Getting your Trinity Audio player ready...
|
A baya-bayan nan an fitar da hukunci (ruling) na Babbar Kotun Tarayya da ke zamanta a Kano a dangane da dambaruwar masarautar Kano lamarin da ya jawo rudani a tsakanin al’ummar Najeriya a dangane da fahimtar dabaibaiyin da ke sarke masarautar ta Kano.
A karar da ya shigar (suit) Aminu Babba Dan-Agundi, Sarkin Dawaki Babba, ya nemi da kotu ta dakatar da sabuwar dokar da aka yi wa gyara ta masarautar ta Kano 2024, wacce ta sake dawo da Muhammadu Sunusi II a matsayin sarkin Kano na 16. Wadanda ake karar sun hadar da gwamnatin Kano da majalisar dokokin jihar da shugaban majalisar dokoki da kwamishinan shari’a a jihar, sauran kuwa sun hadar da kwamishinan ‘yansanda na jihar da Sifeton ‘yansanda na kasa da Hukumar Tsaro ta Fararen Hula (NSCDC) da jami’an ciki na (DSS).
Kotun tun da fari ta fitar da wata oda (issued) wacce ta nemi a dakatar da aiwatar da sabuwar dokar masarautun ta 2024 har zuwa lokacin da aka saurari karar. Har ila yau a ranar 20 ga watan Yuni karkashin jagorancin mai shari’a Abdullahi Liman a odar da ya bayar mai lamba FHiC/KN/CS/182/2024, ya nemi gwamnatin Kano da sauran wadanda ke da ruwa da tsaki kan batun da su dakata wajen aiwatar da wannan sabuwar doka da ta shafi masarautar ta Kano har zuwa lokacin da za a saurari karar da aka shigar.
Wannan hukuncii dai ya haifar da rudani kan shugabancin masarautar da fannin shari’a har ma da fage na siyasar jihar ta Kano wanda kuma ya jawo magoya bayan ‘yanuwan guda biyu Sunusi II da Bayero, suka shiga yada labarai wadanda ba sahihai ba don nuna cewa su ke da nasara. Mazauna jihar ta Kano da sauran masu ruwa da tsaki sun shiga rudani (confused) da hali na rashin tabbas. Ga labarai masu karo da juna a shafukan sada zumunta X (da aka fi sani da Twitter) da Facebook.
Dukkanin bangarorin biyu na gwamnatin Kano da bangaren na Bayero sun bayyana fahimtarsu a dangane da hukuncin kotun, wanda kowanne ya bayyana abin da zai zama mafi so a gare shi. Bangaren gwamnatin Kano suka nunar da cewa hukuncin na nufin Sunusi II shine halastaccen sarki a Kano (Kano emir) don haka ma gwamnatin ta umarci kwamishinan ‘yansanda da ya fitar da Bayero daga gidan sarki na Nasarawa. Suma a nasu bangare Bayero karkashin jagorancin Aminu Babba Danagundi sun nunar da cewa hukuncin na nufin Bayero shine halastaccen sarki (emir) a Kano.
Sannan dukkaninsu Sunusi na biyu da Bayero sun bayyana shirinsu na hawan sallah babba (durbar), sarakuna biyu a Kano, sai dai daga bisani rundunar ‘yansanda ta haramta hawan na durbar a Kano a hawan sallar babba.
Sannan kuma dukkanin bangarorin biyu Sanusi II da Bayero suna zaman fada a dukkanin fadojin biyu a kowace rana. Bayero ya sa an daga tutar sarki (Sultan’s flag) a gidan na Nasarawa wanda hakan ke nuna sarauta halastacciya.
Wasu daga cikin ‘yankannywood sun taimaka wajen baza wannan bayanai masu cin karo da juna, game da wadannan sarakuna ga misali mawakin nan Naziru Sarkin Waka, wanda ya wallafa wani bidiyo (video) da ke tabbatar da cewa Sunusi II shine tabbataccen sarki a Kano. Wannan wallafa da yayi ta samu masu nuna sha’awarsu su 5,400 da masu sharhi 503 da wadanda suka sake yadawa su 194.
