African LanguagesHausa

Da gaske ne albasar da aka yanka aka rage na da lahani ga dan adam?

Zargi: Wani mai amfani da shafin facebook na zargin wai bayan an yanka albasa, wanda aka rage aka ajiye na iya shan kwayoyin cutar da ke muhallin da yake wanda zai iya yin lahani ga dan adam idan aka yi amfani da shi a abinci.

Wani mai amfani da shafin Facebook mai suna Kunle Alade ya yi zargin cewa yankakken albasa na shan kwayoyin cuta abin da ya sa ke nan ake amfani da shi wajen kariya daga kamuwa da mura. A labarin, Mr Alade ya yi zargin cewa wani likita wanda ba’a sunan shi ba, ya gano hakan lokacin annobar murar da aka yi a shekarar 1919.

“Albasa na zukan kwayoyin cuta shi ya sa ya ke kare mu daga kamuwa da mura,” a cewar wani bangare na labarin.

Bayan haka kuma labarin ya sake bayar da shawarar cewa a guji cin albas an da aka yanka aka bari ya yi kwanaki a waje domin idan aka yi amfani da irin wannan albasar tamkar an ci guba ne.

Tantancewa

Da farko mun duba yanayi albasa da irin sinadaran da ya ke dauke da su. Daga nan kuma muka yi binciken mahimman kalmomi inda mu ka gano cewa albasar wadda sunanta ake kira onions da turance ko kuma da sunanta na kimiya wato allium cepa kayan lambu ne mai siffar kwan fitila wanda ake shukawa a karkashin kasa. Akwai albasar iri-iri kuma ana yi banbanta su a girma, siffa, launi da dandano. Wadanda aka fi amfani da su sun hada da mai launin Ja, mai ruwan-kwai da fari.

Binciken mahimman kalmomin sun kai mu ga wani nazarin da Ofishin Kimiyya da Al’umma na McGill ya yi, wanda ya nuna mana cewa ba ruwan albasa da kwayoyin cuta kuma ba su ma shan kwayoyin cutar domin suna dauke da irin sinadaran sulfur da ke hana hana kwayoyin cuta rayuwa a jikin albasar.

Wannan rahoton na McGill ya kuma kara da cewa albasar da aka yanka aka ajiye ba ta da wani dafi sai dai idan an yanka a kan wurin da ke da dafi ko kuma an taba ta ba tare da an wanke hannuwa ba. Ko da shi ke ana iya hana hakan faruwa ta daukar dabi’u irinsu wanke hannu, kayayyakin girki, goge wuraren girki da kuma amfani da man wanke hannu mai kasha kwayoyin cuta kafin a fara girki domin tabbatar da kariya daga kwayoyin cuta.

Wannan dabi’a ba alabasa kadai ya shafa ba, ya shafi duk wani kayan abinci.

Rahoton ya kuma bayyana cewa albasar na iya yin hunhuna, saboda kwayoyin da ke janyo hunhuna na yawo a iska.

Wani rahoton a shafin cookinglight shi ma ya musunta zargin wai yankakken albasar da aka bari a waje na da guba.

Mun sake samo wani rahoton da Kungiyar Masu Noman Albasa (National Onion Association NOA) su ka wallafa inda su ma suka karyata labarai da dama dangane da albasa a ciki har da wanda ke zargin cewa idan an yanka albasa an ajiye ta kan zama guba. Kungiyar ta ce idan har aka dauki matakan da suka dace, yankakken albasa ba shi da guba, ana iya ajiye wanda aka yanka a cikin fridge ko kum a roba ko kwano mai murfi na tsayon kwanaki 7 kuma ba abin da zai same shi.

Wani labarin da aka wallafa a shafin verywellhealth.com shi ma ya ce babu wata hujjar cewa albasa na kare mutane daga kamuwa da mura ko zazzabi. Ya kuma bayyana cewa ajiye albasa a daki sadda mutun ke fama da mura ko zazzabi abu ne da ya dade hasali ma tun shekarun 1500, a cewar NOA.

Binciken mu ya kuma kai mu ga ganin wadansu karin binciken da aka riga aka yi dangane da batun a jaridun USA Today, Snopes, Wall Street Journal da Kamfanin Dillancin Labarun Associated Press inda suka fayyace cewa ajiye albasa a gida ba zai kare cututtuka ba domin albasar ba ta iya zukan kwayoyin cuta kamar yadda aka zata.

A Karshe

Binciken mu ya nuna mana cewa albasata ba za ta iya shan kwayoyin cut aba. Dan haka sa albasa a cikin gida ba zai kare mutun daga kamuwa da mura ko zazzabi ba. Harin da garkuwan ke kai wa kan kwayoyin cutar da ke kokarin shiga jikin mutun ne ke taya shi warkewa daga cututtuka. Ba gaskiya ne ba wai albasa kan zama dafi idan an ajiye domin ana iya ajiye wa a fridge ko a rufe a kwano ko roba har na tsawon kwanaki 7. Dan haka wanann zargin karya ne.

Show More

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
Translate »