African LanguagesFact CheckHausa

Da gaske ne Trump ya umurci sayar da kaddarorin shugabannin Afrika da tasa keyar ‘ya’yansu kamar yadda wani ke da’awa a Facebook?

Getting your Trinity Audio player ready...

Da’awa: Wani labari a Facebook na da’awar wai shugaba Donald Trump na Amurka ba bayar da umurnin sayar da kadarorin ‘yan siyasar Najeriya da ke kasarsa.

Da gaske ne Trump ya umurci sayar da kaddarorin shugabannin Afrika da tasa keyar ‘ya’yansu kamar yadda wani ke da’awa a Facebook?

Hukunci: Karya ce. Babu labarai masu nagarta dangane da wannan da’awar. Hakazalika ba mu ga wani bayani makamancin haka a shafin fadar White House ba bare shafin shugaba Trump na X inda ya saba wallafa bayanansa masu mahimmanci.

Cikakken bayani

Tun bayan da ya kama aiki ranar 20 ga watan Janairun 2025, Donald Trump ya sa hannu kan umurnai da dama wadanda suka shafi batutuwa irin su, ‘yancin kasancewa dan kasa, akidu masu kaifi kan jinsi, kudin haraji a kan kasashen da ke kawancen kasuwanci da su, da kuma dakatar da tallafin kungiyar agaji na USAID.

Haka nan kuma, a babban shirin da ya yi, ya kuduri aniyar mayar da hankali ne kacokan kan jin dadin Amurkawa, dan haka Trump ya kaddamar da  samame a kan bajin da ba su da takardun izinin zama a kasar, wannan ya shafi mutane daga kasashen China, Columbia, Mexico, da ma kwananan nan India, ya na amfani da jami’an hukumar kula da kwastam da shige da fice wato ICE.

Sakamakon haka ne wani mai amfani da shafin Facebook, Ray Captain, ranar alhamis 30 ga watan Janairu ya yi da;awar cewa Trump ya bayar da umurnin sayar da duk kaddarorin da ke zaman mallakar shugabannin siyasar Afirka.

Ya kuma kara da cewa Trump ya ce za’a tasa keyar yaran su da ke can Amurkan suna karatu.

Labarin ya yi bayani kamar haka, “Shugaba Donald Trump ya bayar da umurnin sayar da kananan jiragen saman da ‘yan siyasar Amurka suka mallaka a Amurka. Ya kuma yi kira da a tasa keyar yaransu da ke karatu a kasar,”

Tilas ne ‘ya’yanky su yi karatu a kasarku domin sun tallafawa habakkarta,” ya kara da cewa.

Wannan labarin wanda ya bulla mako daya bayan da ya yi rantsuwar kama aiki ya sami martanoni 645, mutane 222 suka yi tsokaci a karkashin labarin. An sake raba shi sau 15 sadda muka yi ma’amala da labarin ranar uku ga watan Fabrairun 2025.

Masu amfani da shafin sun yi ta tabka mahawara dangane da sahihancin labarin, yayin da wasu kuma suka rika jinjinawa yunkurin shugaban.

“Ina ma da gaskiya ce wannan labarin. Da zai zama shawara mafi inganci da ya taba yankewa a rayuwarsa. Ya kamata ma a hana su zuwa ganin likita a Amurka, ina goyon bayan su,” Aboz AB, wani mai amfani da shafin Facebook ya rubuta.

Wani mai amfani da shafin kuma, Nyar Wema, cewa ya yo, “shin wannan gaskiya ce kuwa? Ina ma da zai kasnace gaskiya.”

Shi ma, Eden Noddy cewa ya yi, “Yanzu wannan ne irin shugaban da mu ke bukata”

A waje guda kuma, DUBAWA ta ga wannan da’awar a wasu shafuka inda ake dangata labarin da Najeriya da zargin cewa a can ya bulla a shafunkan X, Thread, da Facebook (a nan, nan, da nan), sa’annan a Instagram (nan da nan), a TikTok kuma (nan da nan).

Ganin yadda batun ya shiga ko’ina, mutanen da abin ya shafa da ma yiwuwar tayar da hankalin ‘yan siyasa ‘yan Afirkan da ke da dukiya a kasar, DUBAWA ta dauki nauyin tantance gaskiyar batun.

Tantancewa 

Domin tabbatar da gaskiyar batun, DUBAWA ta gudanr da bincike na mahimman kalmomi dan tantance ko da gaske shugaba Donald Trump ya bayar da umurni irin wannan na cewa a sayar da kaddarori mallakan ‘yan Afika, amma kuma ba mu sami wani bayani makamancin haka ba.

Min sake gudanar da wani binciken dangane da tasa yaransu da ke karatu a Amurka, a nan ma ba mu sami wani karin bayani ba.

Bacin haka, mun duba babban shafin fadar White House, inda take fitar da sanarwa a hukumance dan tantance gaskiyar wannan bayanin. Nan ma ba mu ga wani labarin da ke magana a kan tasa keyar mutane ba bare sayar da kaddarori kamar yadda ake da’awa.

Haka nan kuma, ko da muka duba shafin shugaban kasar na X inda ya saba zuwa ya yi bayanai masu mahimmanci, ba mu ga komai kamar haka ba tun bayan da ya yi rantsuwar kama aiki

Bugu da kari, DUBAWA ta yi bitar shafin da ke kula da kaddarorin mutanen kasar wahe a kasar, dan ganin ko za ta sami wani labari ko karin bayani a nan ba babu abun da ya bulla.

A karshe

Binciken DUBAWA dangane da zargin cewa shugaba Trump ya sayar umurci sayar da kaddarorin ‘yan siyasar Afirka da ma tasa keyar yaransu ba gaskiya ba ne.

Show More

Related Articles

One Comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
Translate »