African LanguagesHausa

Bincike ya bayyana alfanun bai wa tsuntsaya gawayi su ci

Getting your Trinity Audio player ready...

Da’awa: Wani mai amfani da Facebook ya bukaci manoma su rika bai wa tsuntsayensu gawayi lokaci zuwa lokaci saboda alfannun da ke tattare da yin hakan.

<strong>Bincike ya bayyana alfanun bai wa tsuntsaya gawayi su ci</strong>

Sakamakon binciken: Wani bangare ne kadai gaskiya! Bincike ya nuna cewa tsuntsayen da aka bai wa gawayi sukan girma sosai kuma sun fi lafiya. To sai dai kwararru na bayar da shawarar cewa a tuntubi likita kafin a bai wa tsuntsayen gawayin.

Ciakken bayani

Bisa la’akari da tarihi, irin gawayin da ake samu daga itace ne ake amfani da shi a matsayin tokar bindiga, kuma ma yana zaman irin sinadarin da ake amgani da shi wajen kona karafa. A wasu sassan duniya inda ba su da albarkarun mai, an sauya kananan motoci da motoci kirar bus ta yadda za su iya amfani da gawayi ko icce ko kuma icce a matsayin janareta.

Historically, wood charcoal was used as a constituent of gunpowder and as a reducing agent in the extraction of metals. In parts of the world where petroleum was scarce, automobiles and buses were converted to burn wood gas, obtained by burning charcoal or wood in a wood gas generator.

Ilimin Makamashi na kwatanta yadda ake samun gawayi bayan an kona abubuwa kamar itace da sauran abubuwan da ake iya amfani da su a matsayin makamashi a muhalli zuwa sinadarin da ake kira carbon da sauran sinadarai ta hanyar hura musu wuta.

Baiwa tsuntsaye gawayi abu ne da aka dade ana tabka mahawara a kai tsakanin masoya tsuntsaye da kwararru. Duk da haka, Michael Temmy wanda ke zaman mamba na kungiyar manoman kaji a Najeriya, ya yi imanin cewa hakan na da alfanu da yawa ga kiwon lafiyarsu.

A labarin da ya wallafa, ya sanar cewa manoma su yi kokari su bai wa tsuntsayen gawayi daga lokaci zuwa lokaci. Da jin haka kuma, masu tsokaci dangane da batun sai suka fara tambayarsa ko zai bayyana masu irin alfanun da yin hakan ke da shi.

Adeola Abiodun tambaya ya yi, “Wadanne alfanu ke nan, idan ka yarda?”

Wani shi ma mai amfani da shafin, Afam Chibuzo, wanda bai gamsu da bayanin ba cewa ya yi, “na zaci cewa kun ce duk abun da mutun ba zai iya ci ba kada ya ba su.”

Labarin ya sami alamar like 1,300, da tsokaci 821 kuma mutane 36 sun sake yada labarin a ranar 6 ga watan Fabrairu kadai.

Tantacewa

Gawayi na iya taimakawa wajen tabbatar da lafiyar ciki musamman wajen nika abinci sadda ya ke wucewa cikin hanji. Ya na kuma taimakawa wajen cire abubuwan da ke da guba, ya rage kaifi ko gafin abinci, ya kuma daidaita irin sinadaran da ciki ke bukata, kuma mai yiwuwa ma yana taimakawa wajen yaki da kwayoyin cutar da ake samu a ciki. Duk wadannan alfanun ka iya taimakwa kajin ku su sami irin sinadaran da yske bukata wanda zai kasance mu su garkuwa daga cututtuka. Tabbatar da lafiyar cikin kaji shi ne mabudin samun kaji lafiyayyu.

Sakamakon wani binciken ResearchGate, wanda aka yi da kajin turawa, masu nau’in da ake kira 800 Cobb 500 broiler chickens.  

An dauki kajin kwana daya mace da na miji ba tare da bin wani mizanin zabe ba aka sanya su cikin rukunnai daban-daban na irin abincin da za’a rika ba su, kowannensu da tsuntsaye 100. Daga nan sai aka kula da su na tsawon makwanni shida aka ba su irin abincin da aka saba baiwa kaji. Rukunin farko an cigaba da ba su abincin kajin kamar yadda aka saba, yayin da a rukuni na biyun sai aka rika garwaya abincinsu da gawayi dan kadan, kimanin kashi 0.3 cikin 100.

