaliyar wajen yada labaran karya a yanar gizo-gizo.
A Karshe
Mun bi diddigin bidiyon mun gano cewa wata kafar yada labaran Somaliya ce ta fara wallafa shi ranar 24 ga watan Maris na 2026, sadda ta ke bayani kan harkokin masu tayar da kayar baya da tashe-tashen hankula dangane da siyasa a yankin Kudu maso Yammacin Somaliya. Dan haka wannan da’awar ba gaskiya ba ne.
Wannan aiki an aiwatar da shi karkashin Cibiyar koyon Aikin Jarida da Kirkire-kirkire da Ci gaba (CJID) tare da tallafin Kungiyar Tarayyar Turai.