Haka shima a nasa bangaren Aminu Ladan Alan Waka, wani fitaccen mawakin a Kano ya gabatar da wasan sallah da yin waka (freestyle concert) a gidan sarki na Nasarawa.
Wani mai amfani da shafin na X, MS Ingawa, ya wallafa cewa duba da oda da kotu ta bayar ya nuna cewa babu sarki a Kano , ta yiwu wannan ya sa Gwamna Yusuf ya sake nada sabon sarki, wannan wallafa ta Mista Ingawa ta ja hankali sosai in da mutane 76300 suka kalla sai wadanda suka nuna sha’awarsu su 361 da wadanda suka sake wallafawa 106, akan dai wannan wallafa wani mai bin sa Tony ya mayar da martani da cewa,
“Idan wannan haka yake me zai faru idan gwamnan ya sake mayar da shi (Sanusi II) a matsayin sarkin Kano har ila yau? Wannan ya ci karo da doka?” Shima Mohammed ya mayar da nasa martani ga Mr. Ingawa da cewa “Mutane irinka da wasu wadanda ke yada wannan farfaganda saboda radin kansu da akida, bai kamata a baku shugabanci ba,. Duba dukkanin su Sunusi da Bayero sun je kotu kuma kotu ta fitar da hukunci, mai ya kawo wannan? Kano ta fi karfin maganar mutum guda.”
” Wani mai amfani da shafin na X Sambo Mai Hula, a wata wallafa da ta samu masu kallo 30,200 da nuna sha’awa 485 da sake wallafawa 148 ta mayar da martani da cewa Aminu Bayero shine sarki a Kano, abin da ke nuna ja ga ra’ayin Mai Hula. Suspect, yace hukuncin ya nunar da cewa an sauke Bayero daga sarki (deposed Bayero). Don haka ya zama “tsohon sarkin Kano ya karbi kaddara da hukuncin kotu.”
Ita ma Gimbiya M ta fitar da nata ra’ayi inda tace “ Nifa na shiga rudani kan wannan hukunci wasu na cewa Sunusi II shine sarki wasu na cewa Bayero a bani mafita, ba na so na zama abar dariya wallahi.”
Wani mai amfani da shafin X Salisu Umar yayi da’awar cewa duba da bayanin da wani babban lauya mai mukamin (SAN) yayi masa ya nunar da cewa Aminu mulkinsa ya zo karshe a Kano Sunusi II shine halastaccen sarki.
“Hukuncin kotu ba zai jingine korar ba. Dokar halastacciya ce mai mukamin na SAN ya ci gaba da cewa ban san macece makomar Aminu ba, amma dai aikin da aka dora masa ya kammala.” a cewarasa.
Wallafar da Umar yayi a shafin na X ya samu wadanda suka kalla 36,200, da masu nuna sha’awa 161, da wadanda suka sake wallafawa 87.
Wani daga cikin wadanda suka mayarwa da Umar martani Real Nigerian, yace Bayero ba shi da wata dama ta ci gaba da zama sarkin Kano, yana bin abin da makiya ke fada masa ne kawai, Sai dai kuma wani mai suna Loke ya mayar da martani da cewa idan da gaske ne bayanan na SAN ba shine hukuncin karshe da kotun ta fitar ba (isn’t )a harkar shari’a ba wanda za a jinginawa.
Don haka DUBAWA yayi nazari kan wannan bayanai masu karo da juna da wasu batutuwa da ke kawo rudani a dangane da dambaruwar masarautar ta Kano, ganin irin tasirinsu don a samu mafita ko fahimta.
Watsi da sake dawo da Sanusi II
Hukuncin kotun ya rushe sake dawo da Sunusi II a matsayin sarkin Kano na 16
“ A wannan gaba nake fitar da hukuncin cewa duk wani abu da aka yi bayan amincewa da dokar masarautar Kano ta 2024 da aka yiwa kwaskwarima ya zama rusasshe mara amfani an kuma jingine shi, “a cewar odar ta kotu.