Tun ana wurin nika abincin ake sanya gawayin. Daga nan ne aka gano cewa kajin da suka ci abincin da aka garwaya da gawayi sun fi lafiya. Bayan makwanni shiddan, kajin da suka ci gawayin sun fi nauyi da ma kiba, hasali ma sun karu da kashi 3.5 cikin 100 yayin da wadanda ba su ci gawayin ba suka karu da kashi 2.0 cikin 100 kadai.

Wannan binciken ya nuna cewa wadanda suka ci gawayin sun ci wadanda ba su ci ba girma.

Gawayi, musamman wanda aka inganta an san shi da iya janye guba da sauran gurbatattun abubuwa daga cikin hanji, abin da kan rage hadarin samun lahani daga gubar da ke cikin abinci ko kuma ma irin abincin da ya riga ya lalace.

Wani biciken kuma shi ne wanda aka yi a wani wurin kiwon kaji da ke karkashin sashen kula da dabbobi na Jami’ar Mosul. Wannan binciken ya dauki kwanaki 42, daga 13 ga watan Nuwamban 2021 zuwa 24 ga watan Disemban 2021.

Kajin da aka yi kawan daya da kyankyashewa an barsu a tare daga farko, amma a mako na biyu sai aka  raba su zuwa rukunnai hudu.

 A nan an lura cewa wadanda aka rika hada musu abincinsu da toka sun fi cin abincin da wajen kashi 7 cikin 100 idan aka kwatanta da wadanda ba’a sa musu gawayin ba.

Mun yi magana da Ms Felicia, likitar dabbobi tare da Vetland, kuma ta yi mana bayani dangane da amfani da gawayi a abinci tsuntsaye.

Ta ce yawanci akan yi amfani da agawayi a abincin tsuntsaye dan ya janye abubuwa masu guba ne daga cikinsu, akan yi amfani da shi a warkar da su daga lahanin da suka samu daga guba.

Ta kuma kara da cewa, tsuntsayen da akan killace sun fi bukatar gawayin saboda sinadarin ammoniar da ake samu daga kulle sun da ake yi na iya hana su numfashi da kyau ya kuma shafi huhunsu. Bacin haka, idan har aka rage karfin sinadarin ammoniar yana iya inganta takin da ake samu daga kashin kajin. Gawayin kan taimaka wajen daidaita kwayoyin da ke cikin takin.

Daga nan ta bayar da shawarar cewa ya kamata manoma su yi magana da likita da kyau kafin su dauki wannan matakin domin idan ya yi aiki da kyau a gonar wani ba lallai ne ya yi aiki a gonar wani ba.

DUBAWA ta kuma tuntubi Bimbo Dayo, ita ma likitar dabbobi wadda ta ce gawayi ba abinci ba ne. Ta ce gawayi na iya kara musu girman jiki ya kuma cire guba daga cikinsu idan har abu ne da suke fama da shi.

“Dan haka duk da cewa yana iya cire guba da kuma gyara abinci, tambayar ita ce shin dan adam na iya cin wannan a matsayin abinci? Har ila yau, wani irin tasiri wannan zai yi a jikin tsuntsayen nan gaba, ko kuma ma a kan dabbobin da suka ci sy? Wadannan nan irin gibin da muke da shi a binciken.”

A karshe dai, daukar lafiyar tsuntsayen da mahimmanci ta hanyar ganawa da kwararru a kan tsuntsaye da dan daukar matakan da suka dace dangane da abincin su ne kadai mafita.

A Karshe

Bai wa tsuntsaye gawayi abu ne da ake cigaba da mahawara a kai a al’ummar kwararrun da ke fannin kula da tsuntsaye, inda akwai wadanda suke kira da a rika amfani da gawayin saboda alfanun da ya ke da shi a kiwon lafiyarsu. Bincike ya nuna cewa tsuntsayen da suka ci abincinsu da gawayi sun fi wadanda ba su yi amfani da gawayin ba lafiya.

Show More

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button