African LanguagesHausa

Labarin Karya: Paparoma Francis bai ce ya soke Bible a matsayin littafi mai ba

Zargi: Wani mai amfani da shafin Facebook na zargin wai Paparoma Francis ya ce ya soke Bible ya kuma bayar da shawarar fara wani littafin na daban

Wani mai amfani da shafin Facebook mai suna Nathan Kuma na zragin cewa a wani mataki na gyare-gyaren da ya ke a Cocin Katolika paparoma Francis ya soke amfani da Bible ya kuma shawarci da a fara kirkiro wani littafin na daban a madadin shi.

A cewar Mr Kuma, Paparoman ya yanke wannan shawarar ce domin a ra’ayin shi abubuwan da ke cikin Bible sun tsufa, ba su da wani tasirin a wannan zamanin, kuma suna bukatar sauyi.

“Paparoma Francis ya soke Bible ya bukaci da kirkiro wani sabon littafi mai tsarki na daban. A cewarsa Bible ya tsufa kuma yana bukatar sauyi na gaske dan haka an dakatar da amfani da shi a hukumance. Coci za ta sanar da sabon littafi da abubuwan da zai kunsa, wanda za’a yi amfani da shi a madadin Bible,”wani bangare na labarin ya bayyana.

“Ba za mu cigaba da tattaunawa da masu sauraronmu a duniya ta zamani ana kuma amfani da tsohon littafan da ya yi dubban shekaru ba. Mun fara rasa almajirai kuma muna bukatar sabunta coci, da maganar Ubangiji, ko da ya kasance cikin attaura ne (Torah)  inda akwai wadansu shafuka wadanda gara kada a sake maimaita su,” a cewar wani bangare na furucin da ake zargi na paparoman ne, wanda aka yi amfani da shi a labarin na Facebook.

Mr Kuma ya ce ya yarda da paparoman, ya kuma kara da cewa akwai sabani a cikin wadansu batutuwan da aka bayyana a Bible.

Da aka kalubalanci mai shafin aka karyata zargin a wurin tsokacin da ke karkashin labarin, Mr Kuma sai ya bayar da adireshin wani bidiyo a shafin YouTube a matsayin hujjar da ke karfafa zargin na sa.

Tantancewa

Mun fara da zuwa shafin YouTube din da Mr. Kuma ya bayar dan ganin bidiyon. Daga nan ne muka lura cewa taken bidiyon mai tsawon minti hudu da sakan biyar mai cewa “Bangaskiya da gyare-gyare a  Cocin Katolika daga Fadar Vatican: Cikakkiyar Daular Romawa” ba shi da wata alaka da Bible da ma bukatar kirkiro da wani littafi a madadin Bible.

Bidiyon ya mayar da hankali ne kan yadda birinin Roma ya kasance cibiyar darkar Katolika

Binciken mahimman kalmomin da muka yi kuma ya nuna mana cewa akwai kungiyoyin da suka riga suka yi binciken da ya karyata wannan zargin. Kungiyoyin sun hada da Politifact, Snopes, da jaridar India Today.

Mun kuma kara da binciken shafin ofishin jaridar Holy See wanda ke wallafa duk abubuwan da ke faruwa a Holy See tunda shi ne mazaunin gwamnatin Paparoma a Vatican. Nan ma ba mu ga komai dangane da soke Bible dan a maye gurbin shi da wani littafin mai tsarki ba.

Haka nan kuma ba mu ga labarin a sauran kafafen yada labarai masu sahihanci ba, tunda dai idan da gaskiya ne paparoman ya fadi hakan, labari ne da ya kamata a ce ya dauki hankalin da zai kasance a kanun kusan kowace kafar yada labarai mai nagarta.

A Karshe

Wannan zargin karya ce, babu inda mu ka ga wani rahoto dangane da soke Bible

Show More

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button