Sai dai a nata martani a dangane da wannan hukunci gwamnatin Kano ta jadda insisted cewa Sunusi II shine halastaccen sarkin Kano, sai dai wannan baya ba da tabbacin cewa matsayar su halastacciya ce saboda gwamnatin ba ta bi umarnin kotu ba na farko wanda ya dakatar da sake restraining nada sarki Sunusi.
Sake mayar da Bayero
A hukuncin kotun alkalin ya ce ya rushe( annulled all actions) duk wasu matakai da gwamnatin Kano ta bi na tube rawanin Bayero da sake dawo da SunusiII, inda ta bukaci dukkanin bangarorin biyu da su tsaya inda ake.
“Na ba da umarni cewa duk wasu matakai da aka dauka da suka jibinci dokar masarautar ta Kano da aka yi wa kwaskwarima 2024 babu shi an kuma jingine shi.” A cewar Mai Shari’a Muhammad Liman.
Da yake fashin baki a dangane da hukuncin kotun lauya mai zaman kansa a Kano Abba Hikima yace Aminu Ado Bayero a idanun doka shine , (remains) sarkin Kano a idanun doka “A idanun doka sarkin Kano shine Aminu Ado Bayero.” A cewarsa.
Kauracewa da hukuncin kotu mai cin karo da juna
Hukuncin babbar Kotun Tarayya ya jaddada cewa abun da gwamnatin Kano ta yi wanda ya hadar da sake dawowa da sarki Sunusi II, ya sabawa umarnin kotu da ya gabata da ta ce kowa ya koma a matsayinsa, ko yadda ake a da,
“Ina ganin lamari ne babba a ce wani yayi wasa da umarnin kotu sannan ya tafi babu hukunci.” Acewar Liman, alkalin ya kara da cewa gwamnati gana sane da wannan umarnin kotu ta toshe kunnenta, wannan ya sanya aka yi fatali da abin da ta yi. Haka nan kuma matakin da kotun ta dauka ya sake dumama fannin siyasa da sharia a Kano ganin yawaitar umarnin kotu da aka rika fitarwa daga alkalai.
Ga misali, a ranar da Mai Shari’a S. Amobeda na babbar kotun tarayya mai lamba ta uku ya ba da umarnin cewa Sarki Sanusi II ya fice daga Gidan Rumfa a wannan rana ce kuma Mai Shari’a Amina Aliyu ta Babbar Kotun jihar Kano ta ba da umarni cewa kada ‘yansanda su kurkura su fitar da (Sanusi and restrained ) sannan ta haka sauran sarakuna su rika bayyana kansu a matsayin sarakuna.
A wani hukuncin kuma Mai Shari’a Amobeda awarded ya umarci gwamnatin Kano ta biya Bayero N10,000,000 saboda abin da ya kira take masa hakki da ‘yancinsa na walwala da watayawa.
Sahihancin Dokar Masarautu ta 2024
Hukuncin da Babbar Kotun Tarayya ta fitar ya nunar da cewa kwaskwarima da aka yi wa dokar masarautun ta 2024 halastacciya ce.
“……umarnin bai shafi sahihancin dokar ba,”a cewar kotun, anan ma Hikima yace odar da kotu ta bayar sahihiya ce har zuwa lokacin da za ta fitar da matsaya ta karshe.
Sauya wurin Sauraren Shari’a
Wannan shari’a an sauya mata wurin saurare (transferred) zuwa Kotun Tarayya karkashin Mai Shari’a Simon Amobeda don ci gaba da sauraren shari’ar bayan da gwamnatin Kano ta daukaka kara cewa waccen kotun ba ta da hurumi na sauraren karar da ta shafi shugabanci na harkokin masarauta.
Shirin Daukaka Kara
Gwamnatin jihar Kano ta bayyana (announced) cewa ta kudiri aniyar daukaka kara kan hukuncin Babbar Kotun Tarayyar. Da yake tsokaci kan wannan Barista Sani Tsanyawa yace babbar kotu ce kadai ke iya jingine umarni ko oda da Babbar Kotun Tarayya ta bayar, don haka bangarorin suna iya daukaka kara idan basu gamsu da hukuncin kotun ba.
