Zargi: Wani mai amfani da shafin Facebook na zargi wai hotunan bidiyon da ke zargin an gano wadansu mahara a maboyarsu a Najeriya ne.
Da abubuwan da suka faru kwanan nan kamar harin da aka kai kan jirgin kasan da ya taso daga Abuja za shi Kaduna, da kuma yunkurin harin da aka kai kan tashar jirgin saman Kaduna, matsalar tsaro ta cigaba da kasancewa kan gaba al’amuran da suka shafi ‘yan Najeriya.
Ranar talata 5 ga watan Maris wani mamban jam’iyya mai mulki ta APD, Joe Igbokwe ya wallafa wani bidiyo. Ya hada bidiyon da wani tsokacin da ke zargin wai maharani Najeriya ne wadanda suka yi kaurin suna wajen kisa da garkuwa da mutanen da ba su ji ba su gani ba.
“Wannan bidiyon da aka dauka da kyamaran drone ne na maharan da ke sata da garkuwa da ‘yan Najeriya. Bidiyon ya nuna su a wata maboyarsu a wani dajin da ba’a tantance ba,” wani bangaren tsokacin ya bayyana.
Sadda aka wallafa wannan binciken, har an rana labarin sau 1,000 a yayin da wasu mutane 31 kuma tofa albarkacin bakinsu dangane da batun a karkashin labarin.
Mun kuma gano cewa ana cigaba da sake raba bidiyon a wahtsapp tare da bayanai mabanbanta dangane da wurin da maharani su ke.
Tantancewa
Mun fara da duba bidiyon mu gani ko za mu gane muhallin da aka nadi bidiyon da ma abin da ke faruwa a ciki amma ba mu gane ba domin babu sauti a bidiyon. Mun dai ga cewa akwai mztane biyar ne a bidiyon, kuma daya daga cikinsu na dauke da abin da ya yi kama da bindiga kirar AK-47.
Da muka sa a manhajar Google reverse search wanda ke tantance hotunan bidiyo, bai ba mu komai ba, dan haka sai muka fara yin binciken dalla-dalla.
A shafin Facebook, mung a labarai da dama da aka wallafa tare da wannan bidiyon da zarge-zarge da dama. MUn kuma gano wani labarin da aka sanya a shafin Tiwita a shafin AF News (@AFNewsNG) da zargi irin wannan.
Sai dai a shafin Facebook, mun gano wani labarin na daban dangane da wani batu a Kenya tare da hoton bidiyon.
“Kyamerar Drone ta gano mahara,” a cewar labarin.
Wani labarin da Madoka Kibet (@Madoke_ke) ya wallafa a shafin Tiwita kuma na dauke da bidiyon. Sai dai an goge jim kadan bayan da muka gan shi.
“Kyamerar drone na sanya ido bisa dalilai na tsaro ya gano maharan kabilar Kalenjin a cikin dajin Baragoi. Ana iya ganin daya daga cikin maharan wanda kyamarar ta fusata yana kokarin harbo ta kasa ba tare da ya yi nasara ba,” kadan daga cikin labarin ya bayyana.
Wani bidiyon da aka wallafa a YouTube a shafin Voice TV Nigeria ranar 5 ga watan Afrilun 2022 ya bayyana cewa lallai mahara ne da aga gano a yankin Laikipia.
Wani bidiyon YouTube din da aka wallafa a Trending Videos Kenya ranar lahadi uku ga watan Afrilun 2022, y ace maharani Pikot ne wadanda kyamerar drone ta nada a maboyarsu da ke dajin Laikipia.
Laikipia daya daga cikin gundumomi 47 da ke kasar Kenya ne, wadanda ke tsohon lardin Rift Valley.
Mun kuma gano wani labarin BBCPidgin wanda ya karyata cewa bidiyon ba a Najeriya ba ne.
A Karshe
Sakamakon bincikenmu ya nuna cewa bidiyon ba a Najeriya aka nada ba. An fara wallafa bidiyon a matsayin mahara a Laikipia Kenya. Dan haka wannan labarin ba gaskiya ba ne.