African LanguagesHausa

Dalilai bakwai da suka sa Najeriya ke aro kudi sabanin ta buga takardun kudin

Getting your Trinity Audio player ready...

A ‘yan shekarun baya-bayan nan Najeriya ta fuskanci tarin kalubale wanda ya hadar da hauhawar farashin kayan masarufi da hawa da saukar farashin mai da ga yawaitar (expanding) al’umma. Irin wadannan tarin kalubale sun sanya ana kallon gwamnatin ba za ta iya warware tarin kalubale da ke gabanta na harkokin kudade ba musamman matsalolin bashi da suka dabaibaye kasar.

“Yan Najeriya na ci gaba da samun damuwa a dangane da dinbin bashi da kasar ta kwasa a tsawon shekaru 10 da suka gabata. Ga mutumin da ke zaune a Najeriya a duk sanda aka yi maganar bashi abin da ke zuwa zuciyarsa shine, an kara masa matsala kuma zai samu koma baya a fannin zamantakewa da tattalin arzikinsa. Ga misali bayan watanni hudun farko na shekarar 2023 bashi da ake bin Najeriya ya kai ya kai Dala biliyan $113.42 wanda ke daidai da tiriliyan N87.38 .

A kowace rana akwai masu tambaya da mamaki ( wonder ) me yasa kasar da ta fi kowace kasa yawan mutane a Afurka ke karbo bashi maimakon ta rika buga kudaden na Naira don ta rika gudanar da ayyukanta manyan ayyuka da wadanda ake yi yau da kullum.

Ga misali wani mai amfani da shafin X Osasioma, ya rubuta cewa “A yau babu abin da uke ji sai zaa buga sabbin kudade da zuwa karbo bashi daga nan zuwa can, an sai ta kudaden da muke samu daga manfetir da kudaden haraji da suke shigarwa kasa kawai a rika biyan bashi.”

Haka nan shima wani mai amfani da shafin na X Seun, ya nunar da mamakinsa har ma yake cewa “mai ya sa a ko da yaushe Najeriya ke zuwa karbo bashi bayan da kuwa Babban Bankin Najeriya CBN zai iya buga kudaden da kasar ke bukata ?”

Wannan ya bude babi na nazartar yadda harkoki na tattalin arziki suke, Domin fahimtar wannan sarkakiya cikin sauki, akwai bukatar sanin dalilai da suke sa kasa ke kaucewa kai tsaye ta tafi tana buga kudade.

Takaita hauhawar farashi

Daya adaga cikin dalilai da suka sa Najeriya ke karbo bashi maimakon buga kudade shine ta dakatar da hauhawar farashi-hauhawar farashi mai muni, yayin da kudade suka yi yawa a hannun al’umma darajar naira za ta yi kasa sannan farashin kayayyaki zai hauhawa.  Ba zaa manta da abinda ya faru ba a tsakiyar shekarar 1996 (mid-1996,) lokacin da hauhawar farashi ta yi awon gaba da “yankudade da Najeriya ta yi tattalinsu, “yan Najeriya na sane da wancan lokaci. Ana samun mafita ne idan akwai yawaitar kudaden yayin da a bangare guda kuma kasa ke kere-keren kayayyaki da wasu ayyuka. Amma Najeriya tafi ga wasu kasashen su kera ta siya ita bata nata kere-keren. Ta hanyar karbo bashi gwamnati za ta iya sa idanu kan karakainar kudade a hannun jama’a, azbin da ka iya jaewo daidaiton farashi  da kare hauhawar farashi.

Abin da aka yi tattali a asusun ajiya na kasashen waje 

Shekaru da dama Najeriya na dogara ne da abin da ake shigowa da shi kasar ga misali manfetir kasar na fitar da shi zuwa ketare amma wanda aka tace ake kawo mata (imports refined petrol) don amfani al’ummma.

Karbar bashi ke sanyawa kasa ta rika tattalin abin da ke a asusunta na kasashen ketare don ta biya kudade yayin da take shigo da kayayyaki ta kaucewa rikicin cin bashi., Shi kuwa batu na buga kudi na rage tasirin kudi , ya takaita kudaden da kasa  za ta yi amfani da shi idan atana so ta shigo da kayayyaki  daga ketare. Wannan kuma ba makawa zai kai ga yanayi da Najeriya za ta rika shigo da kayayyaki ko a yi mata wasu aiakace-aikace bashi.

