Hausa

EFCC ta tabbatar da binciken jaridar Daily Trust da Dubawa dangane da rigar maman lu’u-lu’un Diezani

Kasa da makonni biyu bayan da jaridar Daily Trust da Dubawa suka wallafa sakamakon bincikensu dangane da ko akwai rigar maman lu’u-lu’un da ake zargi ita ce mafi tsada a cikiin kayayyakin da tsohuwar ministan man fetur da ma’adinan karkashin kasa Diezani Alison-Maueke za ta yafe, hukumar EFCC ta tabbatar da gaskiyar sakamakon wannan binciken.

Rahoton da wata jarida ta wallafa ya yi zargin cewa daga cikin kayayyakin da tsohuwar ministar wadda ake zargi da sama da fadi da dala biliyan biyu da rabi, har da “gidaje a Banana Island da ke jihar Legas.” Ya kara da cewa akwai rigunan aure 125, kananan rigunan saw a 13, rigunan maza 11, dammarar tumbi 41, rigunan mama na musamman 11, da sauransu.

To sai dai masu amfani da soshiyal mediya sun yi gaban kansu har suna zargin cewa daga cikin kayayyakin ma akwai rigan maman da aka sanyawa lu’u-lu’u kuma irin shi ne mafi tsada a duniya domin farashin shi ya kai dalan Amirka miliyan goma sha biyu da rabi.

Binciken da jaridar Daily Trust da Dubawa suka wallafa ranar 7 ga watan Oktoba, 2021, ya bayyana cewa zargin wai tsohuwar ministar man fetur na da rigar maman da ya fi tsada a duniya karya ne.

Binciken ya yanke wannan shawarar ne bayan da ya bi diddigin gano tushen tarihin rigar mama mafi tsada a duniya zuwa wata rigar mama mai suna “heavenly star bra” a turance, wanda aka kirkiro a shekarar 2001 a kamfanin Victoria Secrets wani kamfanin rigunan mata na Amirka wanda Heidi Klum, bajamushiya kuma shahararriya a fanin kawa ta sanya lokacin wani bukin kwalisa a shekarar 2001.

Binciken ya gano cewa masu zargin Madam Alison Madueke da mallakar rigar maman sun yi amfani da hotunan daya daga cikin wadanda kamfanin Victoria Secret ya kirkiro ne. Wanda ya rubuta wannan labarin kuma ya nemi karin bayani dangane da batun daga ofishin Antoni Janar na kasa wanda ke kula da irin wadannan kayayyakin.

Mataimakin Antonin a fanin watsa labarai Malam Umar Gwandu wanda ya yi mana karin bayanin ya karyata zargin.  A yayin da shi kuma shugaban hukumar EFCC Abdulrasheed Bawa ranar laraba ya fayyace batun a daya daga cikin shirye-shiryen tashar TVC mai suna “Your View” inda ya ce: “Sau da yawa kuna zargin mu da gudanar da shari’a a kafofin yada labarai amma a tunani nay a kamata a rika kamanta adalci wa kowa da kowa. Babu wata rigar mama. Masu amfani da soshiyal mediya ne kawai suka kulla wannan sharrin.”

Ya kuma kara da cewa: “Zan iya gaya muku wannan kyauta tunda ni ne jagoran binciken kuma ban ga wani abu kamar haka ba. Idan da akwai, da na sani. Ya kamata a ce na sani tunda ni na jagoranci binciken. Shi ya sa na ce daya daga cikin manyan matsalolinmu it ace halayarmu. Ya kamata mu canza dan a sami gyara.” 

Show More

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button