African LanguagesHausa

Gaskiya ne, Okitipupa a tsawon shekaru goma basu da hasken wutar lantarki!

Getting your Trinity Audio player ready...

Da’awa: Wani mai amfani da shafin X yayi da’awar cewa a tsawon shekaru goma al’ummar  Okitipupa, da ke jihar Ondo a yankin Kudu maso Yammacin Najeriya ba su da hasken wutar lantarki.

Gaskiya ne, Okitipupa a tsawon shekaru goma basu da hasken wutar lantarki!

Hukunci: GASKIYA CE! A binciken da DUBAWA ya gudanar ya gano cewa al’ummar yankin na Okitipupa basu da hasken wutar lantarki a sama da shekaru 10.

Cikakken Sako

A ranar 8 ga watan Fabrairu wani mai amfani da shafin X @Iamgomez, posted yayi wallafa da ta nunar da cewa a tsawon shekaru sama da goma al’ummar yankin Okitipupa na jihar Ondo basu da hasken lantarki.

Mai amfani da shafin na X na mayar da martani ne ga wani da shima ke amfani da shafin na X @Bookienotbukky, wanda ya bayyana cewa “Abin yayi kama da karya amma ba karya bane.”

Wannan da’awa kan yankin na  Okitipupa ya samu mutane miliyan 1.2 da suka kalla da wadanda suka sake wallafawa (reposts) 4,721 da wadanda suka nuna sha’awarsu da labarin dubu 13.9k sai wadanda ke kafa hujja 495.

Da yake mayar da martani wani mai amfani da shafin na X mai suna @Templecapalot,  yace “Karya ce don a watan Disambar bara na je bikin binne gawa a garin suna da hasken lantarki a garin kai hasken ma daga gwamnatin tarayya ne.”

Ba da jimawa ba sai wani mai amfani da shafin na X shima  @Omotohwunmi1, “Na yi mamaki da na je garin a shekarar bara da na tambaya game da hasken lantarki aka fada min cewa a tsawon shekaru masu yawa basu da hasken lantarki.”

DUBAWA ya ga dacewar gudanar da bincike kan wannan da’awa ganin yadda aka samu tsokaci mai tarin yawa daga al’umma kan wannan batu.

Tantancewa

DUBAWA ya tuntubi kamfanin rarraba wutar lantarki na Benin Benin electricity distribution company (BEDC) wanda ke lura da rarraba wutar a jihar ta Ondo inda anan ne garin na Okitipupa yake. 

A tattaunawa da aka yi da jami’i a kamfanin na BEDC ta manhajar WhatsApp, jami’in da ya bayyana kansa a matsayin Mikel ya tabbatar da cewa babu hasken lantarki a Okitipupa a sama da shekaru goma.

“Tabbas, akwai rashin wuta a yankin.”, yace bayan da aka tambaye shi ko rashin wutar ya dauki lokaci mai tsawo kamar shekaru 10 kamar yadda mai da’awar ya nunar a shafin na X.

Da aka sake tambayarsa ko babu wuta a yankin, sai jami’in yace “kana iya tuntubar ofishinmu da ke  jihar Ondo don karin bayani.”

DUBAWA bai tsaya anan ba sai da ya tuntubi al’ummar da ke zaune a yankin don kara samun damar kafa hujja game da wannan da’awa.

Wani mazaunin garin na Okitipupa, Oluwadara Sedara, ya tabbatar da da’awar inda yace rabon da al’ummar wannan gari su ga hasken lantarki tun a watan Janairu shekarar 2014.

“An katse mu daga layin da ke ba da hasken lantarki na kasa tun a Janairu 2014. Kamfanin da ke rarraba hasken lantarki na Benin ya fada mana cewa ana binmu bashi na miliyoyin naira, duk wani kokari na ganin an sake mayar mana da wutar lantarki kokarin yaci tura. Mun yi jerin zanga-zanga a karo daban-daban, amma babu wani sakamako da muka gani, muna ta fama da matsalar rashin hasken lantarki kimanin shekaru goma kenan.” a cewarsa.

A nasa martani a dangane da wannan da’awa Itiolu Emmanuel, mataimaki na musamman ga Oba Babatunde Faduyile, jagora a Ikale-land karkashin daular ta Okitipupa yace an samu rashin wuta a yankin sama da shekaru goma.

“Tabbas, mun rasa wuta sama da shekaru goma, Ina iya tunawa abin ya samo asali tun a 2012 ko da yake rashin wutar da aka samu a yankin Ikale land  ma ya wuce wadannan shekaru  tun da ya fara ne a ranar 29 ga watan Disamba, 2012, ” a cewarsa.

Shima Oba Michael Adetoye Obatuga, Jegun na Idepe Okitipupa, shugaban al’umma a yankin na Okitipupa ya ba da tabbacin cewa sun rasa wuta a sama da shekaru goma.

“Ba zan iya tuna adadin shekarun ba, amma na sani cewa ya wuce shekaru goma, a wasu yankunan ma shekarun sun fice haka.”

Har ila yau DUBAWA ya gano cewa gwamnatin tarayyar Najeriya ta hanyar hukumar raya yankin Niger Delta (Niger Delta Development Commission)  a ranar Laraba 22 ga watan Mayu, 2024 ta kaddamar (inaugurated) da aikin da ya lakume miliyan dubu  N8.1 a aikin lantarki na  Ode-Erinje  da zai samar da  132KV/33KV. An ajiye karamar tashar wannan aiki a yankin na Okitipupa a jihar ta Ondo don sake dawo da hasken lantarki ga al’ummar  yankin ko ma a ce ga al’ummar da ke yankin Ondo ta Kudu. 

Kafafan yada labarai da dama sun ba da labarin kaddamar da wancan aiki, lamarin da ya jawo rahotanni masu karo da juna kan adadin yawan shekarun da aka dauka babu hasken na lantarki.

Yayin da kafar yada labaran rediyo mallakar jihar ta Ondo ta ba da labari da yayi ikirarin (claimed) maido da hasken lantarki a yankin ta hanyar kaddamar da wannan aiki bayan shekaru 15 al’umma basu da wuta.

Wata kafar yada labaran ta rediyo kuwa Positive FM of the Federal Radio Corporation of Nigeria, ta ba da rahoton cewa an maido da hasken lantarki bayan shekaru 12.

Ita kuwa kafar yada labarai ta jaridar Hope Newspaper da ke a jihar ta Ondo ta ba da rahoto ne (reported) cewa an mayar da hasken lantarki a tituna a yankin al’umma na  Okitipupa.  

Karshe

A bincike da DUBAWA ya gudanar ya gano rashin hasken lantarki a yankin al’umma na Okitipupa, a jihar ta Ondo sama da shekaru goma. Labarin gaskiya ne. Sai abin da ba a da tabbaci a kansa shine adadin shekaru da aka dauka babu hasken na lantarki.

Wannan rahoto an fitar da shi karkashin shirin gano gaskiya na DUBAWA 2024 karkashin shirin kwararru na Kwame KariKari da hadin gwiwar  The Informant247 a kokari da ake yi na tabbatar da labaran gaskiya da kare martabar aikin jarida da ilimin aikin jarida a fadin kasa.

Show More

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button