Rage nauyin bashi

Buga sabbin kudade na rage darajar naira, abin da ke sa biyan bashi ya zama yana da tsada (expensive)..  Wannan na iya kara nauyin bashin da ke kan Najeriya, saboda sai an sanya naira mai tarin yawa kafin biyan bashi komai kankantarsa. Wani abin mamakin shine bashin zai ci gaba da ninnikawa bayan lokaci, ta hanyar aron kudaden ne gwamnati ke iya rage wa kanta bashi.

Karawa masu zuba jari karfin gwiwa

Masu zuba jari na cikin gida da wajenta na iya kara kudaden da suke zuba a cikin kasa idan suka ga tana da wata fasaha tana kuma iya daidaita tattalin arzikinta, yanayi na bashin da ke kan Najeriya na sa kasa ta mayar da hankali kan nauyin da ke kanta , hakan kuma na jan hankali na masu son zuwa zuba jari abin da ke kara bunkasa tattalin arzikin kasa. Masu ba da bashi na cikin gida da waje da masu zuba jari na bude ido sa rai su kalli kasar da ke kashe makudan kudade wajen buga kudade.

Daukar nauyin manyan ayyuka

Aro kudade shine zai sanya Najeriya ta cimma bukatunta na ci gaba ciki kuwa har da na samar da ababen more rayuwa da gyara harkokin kula da lafiya da ilimi da bunkasa ayyukan noma , wannan kan bunkasa tattalin arziki da inganta rayuwar al’umma, bayan fidda tsare-tsare na karbar bashin mai cin dogon zango. Idan ta shiga kasuwannin duniya Najeriya na iya samo rancen kudade (secure funds) masu saukin kudin ruwa abin da zai taimaka ta rika biyan bashin sannu a hankali tsawon lokaci. 

Dacewa da cika tsarin kasa da kasa

Karbar basukan na sawa kasa ta samu nutsuwa wajen cika ka’idoji da tsare-tsare karbar basukan tsakanin kasa da kasa (lending norms.)  ta hanyar hulda da cibiyoyi masu yawa da masu ba da bashi masu zaman kansu, wannan zai sa Najeriya ta yi taka tsan-tsan kan yadda take kashe kudadenta  ta kuma tirjewa masu wawashe dukiyar al’umma ta hanyar cin hanci da rashawa  da wasu dalilai marasa sahihanci.

Diflomasiya da hada kai

Ta hanyar karbar bashi ana saurin samun kulla alaka da hadin kai da wasu gwamnatoci na kasashen waje da  wasu cibiyoyi  abin da zai kawo musayar kwararru da ilimi da bunkasar kowane bangare ta hanyar bani-in-baka, ta hanyar haka ne Najeriya za ta samu kanta  a tsakanin kasa da kasa tana bin hanyoyi na warwarewa kanta matsaloli na samun ci gaba ta bude wasu damarmaki na samun ci gaba.   

Yadda Najeriya ke gwammacewa ta aro kudade maimakon ta rika bugawa, batu ne na nazariyya kan harkoki na hada-hadar kudade da haraji da daidaiton tattalin arziki da sauye-sauye da ke faruwa a duniya. Shi kuwa buga kudade na warware matsalar tattalin arziki ce ta yanzu-yanzu, bayan an dauki lokaci ne za a fahimci illar da hakan ke wa tattalin arziki.

Ta hanyar amfani da dattako ne da hangen nesa Najeriya za ta hau kadami na samun ci gaba mai dorewa sannan al’ummarta ta samu ci gaba inda za ta rika kai komo kan harkoki da suka shafi kudade tsakanin kasa da kasa  da taka tsantsan.

Wannan bincike an yi shine karkashin shirin binciken gano gaskiya na DUBAWA 2024  karkashin shirin kwararru na  Kwame KariKari da hadin gwiwar WikkiTimes a kokari da ake yi na tabbatar da labaran gaskiya da kare martabar aikin jarida da ilimin aikin jarida a fadin kasa.

Show More

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button