Da’awar cewa Sarkin Musulmi da ke Sokoto bai taba sukar ‘yan fashin daji ba karya ce

Claim Sultan of Sokoto never spoke against banditry false
Getting your Trinity Audio player ready...

Da’awa: Wani mai amfani da shafin Facebook ya yada wani bidiyo inda yayi da’awar cewa Sarkin Musulmi bai taba magana ba, ko yayi kira da a hada kai a yaki masu fashin daji da ‘yanta’adda ba, sai a kwanannan. 

Da’awar cewa Sarkin Musulmi da ke Sokoto bai taba sukar ‘yan fashin daji ba karya ce

Hukunci: Karya ce. Bincike da DUBAWA ta gudanar yayi nuni da cewa mai rike da sarautar gargajiyar a lokuta da dama ya sha yin kira na a hada kai a yaki masu fashin dajin ko ‘yanta’adda.

Cikakken Labarin

A ranar 10 ga watan Yuli,2026 wani mai amfani da shafin Facebook kamar yadda yake amfani da sunan Calid Voice Eco, ya yada (kamar yadda aka alkinta nan) wani bidiyo inda yayi da’awar cewa, tun lokacin da aka fara ayyukan masu fashin daji da ayyukan ta’addanci a Najeriya Sarkin Musulmi Alhaji Muhammad Abubakar III, bai taba magana ba sai a baya-bayan nan.

A cewar mai da’awar Sultan yayi magana ne kawai a watan Yuli,2026 a lokacin da lamarin ya shafe shi, a makale a jikin bidiyon akwai hotuna da ya ce Sultan na cewa mutane su tashi su yaki ‘yanta’adda da masu fashin daji.

A bidiyon yayi masa take da cewa “Yanzu abin ya taba su, sai suke kira da hadin kai.”

Ya zuwa ranar 23 ga watan Satumba,2026 wannan wallafa ta samu wadanda suka kalla 109,000 da masu tsokaci 369 da wadanda suka sake yadawa su 440 da masu nuna sha’awa1,900.

Wannan wallafa ta samu martani kala-kala wanda suka rika nuna gazawar ta Sultan na yin magana kan batu na yaki da masu fashin daji da ta’addanci.

Wani mai amfani da shafin mai suna Chinedu Cornard, ya rubuta cewa, “Saboda suna cikin masu laifi a Amurka, shine yanzu suke magana mai kyau, nan ba da dadewa ba za su zama tarihi, ciki har da wadanda suka rubuta abubuwa a shafukansu marasa dadi kan Amurka daga bisani suka koma suka goge… ”

Temidayo Johnson yayi tsokaci da cewa, “Suna so ne a kawo karshen kisan ‘ya’yansu ‘yanta’adda.”

Ujagbo Jood ya rubuta cewa, “ wannan ai hawayen kada ne bayan da Amurka ta ce ta gano ana kisan gilla kan mabiya addinin Kirista a Najeriya, shi ta shafa.”

Hada masu fashin daji da ‘yanta’adda da Sultan, a cewar Carol Asuai Obi, “Sultan mutum ne da ake son shi kuma sarki mai daraja, amma halin da ake ciki a Najeriya yanzu ban yarda da hadin kansu ba, ba mutanen da za a yarda da su ba ne, sai dai idan suka hade za a fi samun saukin kawar da su. Maganarsu ta hadin kai karya ce.”

Olugbenga Adams ya rubuta cewa “ Sultan na ikirari ne kawai; karaya ce kar a yar da da abin da ya fada.”

Duba da yanayin wannan wallafa da irin tashin hankalin da za ta iya jawowa a fadin Najeriya DUBAWA ta ga dacewar gudanar da bincike kan wannan da’awa.

Tantancewa

DUBAWA ta gudanar da bincike kan abubuwan da suka shafi wannan da’awa sai ta gano wasu labarai masu alaka. A rahoton kafar yada labaran Channel Television na ranar 10 ga Afrilu,2019 bayan da aka rika samun karuwar matsalar tsaro a yankin Arewa maso Yammacin Najeriya Sarkin Musulmi yayi alkawari na ba da tallafi a kokari na jami’an ‘yansanda da sauran jami’an tsaro don kawo karshen masu fashin daji da sauran ayyuka na miyagun laifuka a Arewacin Najeriya.

Ita ma kafar yada labaran The Cable ta ba da rahoto a ranar 30 ga watan Mayu,2020 bayan hari da aka kai a Sokoto, wanda yayi sanadin rayukan mutane 70 mai sarautar ba kawai yace a “kamo masu wannan ta’addanci ba’’ yace matsalar tsaro ta tabarbare a wannan yanki. 

A ranar 31 ga Mayu,2020 kafar yada labaran Channels TV ta ba da rahoto cewa Sarkin Muslmi yayi kira da a kara yawan kudade da ake kashewa harkokin soja ta yadda za su iya kawo karshen masu fashin daji da sauran miyagun laifuka. 

A rahoton sai ya bukaci yin hadaka ta hana tunkarowar ‘yanfashin dajin da ke yawo daga wata jiha zuwa wata.

Mai magana da yawun Sultan  Mallam Aminu Haliru,  ya tabbatar da abin da DUBAWA ta gano inda ya fada mata cewa Jawabin na ranar 9 ga Yuli, 2026 ba shine karon farko ba da Sarkin Musulmi yayi kira da a samar da hadin kai, a kokari na kawo karshen ‘yanfashin daji da ‘yanta’adda; a lokuta da dama ya sha kira na a duba matsalar tsaro a Najeriya.”

A yayin wani taro da Sultan ya halarta a ranar 4 ga Disamba,2025 da kwamitin zaman lafiya na kasa karkashin ofishin mai ba wa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro da Cibiyar Kukah mai taken “Hada kan kafatanin al’umma,” Sultan ya bukaci ‘yan Najeriya su hada kai don tunkarar matsalar masu fashin daji bai daya.

A can baya ma a 2025, kafar yada labaran Jolibalivenews ta ba da rahoto a zaman shugabannin kwamitin masu rike da sarautun gargajiya na arewacin Najeriya karo na 7 a Maiduguri, wanda shi Sultan ya jagoranta ya bayyana cewa “Mutanenmu suna fuskantar yin garkuwa da su da kashe su ga fargaba kowace rana , dole muyi baki daya  mu kuma yi aiki bai daya don dawo da zaman lafiya.”  

Kafafan yada labarai da dama a lokacin da ake samun kai hare-hare a Sokoto, Sarkin Musulmi yana yawan kira da a samu hadin kai ba kawai a jihar ita kadai ba, amma a fadin kasar.

A Karshe

Da’awar karya ce. Rahotanni na kafafan yada labarai sun nunar da cewa a karo daban-daban Sultan na yawan kira da a samar da hadin kai a yaki masu fashin daji da ‘yanta’adda a Najeriya. Kuma wadannan rahotanni an same su kafin Yuli,2026. 

An gudanar da wannan aiki karkashin Cibiyar koyon Aikin Jarida da Kirkire-kirkire da Ci-gaba (CJID) bisa daukar nauyin Kungiyar Tarayyar Turai.