Kamanceceniya tsakanin Dokokin Masarautar ta Kano
A shekarar 2019 Abdullahi Umar Ganduje shugaban jam’iyyar APC a lokacin yana gwamnan Kano ya rattaba hannu kan dokar masarautar Kano wacce ta zama gyara ga dokar masarautar ta 1984 Kano Emirate Law. A dokar ta 2019 an kara samar da karin masarautu Rano, Bichi daKaraye da Gaya. Shekaru uku daga bisani Ganduje ya sanya signed hannu a dokar da aka yi wa kwaskwarima a 2023. Ya kuma amince (assented) da dokar da aka kwaskware a 2020.
Hikima ya bayyan a cewa dokar da aka yi wa kwaskwarima a 2023 tana da sassa 50 da kananan sassa 100 inda suka yi bayani dalla-dalla kan ofishin sarki da sauran masarautun hudu. Sabanin dokar masarautar da aka yi wa kwaskwarima a 2023. Sai dai dokar masarautun ta 2024 da aka gyara bata yi bayani ba kan matsayin masarauta, za ta iya kai kara ko a kaita kara. Bata kuma yi bayani ba kan batun da ya shafi kudi na masarautar ta Kano, abin da ke asusunta da kasafin kudinta ga misali.
Matakan tsaro
Bayan fitar sakamakon kotun rundiunar ‘yansanda reshen jihar Kano ta jaddada reiterated haramta gudanar da zanga-zangar al’umma da taruwar al’umma ta yadda za a samu zaman lafiya da bin doka.
DUBAWA ya lura cewa tun bayan matsayar kotu sai birnin ya zama lafiya al’umma sun ci gaba da huldodinsu an kuma jibge jami’an tsaro a wuraren ciki har da fadar sarkin Kano Sunusi da Bayero. Haka ma ‘yandaba da aka jibge a gidajen sarakunan babban gidan sarki da karamin gidan jami’an ‘yansanda sun tarwatsa su.
‘YanKannywood sun sake hargitsa lamura da bayanai marasa inganci
Wasu daga cikin ‘yan Kannywood sun taka muhimmiyar rawa wajen yada labarai marasa inganci akan hukuncin babbar kotun tarayyar kan batun masarautar ta Kano. Bayan da kotun ta fitar da hukuncinta wadannan ‘yanwasan kwaikwayo sun kara ruruta lamura inda suka rika yada labarai marasa inganci a shafukan sada zumunta. Wasu na cewa hukuncin ya goyi bayan Sanusi II yayin da wasu ke cewa hukuncin yayi dadi ga bangaren Bayero wanda ya nuna cewa shine halastaccen sarki.
Fafatawar Siyasa
An dai shiga yanayi irin na dambaruwar siyasa kan batun masarautar ta Kano wasu dai na ganin batu ne kawai na siyasa. Manyan jam’iyyun siyasa biyu na jihar APC da NNPP sun shiga fafutuka da amfani da masarautar don jan hankalin magoya baya.
A shekarar 2019, gwamnatin APC (APC-led Kano government)ta raba masarautar mai dadadden tarihi zuwa masarautu kanana biyar don rage wa masarautar tsakiya karfi. Itama dokar masarautar Kano ta 2024 (Amendment no 2) wacce gwamnatin NNPP (NNPP-led Kano government,) ta jagoranci yi ta haifar da fargaba da rudani tsakanin masu rike da masarautun gargajiyar da masu rike da madafun iko na bangaren siyasa.
Mai binciken hya gudanar da aikinsa karkashin shirin gano gaskiya na DUBAWA 2024 karkashin shiorin kwararru na Kwame KariKari da hadin gwiwar WikkiTimes,don dabbaka “gaskiya”a aikin jarida da inganta ilimin aikin jarida a fadin kasar.